Idan a ka ce kimiyyar rayuwa a na nufin nazari da bincike a kan abubuwan da su ka shafi hallitu masu rai,kamar kwari da dabbobi da tsirrai da ciyayi harma da ciyayyaki.sai dai kuma duba da yadda wanan fanin ya ke da fadi sosai,ga Kuma karanci lokaci.wanda bisa la'akari da wa'yanan dalilan ne, za mu karkata akalar nazarinmu kai-tsaye izuwa ga bangaren da ya shafi halittar dabbobi ,a cikin hallitar dabbobin Kuma za mu Mike ne dodar izuwa ga bangaren da ya shafi hallitar dan adam.za mu yi hakan ne duba da ratar muhimmancin da ke tsakaninsu, .domin Kuwa fahimtar tsari da yanayin gudanarwar masarautar daukacin halittar jikinmu, na da matukar alfanu a garemu.domin ai kamar mota ce , da za ka tuka,wanda sani da fahimtar yadda ta ke gudanar da cakwalkwalin-zagayar-ma'aunin-juyawarta,(4.stroke).ya na da matukar muhimmanci ga kai matukinta.saboda a duk lokacinda ka ji motar ta na kauri ko Kuma ka ji ta Yi zafi,ko ta na kabiri ,Kai tsaye ka San inda za ka dosa.wanan a mota kenan,domin ai shi jikin Dan Adam,cakwalkwalin da ke cikinsa,ya fi na duk wata kerrariyar na'ura da a ka kera ko ma wacce za a kera a Nan gaba. bugu-da -Kari Kuma sanin fasali da yanayin aikin massarrafan da ke jikinmu,zai yi matukar taimaka mana wajen magance afkuwar kananun matsalolin lafiya da ke addabar mu.wanda kuma hakan zai taimaka wajen rage yawan sinki-sinkin fayil-fayil da ke makare a cikin ma'adanan fayil na asibitocinmu.
Kamar yadda na fada a baya cewa Nazarin hallitar Dan Adam,,babi ne Mai fadin gaske, hakan ne ma ya sa hallau za mu antayo bayanai ne a daidai gwargwadon yadda lokaci ya bamu dama.domin idan mu ka ce za mu yi bayanin komai da fadi sosai to babu mamaki babin ya iya daukar mu na tsawon shekaru biyar, ba mu kamalla shi ba.
Darasin namu, zai fara ne tun daga kwayar zarra,(atom),izuwa kwayar hallita wato,(cell)har dai izuwa tantashi (tissue) da masarrafai,wato(organs) daga nan kuma sai mu zo mu yi nazari da bayaninsu daki-daki,wato daya-bayan-daya.
bayan mun caskale Wa'yanan ,sai kawai mu antaya izuwa ga,babin
Tsarin gudanawar jikin Dan adam.wato(human body systems).
No comments:
Post a Comment