Thursday, December 27, 2018

Gabatarwa.

Da sunan Allah Mai rahama Mai Jinkai.
Yabo ya tabbatar ga Allah da manzonsa.

ina mai matukar farin ciki da lale-marhabin ga 
duk WandaYa samu damar ziyartar wanan shafin.Mai suna Kimiyya da hausa.
ko Kuma  ka ce kimiyya a hausance,a
 saukakakken harshe.
Na Gina wanan shafin ne Domin karatu da Kuma karantar
Da Dan abinda Allah ya sanar da ni a fannonin da suka shafi ilimin kimiyya,da ma wa'yansu fanonin daban.
Duba da yadda yarurruka irinsu Hindanci da sinanci ke
Kara samun ci gaba da habaka,a duniyar yau , ya sa  na ji na antaya izuwa duniyar kawazucin harshena .da kuma na tsaya kyam na yi nazari sai na ga cewa eh lallai ya kamata a ce idan da Hali , na Dan yi  wani Abu a Kai. Wanda  hakan ne  ya sa na
Ji cewa, Ya na da kyau a matsayina  na bahaushe ,na dan jarraba
bada tawa gudummuwar ko da kankanuwa ce ,tare da buri da kuma kwadayin  harshen nawa ya Kara samun habaka kamar sauran takwarorinsa.wanda hakan ya sa  na tambayi kaina da cewa, ta wace hanya kenan zan Yi hakan? Kuma ta Ina zan fara?.to a haka dai sai na ga cewa, ko dai zan Fara ne da  'yan rubuce-rubuce a fanonin da su ka shafi na'urar comfiyuta da ma  Wasu daga cikin ilmomin zamani, mussaman masu alaka da kimiyya,?.wato, ta amfanin  da yaren nawa. .domin kuwa a Dan karamin nazarin da na Yi ,a bisa manuniyar ci gaban harsunan duniya,na hakaito cewa duk wani harshe ko yare da  ya samu shahara a duniyar nan,to za ka samu cewa ya samu  nasarar ne a bisa  martabar da ya ke da ita a wajen al'umar duniya.  ita kuma martabar  harshe ya kan same ta ne a ma'unin zunzurutun alakantuwar sa da  rubuce-rubucen fannonin ilmomin da a ka yi amfani da shi wajen wallafa su.domin kuwa a bayyane ya ke cewa yaren ingilishi da larabci,da faransanci duk sun samu shahara da martaba ne a bisa manuniyar kasancewar ,su ne  yarurrukan da a ka fi yin amfani da su wajen wallafe-wallafen  daukacin ilmomin da Dan Adam ya mallaka a Wanan duniyar tamu. Kenan dai hakan kusan manuniya ce da ke nuna cewa ,iya sinkin-sinkin wallafe-wallafen da a ka Yi da harshe ne ke taimamakawa wanan yaren wajen  yaduwa da shahara a fadin duniya.wato ba adadin yawan masu magana da yaren ba.
To sai dai kuma hakan ba ya na nufin Wanan  ce kadai damar da harshe ke shahara ba ,wato da akwai wa'yansu hanyoyi ko damarmakin da a ke amfani da su wajen shaharantar da harshe. kadan daga cikin hanyoyin Kuwa, su ne kamar haka ;
1.fassarra.
2.rubuce-rubecen ilimi.( ta amfani da yaren.)

3.wake/waka.

4.wasan kwaikwayo.hadi da

 5 ..tafiye-tafiye.da Kuma 

6.harkallar cinikayya.

