I wish to inform you that today 02-02-2019.i have launched my two science bloging websites,Wich i have designed in two versions, that is in hausa and in English .and I have created them for the aims of, to educate and entertain me and my fellow brothers and sisters.if you like to explore what is there, follow this link,
www.simplegeneralscience.blogspot.com.
A Dan karamin turancina, na kintace, abin da na ke kokarin fada ko shelantawa a Nan shi ne; cewa, Ina Mai farin cikin sanar da ku cewa A yau ne ,02-02-2019,na kaddamar da wa'yansu shafunan mudawwana guda biyu da na gina a yanar ankabuti,wato yanar gizo, Kuma duk su biyun su na dauke ne da darussan Kimiyya.daya na yi amfani da saukakkaken turanci ne wajen wallafa darusan da ke cikin sa.dayan Kuma na Yi amfani ne da yarenmu na uwa ,wato hausa. Na Kuma Gina su ne ba Dan komai ba, sai domin ilmantarwa da Kuma nishadantar da ni kaina,da ma sauran al'uma,.hakan na nufin cewa ,izuwa yanzun, duk inda ka ke a fadin duniyar Nan,za ka iya riskar Wa'yanan darusan da ke cikin shafin,ta hanyar bibiyar wanan adireshin.
www.kimiyyadahausa.blogspot.com.
Kimiyya da hausa
Tuesday, August 2, 2022
SANARWA
Thursday, December 27, 2018
Gabatarwa.
bada tawa gudummuwar ko da kankanuwa ce ,tare da buri da kuma kwadayin harshen nawa ya Kara samun habaka kamar sauran takwarorinsa.wanda hakan ya sa na tambayi kaina da cewa, ta wace hanya kenan zan Yi hakan? Kuma ta Ina zan fara?.to a haka dai sai na ga cewa, ko dai zan Fara ne da 'yan rubuce-rubuce a fanonin da su ka shafi na'urar comfiyuta da ma Wasu daga cikin ilmomin zamani, mussaman masu alaka da kimiyya,?.wato, ta amfanin da yaren nawa. .domin kuwa a Dan karamin nazarin da na Yi ,a bisa manuniyar ci gaban harsunan duniya,na hakaito cewa duk wani harshe ko yare da ya samu shahara a duniyar nan,to za ka samu cewa ya samu nasarar ne a bisa martabar da ya ke da ita a wajen al'umar duniya. ita kuma martabar harshe ya kan same ta ne a ma'unin zunzurutun alakantuwar sa da rubuce-rubucen fannonin ilmomin da a ka yi amfani da shi wajen wallafa su.domin kuwa a bayyane ya ke cewa yaren ingilishi da larabci,da faransanci duk sun samu shahara da martaba ne a bisa manuniyar kasancewar ,su ne yarurrukan da a ka fi yin amfani da su wajen wallafe-wallafen daukacin ilmomin da Dan Adam ya mallaka a Wanan duniyar tamu. Kenan dai hakan kusan manuniya ce da ke nuna cewa ,iya sinkin-sinkin wallafe-wallafen da a ka Yi da harshe ne ke taimamakawa wanan yaren wajen yaduwa da shahara a fadin duniya.wato ba adadin yawan masu magana da yaren ba.
zai bada damar a kira Shi da gurgun yare ba.domin ai idan ka Ware yaren engilishi,da na sinanci da Hindanci da Kuma larabci,to a mafi yawancin yarrurukan da
2).mu yawaita nazari da bincike tare da kokarin kirkiro sababbin kalmomin da za su iya maye gurbin wa'yansu daga cikin kalmomin da mu ka aro daga wa'yansu yarrurukan.
3).Mu rinka cike dokoki da ka'idojin rubutu ,a rubuce-rubucenmu na yau- da-kullum,.
4).mu kuma Rika nanatawa da Jan hankali izuwa ga hukumomin da abin ya shafa, kan cewa a rika maimaita kokarin Nan na jarraba maida tsarin koyar da daukacin ilimomi a yarenmu na uwa, wato hausa.idan Kuma hakan zai Dan-tada kura ,to sai a Rika karantarwar da dukan yarukan biyu, a lokuta mabanbanta, ,domin yin hakan zai yi matukar saukaka wa yara fahimtar ilimin da a ke so su fahimta a cikin sauki.
www.simplegeneralscience.blogspot.comwww.simplegeneralscience.blogspot.com
Wednesday, December 26, 2018
(1).KA'IDOJIN KARATU DA RUBUTU A HARSHEN HAUSA.
