Abubuwan da ke cikin.
A hausance idan a ka ce kimiyya,a na nufin ;wani tsarin binciken ilimi ne da ke amfani da hikima wajen gano ko hakaito tsari da kintsin da Allah ya yi a hallitun, cikin sararin wanan duniyar, da ma ita kanta duniyar , har ma da kewayenta,Kama da ga kwayar zarra (atom) har IZuwa duniyar-duniyoyi,wato (univers.).
ASALI.
A falsafance ilimin kimiyya ilimi ne da aka San tarihin habakarsa Amma Kuma ba a san takamaiman tushenba,
Sai dai idan Kai musulmi ne,ko kirista zai fi maka sauki ka sanya a ranka cewa ko wanne ilimi da za ka ji ko za ka gani a duniyar Nan,to daga Allah ya ke.ganin damarsa ne, kuma ya saukar muna da ilimin ta hanyar wahayi,ko Kuma ta wadansu hanyoyin daban .wasu ilimimomin Kuma ya kan kyale mu ne ,mu je mu Yi ta bincike har dai mu gano ya Abin ya ke.kasancewar ya Riga da ya hore mana fikira da kaifin tinanin yin hakan .kasancewar kuma a haka ya tsara duniyar.
TARIHI
A kiyasance dai za a iya cewa ilimin kimiyya ya fara Gina kansa ne tun kimanin shekaru dubu hudu da su ka wuce.ya na Kuma girma da habaka ne a irin tsarin gini ko katanga.wato a duk lokacin da wani ya zo,zai Gina fahimtarsa ne,a kan ta wani , idan wani ya sake zuwa, dorawa kawai zai Yi a kan fahimtar wancan da ya gabace shi.duk da cewa a wasu lokutan wani yakan rushe fahimtar wani,Wanda ya gabace shin ,matukar cewa ,ya zo da fahimta da kuma hujjojin da su ka fi na wancan gamsarwa.
GIRMA.
Duk da cewa ilimin kimiyya shi ne ya Gina kansa hakan ba Yana nufin shi ya kirkiro kansa ba 'a'a,ana nufin dai ba mutum daya ne ko gari daya ne suka Gina shi ko kirkiro shi ba .wato hadaka ce ta fasihai da Kuma masana ta kowanne bangare na duniya.
Yadda tsarin ke gudana shi ne: ko Dan Ina ne Kai,idan ka zo da sakamakon wani bincike ko nazarinka akan wani Abu da ka yi a rubuce ko kuma a zahirance,to za a karba a duba a gani a Kuma auna,idan ya yi daidai da tsarin da kimiyya ke tafiya a kai,to sai a karba a sa shi cikin kundin ilimin kimiyyar wanan fannin,a Kuma Yi kokarin yada wanan sakamakon I Zuwa uwa duniya.Kai Kuma a bisa kwazo da gudummuwarka a wannan fanin, za a martabaka iya martabawa,a Kuma Yi kokarin antaya sunanka a jikin tituna da makanratu,ta yadda sunan naka ba zai Yi sauri antayawa cikin kogin mantuwaba.
UWAYEN KIMIYYA.
Kasashen da suka fi taimakawa kimiyya wajen ganin ta samu 'yancin kai su ne kamar haka: girka, (Greek) andalus,(Spain), jamus,(Germany) burtaniya,(England) farisa,(France) misira,da Kuma sauran daulolin larabawa da hindawa da ma wani yanki na sinawa.me yiwuwa wani zai iya tambayar kansa ya ce;" 'yancin Kai Kuma?,eh haka a ke nufin,domin ai a can farkon zamani kimiyya ba ta da 'yancin-kai.domin kuwa a wancan lokacin, duk wani Wanda ya zo da wani sabon ilimi ko fahimtar da ta sabawa addininsu na kiristanci, to hukuncinsa shi ne kisa.domin ya zo a tarihi cewa;wanan shaihin malamin ilimin TAURARI da lissafi da falsafa, Dan kasar andalus (spain).Mai suna; (Galileo galili)1564-1643,Wanda shi ne mutum na farko da ya fara kirkiro da na'urar nan ta hangen nesa wato (talaska)ko Kuma (telescope). wacce da ita ya Yi amfani wajen gano cewa duniyarmu (earth) ba ita ce tsakiyyar duniyar-duniyoyi ba,wato (univers) ,Kuma ba Rana ce ke zagayar duniyarmu ba .wato ita duniyar tamu ce ke zagayar Rana.Wanda kuma hakan ya sabawa tsarinsu na kiristanci da yahudanci.hhmm, ai kuwa a nan take su ka kwamashe shi su ka garkame shi a magarkama,da ga karshe dai,a can ya iyar da sauran rayuwarsa.sai dai duk da hakan , daga karshe sai a ka zo, reshe ya juiye da mujiya,inda kimiyya da fasaha su ka kwace mulkin duniyar daga hanun malaman majami'ai, a ka Rika kashe malaman cocin.a takaice dai wanan manuniya ce da ke nuna cewa kimiyya ta hadu da kalubale kala-kala kafin ta samu ta tsira da mutuncinta.wanda yanzu ga shi an wayi gari, ita ce abu mafi kima a siyasar duniya,ma'ana ;tattalin arzikin kowace kasa da karfin fada-ajinta,ya dogara ne kacokan a kan karfin kimiyya da fasaharta.
wani Abu Kuma da ya kamata Mai karatu ya shigar a kwakwalwarsa a yayin da ya ke auna ingancin falsafar kimiyya,shi ne;. A tsarin irin na kimiyya; ba a yarda da tsafi ko sihiri ba ,Kuma ita kimiyya ba ruwanta da addini ko akida.wato atakaice dai idan ka na karanta kimiyya a matsayin godaben rayuwa,ne wato (carrier)ko Kuma ka na karanta ta ne domin nishadi.;abin da za ka yi kawai shi ne; ka dauki falsafar da ta zo daidai da karantarwar addininka.Sauran zancen kuma ka barmusu kayansu,ka ce da su; "su je dai su Kara bincike".me yiwuwa daga baya sa gano gaskiyar,kamar yadda ya Sha faruwa.
Masana kimiyya, sun karkasata,bangarori da dama,Amma dai bangarorin da za mu kwamaso a darrussanmu na Wanan shafin su ne kamar haka:
1.kimiyyar rayuwa.(biology)
2.kimiyyar duniya.(earth science).
3.Kimiyyar na'urar comfiyuta.(computer science).
4.kimiyyar sinadarai.(chemistry).
5.kimiyyar fiziya.(physics).
Da yardar Allah Za mu kasa su a tire daya-bayan-daya.
Ga Mai bukatar karanta darusan a turance; sai ya ziyarci dayan shafinmu ta Wanan adireshin.
www.simplegeneralscince.blogspot.com
Ga Mai neman Karin bayani ko gyara ko Kuma tsokaci,sai ya antayo sakon karta- kwana ta Wanan lambar,09035907765. Ko Kuma ya zuba sharhinsa ta Wanan akwatin sharhin..da ke kasan shafi.
Sunana junaidu.shekaruna 26 ina zaune a garin sokoto Kuma ni dalibin ilimi ne,na kowanne fanni.
Subscribe to:
Posts (Atom)
No comments:
Post a Comment