Sai dai a bayyane ya ke cewa ; Fassara ita ce mafi muhimmanci daga cikin Wa'yanan hanyoyin yadawa da habbaka harhse.kuma da ita ce na ke ganin ya kamata mu yi amfani  wajen nemawa namu yaren martaba a idon duniya.wato mu karfafamin zuciyoyinmu wajen kokarin  fassarrawa Hadi da wallafa Wasu daga cikin jerin sinki-sinkin ilimomin da a ka riga a ka wallafa da wa'yansu yarrurukan.wato mu  fassara su izuwa namu yaren.musaman ma na fannonin kimiyya. 
Wanda hakan Kuma, ba Abu ne mai wahala  ba,domin za kusan mu iya cewa ; kowacce rayyayar kalma da ke a cikin kamus din manhajar yarurrukan duniyar nan,idan ka bincika za ka samu cewa da akwai Wacce za ta Yi kusa ko ma dai-dai da ma'anarta a yaren hausa, ta yadda za ta iya maye gurbinta.
Kasancewar yaren namu ya na da yalwar kalmomi daidai gwargwado.sai dai rashin tattalin kalmomin yaren namu,  da Kuma  karancin bincike,da mu ke da shi kan sa mu ga kamar rashin yuwuwar hakan.domin ai idan ka duba tare da yin  nazari a Kai,za ka ga cewa,yaren hausa ya fi yaren sinanci ma'ana da saukin fahimta.amma jajircewar da masu yaren sinancin ke da ita, da Kuma shantakewar mu ne ya taimamakawa yaren sinancin wajen Dame namu yaren ya shanye.domin kuwa a halin yanzu miliyoyin amurikawa da jamusawa hadi  burtaniyawa ne ke zuwa   birnin sin(chana).domin koyo da nazarin yaren sinanci.wanda hakan kusan shi a ke kira da.(, reshe ya juye da mujiya). 
Abinda na ke kokarin bayyanawa a Nan shi ne; matukar mu na so mu daga  martabar yaren  namu, a idon duniya to lallai yin wani abu a Kai ya wajaba a gare mu,,wato  hubbasa wajen ganin an Fara koyarda ilimin fiziya da na likitanci a harshen hausa,ba ma a najeriyar kadai ba,har ma da daukacin kasashen afirika ta yamma,wato(West African countries).

Wanda samun nasarar yin hakan ne zai bai wa harshen namu damar shiga 
 lungu da sako na duniya  a san da zamansa.bugu-da-kari ,kuma hakan zai karawa malam bahaushe martaba a idon duniya.
A takaice dai ,in -so -samu- ne, za mu so a ce;  a na  amfani da harshen hausa a sauran  nahiyoyin gabasci da na yammacin duniya.
(Europe, Asia, Australia, north and south Americans continents)


ASALI.

A ra'ayin wa'yansu da ga cikin malaman falsafar harshe ,na yankin girka,(Greek); sukan ce ; " shi
Harshe ko yare; shi da kansa ne ya ke Gina kansa ,ma'ana,
ba sarakai ko malamai ne ke zaunawa cikin zaure su ce,"
daga yau; a Rika Kiran  kaza da suna kaza ba."a'a, a cewar su ,"kawai dai
 mu'amala da Abu yau da kullum ne da Kuma kamanni da 
yanayin wanan Abin ke sawa a ba wa wanan abin suna mai Kama da yanayinsa.
Sai dai hakan baya rushe cewa ,a Wasu lokutan,a kan kira taron kasa-da-kasa,domin tattauna wa'yansu al'amuran da su ka shafi yaren.wato a kan dai zauna jefi-jefi a tsakanin masana yaren, domin a kakkabawa yaren dokoki da kuma ka'idojin rubutu Hadi da  tantance wa'yansu kalmomin.(wanan a 'yan baya-bayanan kenan ba wai tun a farkon zamanin kafuuwar  yaren ba))

.( Idan mu ka je a darasinmu na gaba Mai taken: 

(KA'IDOJIN KARATU DA RUBUTU A HARSHEN HAUSA,)
za mu Yi bayani Mai Fadi. za Kuma mu fa'idantu sosai.


 A falsafance kuma Idan mu   ka dubi wanan maganar da ke cewa yare ko harshe shi da kansa ne ya ke Gina kansa, , za mu ga cewa; eh lallai  da akwai  Dan kamshin gaskiya a cikin maganar,musaman ma a harshen hausa.domin kuwa idan mu ka kalli wa'yansu kalmomin,tare da yin nazarinsu a falsafance
,za  mu ga  cewa eh lallai kamar ("biri ya Yi kama da mutum").misali kamar ka ce ;
,langa-langa,, laulayi, maloho , mazgewa ,hamago, santalele, karyewa,  botorami, kankamo, suburbuda, da dai sauransu. To Ka ga a nan idan a ka cire son Rai irin na Dan Adam, aKa kuma yi tsai aka yi nazarin
wa'yanan kalmomin, da ma sauran ire'iren su, za  mu  ga cewa ;eh lallai
Sun yi kama da abinda a ka siffanta su da shi. 