KA'IDOJIN KARATU DA RUBUTU A HARSHEN HAUSA.
MATASHIYAR FARKO.
Kasancewar tun kafin yanzun ina mai lura da kura-kuran da muke ta tafkawa a wajen rubuce-rubucen da mu ke Yi a harshen Hausa. Na lura da hakan ne a sakamakon karance-karancen mukalolin da na ke karantawa da ake rubuta a harshen Hausa, da Kuma littattafan Hausa, da littattafan hikayoyin da aka rubuta cikin harshen namu na Hausa, da Kuma sakunan sharhi da tambayoyi da a ke rubuto mini, kai har ma da rubuce-rubucen da ake yi a jikin motocin hawa, irin su manya motoci, kamar rokoki, Daf-Daf da dangoginsu, har ma izuwa mashina da kekuna da muke hawa. Na sake lura da wa'yansu kura-kuran da mu ke yi a rubuce-rubucen da mu ke yi a gaban shagunanmu domin talla, da kuma rubuce-rubucen da mu ke yi a jikin allunan kan hanya,wato (billboard).
MATASHIYA TA BIYU.
Hallau dai
Kusa-kuran sun hada da harhade kalmomi a wajen da ba a nan a ake hadawa ba, da kuma raba kalmomin a wajen da ba a Nan ake rabawa ba, wato (Word margins and divisions), da kuma rubuta kalmomin da su ka kunshi bakake iri daban-daban, wanda a ka’ida ba a haka ya kamata su zo a rubutu ba, da kuma cusa kalmomi ba a muhallin su ba, wani lokaci kuma rashin amfani da alamomin rubutu (Orthography) a wajen da suka dace, ko kuma rashin amfani da su ma kwata-kwata da mu KE yi, da dai sauran matsalolin da kan Iya zamewa barazana wajen keta-hadin yarenmu namu.
MATASHIYA TA UKU.
kasancewar faruwar hakan na da alaka da cewa ba asalin Hausawa ne, su ka fitar da Manhaja ko Jadawalin rubutun Hausa ba. Domin Idan mu ka koma a can tarihin baya , za mu tarar cewa irin su Farfesa Neil Skinner, wato Daraktan Hukumar NORLA da George Percy Bargery, Mawallafin Kamusun Hausa da Hanns Vischer, wanda ake kira Dan Hausa da Dokta R. M. East, Shugaban Hukumar Talifi da Mista. L. C. Giles, Editan farko Bature na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da sauransu, su ne suka fitar da yadda za a yi rubutun Hausa. Kasancewar kuma su ba Hausawa ba ne, bugu-da-kari kuma ,ba su san furucin Hausa da kuma kalmomin hausar sosai ba.wanda hakan ne ya sanya ,rubutun Hausa ya taso cikin hajijiya da kuma rudani, wanda ya janyo har izuwa yanzu mu ke ta tafka kura-kurai, a rubuce-rubucenmu. , Wanda kuma hakan ne ya janyo yaren namu ke ta tafiya da dingishi, face wa'yansu Daga cikin malamanmu da kuma dalibai iri na da ke tashi tsaye, don neman fahimtar yaya ka’idojin rubutun Hausar su ke kafin su yi rubutun Hausar.
MATASHIYA TA HUDU.
To a baya-bayanan Nan dai da a ka ga cewa matsaloli sun cunkushe rubutun Hausar, sai aka Fara shirya manyan tarrurrukan kasa-da-kasa,inda izuwa yanzun da na ke wanan rubutun.(15-02-2019) an samu damar gudanar da manyan taruka guda uku.an Yi su ne Kuma , domin daidaita KA’IDOJIN KARATU DA RUBUTU a HARSHEN hausa. Taron farko an yi shi ne, a Birnin Bamako da ke kasar Mali, daga 28, ga watan Fabrairu, zuwa 5, ga watan Maris a shekara ta 1966. Taro na biyu kuma an gudanar da shi ne, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a ranar 21, ga watan Yuni a shekarar 1970, sai kuma na ukun da aka yi a Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, a cikin Jami’ar Bayero da ke Kano, a watan Satumbar shekarar 1972. A cikin wadannan tarurrukan an yi gyare-gyare wa littafin nan na'yanttatun kalmomin Hausa wato (hausa Spellings book’,)Wanda shi ne littafin da turawa suka dora mu a kansa domin yin rubutu a HARSHEN hausa, wanda kuma shi ke dauke da Manhaja da Jadawalin rubutun Hausa.
