Thursday, November 1, 2018

KIMIYYAR DUNIYA.

Kimiyyar duniya: wani fanni ne daga cikin fannonin Kimiyya da ke
  bincike da nazari a kan Al'amuran da su ka  shafi zubi da  fasali hadi da gudanarwar Wanan duniyar tamu.bugu-da-kari kuma fannin Kimiyyar duniya fanni ne Mai kunshe da abubuwan al'ajabi.hakan kusan daidai ya ke da in ce fanni ne  da ke zurfafa bincike da nazari a kan halittun da ke cikin wanan duniyar tamu,masu rai da ma maras Rai,hakan na nufin  ruwa ,da duwatsu da dai duk Wasu hallittun da ke cikin duniyar har ma da sararin da ke wajenta.
A taikaice dai fannin Kimiyyar duniya,fanni ne Mai fadin gaske,Wanda a cikin sa ne  a ka 'yanta ko a ka yaye fannonin Kimiyyar da adadin su ya Kai 70.
To sai dai mu a Nan kasancewar ba mu da issashen lokacin da za mu Yi bayanin su daya-bayan-daya,.Wanda hakan ya tilastamana cewa za mu hade fannonin waje daya ne mu yi nazarin su a sakayance.wato za mu Yi nazarin fanonin ne a bisa turbar kakansu,hakan na nufin  nazarin namu zai ratsa ne ta ko'ina,a cikin Wa'yanan kananun fannonin ,hakan na nufin tafiyar tamu za ta kasance  kan-mai-uwa-dawabi.ma'anar hakan kusan daidaidai  ya ke da in ce , a duk fanin da hanyar karatunmu ta antayamu,za mu shiga mu sankamo bayanai ba kakkautawa domin fito da ma'anar darasin da mu ke so mu  fahimta. A,,,,, kafta,,,,,,,.

Maudu'an
 da za mu yi nazari da bayanin su a darrussanmu , su ne kamar haka.

(1). DUNIYA, ASALI , DA TARIHIN SAMUWARTA.  .(EARTH ORIGIN AND HISTORY)

(2).ZUBI DA FASALIN DUNIYA. (EARTH SHARPE).

(3).JUJJUYAWA DA ZAGAYEN DUNIYA.  (EARTH ROTATION AND REVOLUTION).

(4).MANYAN SASSAN DUNIYA GUDA HUDU.4.  (EARTH SPHERES)

(5).SASHEN RUWA.  (HYDROSPHERE).

(6).SASHEN GUNDARI. (LITHOSPHERE).

(7).SASHEN HALLITU MASU RAI.(BIOSPHERE).

(8).SASHEN MALFAR SARARIN SAMA.(ATMOSPHERE).

(9). MANYAN NAHIYOYIN DUNIYA 7.(WORLD'S 7 CONTINENTS).

(10).MANYAN TEKUNAN DUNIYA.(WORLD'S OCEANS).

(11).TSARIN SAMUWAR RUWAN SAMA, CIDA DA WALKIYA. (WERTER CYCLE,LIGHTNIN ANDA TUNDER).

(12).YANAYIN RANI DA DAMANA. (WET AND DRY SEASON).

(13).SAUYAWAR YANAYI NA YAU-DA GOBE.(WEATHER)

(14).SAUYAWAR YANAYI MAI daukar DOGON ZANGO, (CLIMATE).

(15). DARKAKEWA DA RUDUDDUGEWAR DUSAR DUWATSU,(WEATHERING).

(16).FARFAJIYAR SHIMFIDAR DUNIYA,(EARTH SURFERCE).

(17).DUWARWATSU DA TSAUNUKA,(ROCKS AND MOUNTAIN).

(18). MAKAMASHI DA NAU'O'INSA (EART'S ENERGY)

(19).GURBACEWAR YANAYI,(POLLUTION).

(20).MANYA-MANYAN FAYA-FAYEN 
DORON DUNIYA,,(PLATE TECTONICS).

(21).SHUKOKI DA TSIRAI.(WORLD VEGETATION).