A bangaren daya Kuma , duk da
 cewar yaren hausa ba ya da harufa na kashin-kansa,  Wanda kuma  hakan ba
zai bada damar a kira Shi da gurgun yare ba.domin ai idan ka Ware yaren engilishi,da na sinanci da Hindanci da Kuma larabci,to a mafi yawancin yarrurukan da
Za ka ji ko za ka gani ,duk za ka samu cewa sun aro harufa ne a wa'yansu yarrurukan,sai Su ka yi wa harufan 'yar kwaskwarima,da nufin basaja.wato -kamar dai a
Yaren engilishi da faransanci,da Kuma yaren sinanci da japananci,haka-zalika,da yaren hindanci da urdanci.

to sai dai  Kuma a fasali da Zubi irin na siyasar duniya; shi aron  kalma ko  
harufa ,ba laifin ba ne a tsakanin al'umma.musamman ma idan da akwai 'yar wata harkakala ta kasuwanci ko kawance ko Kuma dangantakar addini 

Misalin  aron kalma shi ne; a duk sanda balarabe ya ji; bahaushe ya ce "aljani" to a nan take shi balaraben zai Gane cewa ai kalmar nan ce ta jinni, Wacce kakanin-kakaninsa,su ka kirkira Ko kuma,
suka gina shekara -da- shekaru.,sai ga shi yau wata
kabilar bakar fata , Wacce Babu dangin-iya-Balle-na- baba, ya zo ya sankami kalmar, ya
karye mata wuya da kafafu, ya murdata  domin  shigar da ita cikin 
Kundin jadawali,na manhajar yarensa.
to a Nan  gani kawai
za ka yi, balaraben Nan ya yi murmushi,ya kuma damalmale cikin farin ciki ,irin farincikin da Mai hoharas da Dan kwallo ke ji (coach) yayin da Dan kwallonsa ya Saka kwallo a raga..
Wato balaraben zai yi farin ciki ne ganin cewa harshensa ya zame Abin kwaikwayo,.
 Wanan shi a ke kira da aron kalma na gar-da-gar,domin ai shi mallam bahaushe bai iya nuku-nuku ,ba.to Amma bari ka ji shi gogan naka,,,"wa kenan?",bature Mana,,,"na gane,sai a kafta"...wato shi   mista kyam-kyam," a gimtse!!,ban gane ba,"wa ye musta kyamkyam Kuma?", ,,baturen Mana ,"da Kayau!! A kafta",,, "",,wato shi Mai jajayen kunnuwa,,"  a sake gimtsewa ,,,ni fa ban gane ba,,waye Mai jajayen kunnuwa kuma ?",,hallau dai baturen na ke nufi,",to yanzu Kam na gane,Dan haka  ci gaba kawai da antayo bayanai,ba kakkautawa ,wato a Yi ta antayo su ,ba gimtsewa ba kuma zuwa hutun rabin lokaci.
amma fa a gwari-gwari".

Ina Gaya maka cewa shi bature da ya ci karo da ayaba a wajen bulaguronsa  .,ya kuma duba a cikin kundin kamus din yarensa bai samu sunanta ba,sai kawai ya shiga lalube a  kundin kalmomin yaren larabci,sai kuwa ya same ta .to sai fai kasancewar mutumin naka ya na  da matukar wayo, wato a maimakom ya nema kalmar a larabci ya sankamota kai-tsaye izuwa cikin yarensa a matsayin aro,sai kawai ya ajjiya ta gefe, ya Fara neman sunan yatsun hannu a larabci,domin a hankalce ai yatsun hannu sun yi Kama da  zubin fasalin 'ya'yan ayaba. .sai kawai ya Fara binciken ya a ke Kiran   yatsun hannu a larabci,sai a ka ce masa  (al-ba-nan). A basajance sai kawai ya sankami wanan kalmar ta banan,wato sunan yatsu a larabci ya sankamawa ayabar,inda  ya maida ita banana,.Wanda hakan kenan dai manuniya ce da  ke nuna cewa yaren larabci shi ne gagara-badau a tarihance.

To dan haka ne dai 'yan-uwana hausawa na ke Mai Kira a gare mu, da cewa ;mu Kara karsashi da hubbasa wajen fadadawa hadi daidaita tsayuwar yarenmu, ta yadda zai zamo,zakaran-gwajin-dafi,a cikin harsunan wanan duniyar tamu.
A karo na biyu Kuma wato  a jaddadance na ke kara janyo hankalinmu izuwa ga Wa'yanan hanyoyin , da za su taimaka wajen karawa yaren namu karsashi.wato , su ne dai kamar haka.

1).mu Rika amfani da inganaciyar hausa,wajen rubuce-rubucenmu, na yau-da-kullum, da ma wajen magana..

2).mu yawaita nazari da bincike tare da kokarin kirkiro sababbin kalmomin da za su iya maye gurbin wa'yansu daga cikin kalmomin da mu ka aro daga wa'yansu yarrurukan.
wanda yin hakan Kuma zai  karawa harshen namu fadi da karsashi .wata falallar yin hakan a nan  ita ce; a hukumance ba a biyan harajinl na adadin kalmomin da yare ya mallaka,Wanda kuma hakan a wani kaulin,  manuniya ce da ke nuna cewa ba a fitar musu da zakka ko wakafi.