MATASHIYA TA BIYAR.
Sai dai duk da gyare-gyaren da aka yi wa ka’idojin rubutun da kuma kalmomin Hausa, sai ya zamanto duk da hakan dai tsugune-ba-ta-kare ba, wato ba-a-rabu-da-Bukar-ba-an-haifi-abu, inda al’amarin ya koma ana kukan targade sai ga karaya, domin an dada rikita mutane ne, wanda ya sa a rubutu guda sai ka ga ana amfani da tsohuwar ka’ida da kuma sabuwar ka’ida a wake daya.
To Haka dai abubuwa suka yi ta tafiya a kudundune, ba tare da kuma an samu mafita ba, wannan matsalar ta ci gaba da ci-wa-masana ilmin harshen Hausa tuwo-a-kwarya. Da dai tura ta kai bango ne, ganin ruwa yana neman karewa dan kada bai gama wanka ba, ma’ana ganin rubutu cikin harshen Hausa na neman ya ci tura, sai masana ilmin harshe na kasar Jamhuriyar Nijar suka gayyaci takwarorinsu na Najeriya, inda a nan suka shirya wani gagarumin taro a birnin Yamai, a Cibiyar Harshe da Tarihi ta Sarrafa Adabin Baka Wacce a Turance a ke kira da (Centre for Linguistic and Historical Studies by Oral Traditions ), a karkashin jagorancin Majalisar Hadin Kan Afirka (OAU), wanda yanzu ta
dawo Tarayyar Afrika (AU), an yi taron ne tun daga ranar 7 zuwa 12 ga watan Janairu, a shekarar 1980.
Daga farko sun daidaita kawunansu a Bakake da Wasulla da Auren Wasulla da kuma Tagwan Bakake, kana daga bisani suka daidaita ka’idojin rubuta kalmomi.
KAFCEE.
Ga abubuwan da suka zayyana kamar haka:
BAKAKE.
Bakake na nufin harufa.
Bakaken da aka yarda da su a rubutun hausa, su ne Kamar haka.
KANANA: b, b’(mai lankwasa), c, d, d’ (mai lankwasa), f, g, h, j, k, k’(mai lankwasa), l, m, n, r, s, t, w, y, ’y, z
MANYA: B, B’ (mai lankwasa), C, D, ‘D (mai lankwasa), F, G, H, J, K, K’ (mai lankwasa), L, M, N, R, S, T, W, Y, ’Y, Z
WASULLA
KANANA: a, e, i, o, u
MANYA: A, E, I, O, U
AUREN WASULLA
KANANA: ai au maimakon ay aw
MANYA: AI AU maimakon AY AW
TAGWAN BAKAKE.
tagwayen bakake na nufin,hade harufa biyu domin Samar da wani sautin furuci a harshen hausa.
KANANA: fy, gw, gy, kw, ky, kw(mai lankwasa), ky (mai lankwasa), sh, ts
MANYA: FY, GW, GY, KW, KY, KW (mai lankwasa), KY (mai lankwasa), SH, TS
KA’IDOJIN RUBUTA KALMOMI
Da suka dawo ka’idojin rubuta kalmomi kuma, sun fito da dokoki goma sha uku (13).
Ga ka’idojin rubuta kalmomin da aka fitar a taron da aka yi a kasar Nijar kamar haka:-
(1). MANYA BAKAKE
Wannan ya kasu kashi biyu ne:
(1a). Duk jimloli suna farawa da manya baki.
Misali: Gobe zan je kasuwa.
Jiya na ci tuwo.
(1b). A rubuta manyan bakake a farkon zanannun kuma sunayen yankan na mutane da kuma na takamaimun wurare.
Misalin sunan yanka a mutane shi ne
Sunayen mutane: Adamu, Shamsiyya, Haruna, Mahmud.
Sunayen wurare: Jami’ar Maiduguri, Asibitin Murtala, Bauchi, Kano.
(2). Ba a yarda a yi amfani da bakin P a rubutun Hausa ba , sai dai F. Amma za a iya amfani da P a cikin zanannun sunaye kamar haka:
Palasdinu ba Falasdinu ba.
Paris ba Faris ba.
Sipikin ba Sifikin ba.
Mustapha ba Mustafa ba.
Amma za a iya rubuta harafin P idan ta zo cikin Kalmar amsa-kama, kana sun amince a rubata Fensiri da Panko, maimakon Pensiri da Panko
(3). Ana amfani da wadannan ka’idojin wajen rubuta bakaken M ko na N.