(22).KARAN SAITIN  AWON LOKACI DA NISA. (LATITUDE AND LONGITUDE).

(23).KINTACEN HASASHEN RUWAN SAMA DA HAZO. (WEATHER FORCAST.)

(24).TAURARON DAN ADAM,(SATELLITE).

(25).(KINTACEN KISFEWAR RANA DA WATA.(MOON AND LUNER ECLIPSE)

(26).ALBARKATU DA KE CIKIN KASA.(MINIRALS RESOURCES).


(27).SAMUWAR KASA DA  TURBAYA.(SOIL FORMATION).

(28).YASHI DA HAMADA,(SAHARA AND DESERT).

(29).DUSA DA TSAUNUKAN KANKARA.( FROST AND GLACIER).


(30).DUWATSU MASU AMAN WUTA.(VOLCANOES).


(31)).GIRGIZAR KASA.(EARTHQUAKE).

(32).ZAIZAYAR KASA.(SOIL EROSION).

(33). AMBALIYAR RUWA.(FLOODING).

(34).DUMAMAR YANAYI. (GLOBAL WARMING).

(35).AL'UMAR DUNIYA. (WORLD POPULATION).

(36).YAKIN DUNIYA NA FARKO DA NA BIYU.(FISRT AND SECON WORLD).


(37).TASWIRAR DUNIYA.(WORLD MAP).

(38). NAHIHAR AFIRIKA,(AFRICA).

(39),YANKIN AFIRIKA TA YAMMA.(WEST AFRICA).

(40).KASATA, (NIGERIA ).


(41).DUNIYAR DUNIYOYI,.(UNIVERS).

(42).HADAKAR DUNIYOYI DA TAURARI.(GALAXY).

(43).RANA.(SUN).

(44).TAURARI.(STAR).

(45). DUNIYOYI.(PLANETS).

(46). TSARIN DUNIYOYI TARA DA RANA.(SOLAR SYSTEM).

(47).WATA.(MOON).

(48).HUKUMAR BINCIKEN SARARIN SAMANIYA,(AMERICAN N.A.S.A.).

(49). YUNKURIN WANZAR DA AL'UMA A DUNIYAR MASSS. (MARS HABITATION MISSION)

(50).SAMMAI 7.(UNIVERSIS).

(50).IKO DA GIRMAN UBANGIJI.( THE MIRACLES AND GREATNESS OF ALLAH).

Duk Wa'yanan maudu'an,da yardar Allah za mu yi nazari da cikakken bayanin  su tiryan-tiryan,daya-bayan-daya,Wanda hakan ke nufin cewa za mu Samar da darasi Mai zaman kansa,wa kowanne daya daga cikin su.
Wanda Bayan mun kammalla nazarinsu,daga Nan me Kuma za mu Mike dodar izuwa ga fanni na gaba,wato fannin ilimin na'urar kwamfiyuta, Wanda a turanci a ke kira da
(computer science).inda a Nan Kuma za mu fi mayar da hankali ne izuwa muhimman abubuwa guda uku,na farko shi ne ita
1.kwamfiyutar kanta.na biyu Kuma shi ne
2.fahimtar yaren ita  kwamfiyutar ,da Kuma dubarun Gina manhaja,ta hantar amfani da shi yaren kwamfiyutar.wato,.
(programming language and software development).sai Kuma sashe ko in ce bangare na uku,Wanda shi ne,
3.Dubarun gina Gidan yanar ankabuti,wato  (yanar-gizo),Wanda a turancin kwamfiyuta a ke kira da (website) . A kan Gina shi ne ta hanyar amfani da wa'yansu dubaru ko tsare-tsare,Wanda mafi shahara daga cikin su ,shi ne.(HTML).
Duk wa'yanan da ma wasun su,za mu Yi nazarin su,daya- daya-bayan.
Ga Mai bukatar karanta Wa'yanan darusan a harshen ingilishi,sai ya shigo Nan domin a rage Masa hanya, izuwa dayan shafinmu.

No comments:

Post a Comment