3).Mu rinka cike dokoki da ka'idojin rubutu ,a rubuce-rubucenmu na yau- da-kullum,.
wato kada  mu bada dama ko taimamakawa wajen a keta-hadin yarenmu,Wanda hakan kusan daidai ya ke da in ce; kada mu bada dama har a samu damar assassa  karyayyar hausa,wato kamar yadda al'umar kudancin najeriya su ka assasa karyayyen ingilishi wato (broken engilish).

4).mu kuma Rika nanatawa da Jan hankali izuwa ga hukumomin da abin ya shafa, kan cewa  a rika maimaita kokarin Nan na jarraba maida tsarin koyar da daukacin ilimomi a yarenmu na uwa, wato hausa.idan  Kuma hakan zai Dan-tada kura ,to sai a Rika karantarwar da dukan yarukan biyu, a lokuta mabanbanta, ,domin yin hakan zai yi matukar saukaka wa yara fahimtar ilimin da a ke so su fahimta a cikin sauki.
Wato ba  lallai sai a tsohuwar turbar da turawan mulkin-mallaka su ka bar mana ba.
domin ai su turawan sun yi hakan ne domin cigaban yarensu da Kuma al'adunsu.kuma ai idan ka duba a kasashe masu tasowa,kamar Hindu,(India).za ka ga cewa da mu da su kasa daya ce ta mulkemu ,wato burtaniya.
 to Amma saboda tsananin kishin kasar su da kuma harshensu da su ke Yi ne,ya sa su ka yi kokarin fassarawa hadi da taskance dukan  fannonin ilimomin da ke da amfani ga rayuwar Dan Adam ,su ka maida su da yarensu na hindanci, wanda samun damar yin hakan ne da su ka Yi,ya  taimakawa kasar tasu wajen cika -da-batsewa a fannonin ilimimomi,mussaman a bangaren kiyon lafiya.
sai dai Kuma hakan ba daidai ya ke da cewa  ba a koyarda karatu da yaren turanci a indiya ba,a'a ,sukan yi hakan domin nishadi. 
Wato hakan daidai ya ke cewa ; ba'indiyen kirki yakan koyi turanci ne domin gudanar da harkallolin Kasusuwanci a ciki da wajen indiya.ba wai domin ya Yi tinkaho da ya iya turanci ba.domin kuwa rinjayen da su ke ba yarensu ne ya sa duk yadda ba'indiye ya shahara wajen iya furta kalaman turanci,da zarar ya Yi turancin za ka gane cewa lallai shi ba'indiye ne.domin akwai kalaman da yarensa na uwa ya Riga da kwace wa harshensa ragamar alhakin furta su.

I ta ma dai  kasar sin wato (chana) da kusan irin Wanan dabarar ta yi amfani wajen inganta kirkire-kirkirenta na kimiyya da fasaha. 
A taikaice dai kusan za mu iya cewa ; duk wata kasa ko al'umar da ka ga ta samu ci gaba,to za ka samu cewa hakan na da nasaba da martabar harshenta, da Kuma baiwa ilimi muhimmanci da al'ummar ke Yi.inda za ka ga cewa tunani da burin gama-garin 'yan kasar da masu mulkin kasar ; shi ne ; TA YAYA ZA A YI KASA GABADAYA TA CI GABA.

Kenan dai mu ma a kasarmu ta najeriyar idan ya kasance cewa;
 mu gama-garin 'yan kasa mu  ka canja kidan,ta hantar baiwa ilimi muhimmanci, to su ma shuwagabanin namu dole ne su canza rawar.
wanda hakan zai ba kasar tamu damar tafiya kafada-da-kafada da wa'yancan takwarorin nata. 
A takaice dai ya na da kyau mu gano  cewa a cikin jerin jadawalin matattakalar cigaban al'umma, ilimi ne kan gaba,ba yawan jam'iyun siyasa  ko adadin al'umar kasar ba.
wato bai kamata mu matasa mu rinka auna gobenmu a ma'unin turbar  shugabaci ko yin arziki a dare daya  ba.
 A saukakkaken harshe hakan na ishara ne da cewa; mu rage bibiyar nasara  kai-tsaye,wato mu fara neman kwarewa da gogewa a wa'yansu fannonin Rayuwar daban-daban.domin idan mu ka ce za mu rinka bibiyar   nasarar kai-tsaye , Kuma a gudane.to faa ,ba za ta bari mu riske ta  cikin sauki ba.amma idan mu ka jajirce muka nemi kwarewa ta wani fanin, to ita nasarar ce da kanta za ta antayo izuwa gare mu.daga nan kuma sai cimma buri  ya kawo kansa izuwa garemu.
Domin da yawa za ka samu cewa  jajirttacin mutane  da dama,a kasashe daban-daban ,ba wai da jadawalin karatun da su kayi a jami'o'i ne kan sa a Basu shaidar darajar karatun dakta ko cansilo ba,.kawai dai ita jami'ar ce da kanta ke yin nazari a bisa fafutukarka a rayuwa,sai tl kawai ta Kira ka ta martaba ka a bisa jajircewar ka wajen ganin ka kawowa kasa ko al'umar ci gaba.
Daga cikin wa'yansu ma za ka samu cewa ba su taba halartar makarantar boko ba,Amma a bisa kyakykyawar zuciyarsu da Kuma kishin a'umarsu da su ke da shi,sai ka ga an Gina jami'a kacokan an  rattaba Mata sunansu.