(3i). A yi amfani da M a tsakiyar kalma, idan bakin B, B (mai lankwasa), F, ko da harafin M ne yake gaban M din, a rubuta M, misali:
(a). Tambaya ba Tanbaya ba.
Jimbiri ba Jinbiri ba.
Gammo ba Ganmo ba.
(b). Amma a rubuta N a sauran muhallai, misali:
Gansheka ba Gamsheka ba.
Gungume ba Gumgume ba.
Ganzaki ba Gamzaki ba.
Tuntube ba Tumtube ba.
Kanwa ba Kamwa ba.
(c). Ana rubuta N a karshen kalmomi, ko da kalmomin da ke gaba sun fara ne da bakaken B, B (mai lankwasa), F, ko M, misali:
Gidan Bala ba Gidam Bala ba.
Ramin bera ba Ramim bera ba.
An fasa ba Am fasa ba.
Sabon maho ba Sabom maho ba.
(d). Idan kalma tana karewa da M ne a karshen ta ,sai a rubuta M din:
Malam Ali ba Malan Ali ba.
Kullum ba kullun ba.
Mutum daya ba Mutun daya ba.
(e). Kalmomin amsa-kama masu karewa da M, sai a rubuta M din:
Jimgim ba Jingin ba.
Sukutum ba Sukutun ba.
Kundum ba Kundun ba.
(4). Bakaken nasaba da na mallaka.
(1).Bakaken nasaba, watau da N da R, ba sa sajewa da bakaken da ke gabansu:
(a) Sarkin makafi ba Sarkim makafi ba.
Akwatin fata ba akwatim fata ba.
Sarkin fada ba Sarkim fada ba.
Sarkin baka ba Sarkin baka ba.
(b) Ranar dariya ba Ranad dariya ba.
Ranar kuka ba Ranak kuka ba.
Ranar tashi ba Ranat tashi ba.
(2). Bakaken mallaka, watau N da R ba sa sajewa da bakaken da ke gaba da su.
(a). Gonakinmu ba Gonakimmu ba.
Rigunanmu ba Rigunammu ba.
Matanmu ba Matammu ba.
(b). Gonarmu ba Gonammu ba.
Rigarmu ba Rigammu ba.
Motarmu ba Motammu ba.
(5). Bakin R mai zuwa karshen fi’ilan haddasau ba ya sajewa da bakin da ke biye da shi, misali:
(a). Mayar da shi. ba Mayad da shi ba.
Sayar masa da shi. ba Sayam masa da shi ba
Mayar wa Ali shi. ba Mayaw wa Ali shi ba.
(b). Motar da ka shiga. ba Motad da ka shiga ba
Sakar da ta yanke ba Sakad da ta yanke ba.
Hular da ya karba ba Hulad da ya karba ba.
(6). Ana rubuta karan-dori wajen rubuta tagwan kalma:
Fadi-tashi ba Fadi tashi ba.
Kwan-gaba ba Kwan gaba ba.
Bar-ni-da-mugu, ba Bar ni da mugu ba.
(7). Ana rubuta kalmomin jam’u a hade kamar haka:
Komai ba Ko mai ba.
Kowa ba Ko wa ba.
Ko’ina ba Ko ina ba.
Koyaushe ba Ko yaushe ba.
Kowanne ba ko wane ba.
Kowane ba Ko wane ba.
Kowadanne ba Ko wadanne ba.
(8). Ana rubuta wadannan zagagen fi’ilan a hade:
(a). Yakan rubuta ba Ya kan rubuta ba.
Takan “ ba Ta kan “ ba.
Nakan “ ba Na kan “ ba.
Mukan “ ba Mu kan “ ba.
Kukan “ ba Ku kan “ ba.
Sukan “ ba Ku kan “ ba.
Kikan “ ba Ki kan “ ba.
Kakan “ ba Ka kan “ ba.
Akan “ ba A kan “ ba.
(b). Yana rubutawa ba Ya na rubutawa ba.
Tana “ ba Ta na “ ba.
Ina “ ba I na “ ba.
Muna “ ba Mu na “ ba.
Kuna “ ba Ku na “ ba.
Suna “ ba Su na “ ba.
Kina “ ba Ki na “ ba.
Kana “ ba Ka na “ ba.
Ana “ ba A na “ ba
(c). Yake rubutawa ba Ya ke rubutawa ba.
Take “ ba Ta ke “ ba.
Nake “ ba Na ke “ ba.
Muke “ ba Mu ke “ ba.
Kuke “ ba Ku ke “ ba.
Suke “ ba Su ke “ ba.
Kike “ ba Ki ke “ ba.
Kake “ ba Ka ke “ ba.
Ake ” ba A ke “ ba.
(d). Ana so kuma a rubuta kamar haka:-
Ta rubuta.
Mun “
Kun “
Kin “
Ka “
Sun “
Ya “
An “
(9). Zagagen fi’ili masu nuna lokaci mai zuwa ana rubuta su ne: Kamar haka:
Zai tafi.
Zan tafi .
Za mu tafi ba Zamu tafi ba.
Za ku tafi ba Zaku tafi ba.
Za su tafi ba Zasu tafi ba.
Za ki tafi ba Zaki tafi ba.
Za ka tafi ba Zaka tafi ba.
Za a tafi ba Za’a tafi ba.
(10). Ana rubuta kalmomi masu ma’ana a wawware cikin jimla:
Misali Kamar ka ce:
Ya sa ni in ba ka kudi.
Abin da ya sa ya fi shi cancanta shi ne…..
Na tsai da kai don mu yi kallon tare. Ka ga a Nan za ka ga cewa kowacce warrariyyar kalmar, a cikin su, za ta iya cin gashin kanta,woto za ta iya bada ma'ana.
(11)(a) Ana rubuta abin malllaka hade da gajeriyar kalmar mallaka:
Dokina ba Doki na ba.
Rigarsa ba Rigar sa ba.
Zanenta ba Zanen ta ba.
(b) A na rubuta abin mallaka daban, kuma doguwar kalmar mallaka daban:
Misali::
Wani doki nawa ba Wani dokinawa ba.
Wata riga tawa ba Wata rigatawa ba.
Wani zane nata ba Wani zanenata ba.
(12) Ba a hade wakilin-suna mafa’uli da kowace kalma:
Ya ba ni ba Ya bani ba.
Mun sa shi, ba Mun sashi ba.
Ana kiran ka ba Ana kiranka ba.
(13) sannan ana rubuta
Saboda ba Sabo da ba.
Watakila ba Wata kila ba.
Bayan sun fitar da wadannan ka’idojin rubutun kalmomi ne, suka sake fito da wasu ka’idoji da ya kamata abi wajen rubuta wa'yannan: kalmomom.Kamar haka:
Shi ne ba shine ba.
Ita ce ba Itace ba.
Mu ne ba Mune ba.
Kai ne ba Kaine ba.
Ke ce ba Kece ba.
Su ne ba Sune ba.
Ku ne ba Kune ba.
Ni ne ba Nine ba.
(2) haka a rubuta: Wa'yanan kalmomin kamar haka:
Ya yi ba Yayi ba.
Ya ci ba Yaci ba.
Ya tafi ba Ya tafi ba.
Ya je ba Yaje ba.
Ya fi ba Yafi ba.
Ya ki ba Yaki ba.
Ta ki ba Taki ba.
Ta yi ba Tayi ba.
Idan muka dawo a bangaren ka’idoji ko alamomin rubutu Kuma wato (orthography), nan ma na dan hakaito wa'yansu 'yan kura-kurai da mu ke antayawa. Wanda Lura da hakan ne ya sa na dan yi takaitaccen fashin baki a kan yadda ake amfani da alamomin rubutu, wajen rubutu a cikin harshen Hausa.
(1). AYA (Full Stop) (.)
Ana amfani da aya a rubutu wajen da ake bukatar cikakkiyar tsayawa, ko saukar da numfashi gaba daya. Idan har an yi aya a rubutu, to wata jimla ko zance ko magana mai zaman kanta ce za a shiga, ko kuma rubutu ya kare. Bayan Aya in har za a ci gaba da rubutu, to da babban baki ake fara rubutun, misali:
(1). Idris ya ci abinci ya koshi. Da yammaci kuma sai ya tafi rafi debo ruwa.
(2). Shamsiyya ta tafi kasuwa.
A jimla ta biyu an nuna jimla ta riga ta kare, wanda hakan ne ma ya sa aka yi Aya a rubutun. Ana kuma amfani da Aya wajen takaita zance, misali, kamar :Mal. A. Shehu maimakon Malam Adamu Shehu.
(2). WAKAFI (COMMA) (,).