  wato dai  ita rayuwar Nan kamar ginin bene ce ,shi Kuma bene a mahangar hankali da hangen nesa,zai fi kyau ka jajirce ka nemi hawansa ta mattatakala wato ba ta mahaya ba,(lifter),domin a Wasu lokutan mahar kan iya lalacewa a wani matakin da ba-ka-kasa-ba-ka-sama,Wanda a wani kaulin za mu iya Kiran hakan da tsaka-mai-wuya.daga Nan Kuma saiii...ta Allah
A dayan bangaren Kuma wato idan ka Yi aiki tukuru ka Kuma jajirce ka hayo ta mattatakalar benen ,to lallai ka na da kwarin guiwar cewa: komai daren-dadewa za ka cimma gaci ,a bisa lamuncewar UBANGIJi..

(,,,Amma fa duk wanan 'yar karamar falsafata ce,,,)

 A takaice dai matsalar kasarmu ta najeriya, ba ilimin ne ba mu da kwakwalwar daukar sa ba,a,a. Domin Kuwa a maimakon haka, Kusan za a iya cewa duk wani ilimin Kimiyya da fasahar da ke duniyar nan, za ka iya samun sa kwance a daskare, ya na ta hutawa abinsa a cikin kwakwalwar dai-daikun mu,.sai dai  kasa-a-guiwa da mu ke Yi wajen yadawa da wallafa wanan ilimin izuwa ga sauran al'umar,wanda kuma hakan ne kan zamo sanadiyar rashin morar wanan ilimin.

Wato idan da a ce sinki-sinkin darussan  ilimin da kowannenmu ya fi kaware ne ya ke dabbakawa   tare da yadawa a shafukanmu na yanar gizo da Kuma shafukanmu na sada zumunta,wato a maimakon hotuna da labaran kintacen abin kunyar da wani ya aikata, da mu ke yadawa,to da yanzu an wuce gurin.
domin ai karantarwa tsakanin dalibi da dalibi ta fi inganci fiye da ta malami da dalibi."dalili?",, Dalili shi ne, ai shi dalibi Dan uwanka nee matakin hankali, wanda hakan manuniya ce da ke nu na cewa; za a iya samu cewa kaifin hakaitowa da budewar kwakwalwarku kusan su iya kasancewar a zango da ya .
amma a tsakanin malami da dalibi , za  ka samu cewa da akwai rata mai dan tsawo .kenan dalibi dan uwanka ne zai iya yi maka bayani tiryan-tiryan a irin yaren da za ka fi fahinta ,wato a saukakkaken harshe.

KAMMALAWA.

 A takaice dai 'yan'uwa,  Kira na a gare mu shi ne ; mu maida shafukan sada zumuntarmu su zamo mana makarantunmu.,,, A Nan na ke cewa,,, "a kafta,,,,,

Ga Mai bukatar cancare darussan da ke tafe ,wato ga Mai sha'war karanta wa'yanan darusan da ke  wanan shafin,a harshen turanci ; sai ya antaya  izuwa Wanan adireshin;
www.simplegeneralscience.blogspot.comwww.simplegeneralscience.blogspot.com
ALLah ya sa mu Dace.ameen

Domin neman Karin bayani ko sharhi ,sai a tattaro su a sankama su a cikin akwatin sharhin da ke kasan kowanne darasi.
Ko Kuma a aikace sako izuwa 09035907765.


.

1 comment:

  1. Gaskiyane Allah Yataimaka yakuma kara basira dan uwa,
    A gaskiya naji dadin jin wannan kuma nayadda da abundakace dari bisa dari yasin babu ta akwai bukatar a hausantar da ilmin zamani saboda tahakane zamu samu ingantaccen ilmin dazamu rayuwa yarenmu yayi alfahari damu.

    ReplyDelete