Ana amfani da wakafi a rubutu wajen da ake bukatar ‘yar karamar dakatawa ko saukar da numfashi kadan. Bayan an yi wakafi a rubutu karamin baki ne yake biyo baya, kasancewar an dan hutar da mai karatu ne, don ya samu ya daidaita numfashinsa; domin karutan ya yi masa ma’ana da kuma dadi. Misali:
(a) Musa ya tafi kasuwa dazu-dazu, don ya sayo yadin sallarsa. Ka ga an bayyana Musa ya tafi kasuwa, sannan sai aka yi wakafi, don a hutasar da mai karatu, daga bisani kuma aka karasa rubutun da cewa ‘don ya sayo yadin sallarsa.’
(3). ALAMAR TAMBAYA (QUESTION MARK) (?).
Wannan tana daga cikin ka’idojin rubutu, masu matukar amfani a rubutu, domin tana bambance ma’anar jimla, zance ko magana, inda take nuni da tambaya aka yi, ba wai zance ko bada labari ba wato (statement). Ma’ana, ana kore wa mai saurare ko mai karatu tantama. A taikaice dai a duk inda aka yi alamar tambaya, to ana ja , wato madda yayin karantawa. Haka shi ma mai karantawa ana so ya ja yayin karantawar.
Misali:
(1) Maryam ta je asibiti jiya. Zance (Statement).
Amma idan ka ce:
(2) Maryam ta je asibiti jiya ? Tambaya (Interrogation).
A falsafance
Jimla ta farko ta nuna cewa da Maryam ta riga da ta je asibiti jiya. Amma sakamakon alamar tambaya da aka yi a jimla ta biyu, sai ma’anar ta canza, inda ake tambayar ko Maryam ta je asibiti jiya?.
Babban baki ne yake zuwa bayan an yi alamar tambaya a rubutu. Misali:
(a). Yaushe rabon duniyar siyasar kasar nan da ayyeyare ? Ina jin tun lokacin jamhuriya ta farko, hana rantsuwa zuwa farkon jamhuriya ta biyu.
(4). ALAMAR MOTSIN RAI (EXCLAMATION MARK) (!).
Ana amfani da alamar motsin rai, wajen sanar da mai karatu wani abu na takaici, tsoro, kaduwa, mamaki da sauransu. Misali:
(a). Wayyo Allahna !
(b). Ah ! Ya kashe ni.
(c). Oh ! Abin da mamaki, dan akuya da wanke-wanke.
(d). Ya cire min ido !
Bayan an yi alamar motsin rai a rubutu, babban baki ne, yake biyo baya in har za a ci gaba da rubutu. Misali:
Ah ! Na shiga uku, na lalace.
Das ! Gabansa ya buga.
Zambur ! Ta mike kamar wacce aka tsikara da tsinin mashi.
Sun yi masa caa ! Kasuwar kuda.
(5). BAKA BIYU (BRACKET OR PARENTHESIS) ( ).
Ana amfani da baka biyu a rubutu wajen karin bayani ga mai karatu, wato kara fito da ma’anar me ake nufi a zance, jimla ko maganar da aka yi.
(a). Da sanyi safiya Abubakar ya bar jiharsa (Bauci). Ka ga an ji Abubakar ya bar jiharsa, to amma wani zai so ya ji ina ne jihar Abubakar, amma da aka sa a cikin baka biyu, sai ya gamsar da mai karatu.
(b). Sai a watan Satumbar shekara ta 1927, aka samu wani basudane (dan kasar Sudan) da ya fitar da mutane daga duhun jahilci..
HAka-zalika Ana amfani da baka biyu, wajen sakaye wani batu da bai danganci rubutun da ake yi ba. Misali, ana rubutu cikin harshen Hausa, sai wata kalma ta shigo, ba ta Hausa ba, ko kuma an fadi ma’anarta da Hausa, amma kuma an fi saninta da Turanci, ko kuma dai ana so a santa cikin harshen Turanci, to sai a sanya ta cikin baka biyu. Misali,
Amina ta dafa miyar tumatir (stew) da safe. Ka ga wani idan ya ji an ce, an yi miyar tumatir, abin zai dan ba shi mamaki, amma kuma kasancewar an sa Kalmar stew, cikin baka-biyu, kuma dama an fi sanin miyar tumatir din da sunan stew, sai ya zamanto an fi fahimtar jimlar.
Ana amfani da baka biyu wajen sakaye takaitattun harrufa. Misali, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Babban Bankin Najeriya (CBN).
Yayin da ake amfani da baka biyu, wakafi, alamar tambaya ko aya duk za su iya biyowa baya.sai dai Kuma, ya danganci yaya jimlar, zancen ko maganar ta ginu. Misali:kamar;
(1). Amina ta dafa miyar tumatir (stew), da sanyin safiya. (wakafi)
(2). Bafarawa ya bar biliyoyin Nairori a baitul-malin jiharsa (Sakkwato). (aya)
(3). Kana ganin zai iya rabuwa da ita (motarsa) ? (alamar tambaya).
Bakin da ke biyo baya, bayan an yi baka biyu a rubutu ya dangancin da wane daga cikin ka’idojin rubutu aka yi amfani. Idan wakafi ne aka sankama bayan Bayan baka-biyun. to karamin baki ne zai biyo baya. Idan kuma aya ko alamar tambaya ce, sai babban baki ya biyo bayan baka biyun.
(6) KARAN-DORI (DASH) (-).
Ana amfani da karan-dori a rubutu, wajen rubuta tagwan kalmomi, misali,
(1). Ahmad yana ta safa-da-marwa a dakinsa.
(2). Shamsiyya ta tsaya kai-da-fata, domin ganin ta samu nasarar cin jarrabawarta.
(3). Hassan yana ta fadi-tashi don ganin ya ci zabe.
Akan Kuma yi amfani da karan-dori wajen hada kalma da kalma, misali, kamar ka ce kaka-tsara-kaka, tana-kasa-tana-dabo, sa-toka-sa-katsi. Idan bayan an yi amfani da karan-dori a karshen rubutu , aya ce take ke zuwa, idan kuma ba a karshen rubutu ya zo ba , wakafi ne ke zuwa. Misali:
(1). Siyasar kasar nan, tana-kasa-tana-dabo.
(2). Tana-kasa-tana-dabo, damben Shago da Namadi.
Wani lokaci ko da an yi amfani da karan-dori, babban baki na iya biyowa baya, misali, wajen rubuta suna mai dauke da Al: Al-Mustapha, Al-Amin da sauransu. Haka zalika, ana amfani da karan-dori wajen nuna zancen wani musamman ma wajen aikin jarida, misali: Kungiyarmu ta dukufa wajen kare hakkin dan Adam - Alhaji Umaru Ahmed. Wannan karan-dorin da ya zo shi ya nuna cewa zancen wani ne. Har ila yau, ana amfani da karan-dori wajen danganta wasu batutuwa, misali: shekara 50-60, ko daga 1990-1999, awa 20-30, tarihin dandalin a daidaita sahu 2004-2009, da sauransu.
(7). RUWA BIYU (COLON) (:).
Ana amfani da ruwa biyu idan za a lissafa ko zayyano wasu batutuwa yayin rubutu, kuma akasari idan an yi aya mai ruwa a rabutu, an fi yin sakin layi, misali:
Bashir Yahuza Malumfashi ya yi rubuce-rubuce da yawa, wanda suka kunshi littattafan hikayoyi da wakoki. Daga cikin littattafansa akwai:
(1) Kudin Jini.
(2) Zinatu Matar Gwamna.
(3) Sinadarin Rayuwa
(4) Bikin Kishi.
Ba wai ya zama dole duk lokacin da aka samu ruwa biyu a rubutu, ya zama sai an yi sakin layi ba, misali, Kadan daga cikin wakokin Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) su ne: ‘Bara A Kufa’ da ‘Sakarkari’ da Bubukuwa. Abin da nake so Mai karatu ya antayawa kwakwalwarsa a Nan shi ne, a duk lokacin da aka yi amfani da ruwa biyu a rubutu, to harafin da zai biyo baya bai zama lalle sai babban baki ba, misali,
Ga yadda ake hada maganin: da farko a samu nono marar tsami, sai a zuba garin magani, sannan a kada, sai kuma a sha.
Amma wasu masana ka’idojin rubutu sun ce, dole bayan an yi ruwa biyu a rubutu, sai babban baki ya biyo baya.
(8). WAKAFI MAI RUWA (SEMI-COLON) (;).
Ana amfani da wakafi mai ruwa wajen daidaita jimloli, zantuka ko maganganun da suka zo bi-da-bi, misali:
(1). Lokacin da aka shelanta ganin watan azumin Ramadana, wasu sun yarda; wasu shakulatin-bangaro suka yi da batun; wasu kuma sun tsaya a rigar-tsakani.
(2). Hotuna ne guda uku, na farko Bello ne; na biyu Kabiru; na uku kuma Fahad ne. Wani abu da ake so mutane su sani, shi ne, a wannan rukunin yayin da aka yi wakafi mai ruwa a rubutu, karamin baki ne yake biyo baya, ba kamar idan an yi aya ruwa biyu ba.
(9) ZARCEWA DODAR, (DOTS OR ELLIPSIS) (...).
Ana amfani da zarce a rubutu wajen sanar da mai karatu cewa akwai sauran wani abu da ba a karasa ba, wani lokaci akan yi zarce a rubutu domin abin da ake so a sanar da mai karatu ya shige shi sosai, kasancewar shi zai karasa zancen da kansa. Zarce yana farawa ne daga ayoyi (digo) uku zuwa sama. Misali:
(1) Rayuwar ‘yan Afirka a Turai, ba girin-girin ba………
(2) Idan kunne ya ji, gangar jiki………..
Sai dai idan har rubutu bai kare ba, bayan an yi amfani da zarce a rubutu, to babban baki ne zai biyo baya, misali:
(1). Rayuwar ‘yan Afirka a Turai ba girin-girin ba…… Amma idan ka je za ka gane irin kudar da ake dandanawa.
(10)ALAMOMIN ZANCEN WANI (QUOTATION MARK) (“ ” ko ‘ ’)
Ana amfani da alamomin zance don kebe ko nuna zance ko magana ta wani ne. Masana ka’idojin rubutu, sun amince a yi amfani da (“ ”) ko (‘ ’) yayin kebence ko nuna zancen wani. Ana kiran wannan alama ta farko (“ ko ‘ ) da sunan BUDE ZANCE, ta biyu kuma (” ko ’) ana kiran ta da sunan RUFE ZANCE. Misali:
Mamuda ya ce “Bello ya sayi na’urar kwamfyuta jiya.” ko
Mamuda ya ce ‘Bello ya sayi na’urar kwamfyuta jiya.’
Sai dai takaddama ta kaure tsakanin masana ka’idojin rubutu, wasu daga cikin su, sun ce, lallai ne a saka Aya a karshen magana, zance ko jimla, misali:
Hassan ya ce “Ibrahim ba shi da lafiya”.
Dalilinsu na fadin hakan shi ne, idan dai an yi aya a rubutu to komai ya kare, idan kuwa haka ne alamar zance za ta kasance kafin aya. Wasunsu kuma suka ce, a’a, idan har ba a sa Aya a rubutun ba, yaushe za a gane cewa zance ko, jimla ko maganar ta zo karshe, bare har a sa alamar zancen wani.
Ittifakin da aka yi shi ne, duk ka’idar da ka dauka ka yi amfani da ita an amince. Ana nufin idan ka dauki amfani da Aya bayan alamar zancen wani shi ke nan, imma kuma ka zabi ka yi amfani da sai ka sa Aya kafin alamar zancen wani duk dai Annan wai (makaho ya Yi dare a kasuwa.
(12). KARAN TSAYE KO SANDA JIRGE (OBLIQUE OR SLASH) (/).
Amfanin karan tsaye ko sanda jirge a rubutu shi ne, don a nuna kalmomi biyu ko fiye da haka, wa'yanda su ke da ma’ana iri daya, kuma duk wacce aka yi amfani da ita ta wadatar. Misali:
Ba da/bayar da
Domin/don
Sa da/sadar da.
Kana za a iya amfani da karan tsaye ko sanda jirge a jimla, zance ko magana irin misalan da za su biyo baya:
(1) Ka/ki amsa tambayoyi biyar kawai a wannan sashin.
(2) Ware jinsin ka/ki daga nan: Namiji/Mace.
(3) Wannan sashi an yi shi ne, don Yaro/Yarinya.
(13) DAFI (‘).
Ana amfani da wannan alama a rubutu wajen banbamce wa mai karatu bakake da kuma wasulla da kuma yadda za a karanta a rubutu. Misali:
Ko’ina maimakon koina
Ka’idoji maimakon kaidoji
Ummul’abai’sin maimakon Ummulabaisin.
Ka ga yin amfani da wannan alama ce ya sa ake iya gane yadda za a furta wadannan kalmomi yayin karatu.
Da wanan ne mu ka zo karshen wanan makalar.
na Kuma sadaukar da wanan darasin ne wa ni kaina da Kuma sauran ilahirin al'umar hausawa baki daya.
Wanda a wata fuskar hakan daidai ya ke da in ce na sadaukar da wanan kasidar wa Kai/ke
A Nan na ke Mai cewa sai mun sake jamewa a jadawali na gaba.