MATASHIYAR FARKO.
Kwayar zarra.(atom).
kwayar zarra,wata kankanuwar hallitta ce ,da idon Dan Adam ba ya da kaifin ganinta,sai tare da taimakon na'urar hangen kananun abubuwa,wato (microscope)
duk wani Abin da da za ka gani a duniyar nan Mai cin mizanin muhalli,to za ka samu cewa, hadaka ce ta dubbanin kwayoyin zarra masu adadin madda da Allah ya hallita Kuma ya tattara su waje daya domin Gina Wanan bayyananiyar hallitar
A kiyasance gundarin hallitar dan Adam hadaka ce ta kwayoyin zarra da adadinsu ya kai okutiliyan bakwai.(7,000,000,000,000,000,000,000,000,000,).
MATASHIYA TA BIYU.
Rayyayen tubalin gina hallitta,ko Kuma ka ce kwayar hallita, a saukakkaken harshe.
Duk wani ko wata hallitta mai Rai da za ka gani a duniyar nan, to tabbas za ka samu cewa, hadaka ce ta daya ko sama da dayan Wanan kwayar hallittar.duk da cewa da akwa kananun hallitun da ba su Kai girmanta ba kamar kwayar zarra,Amma kuma; ai sai a nata matakin ne Allah ya Fara sanyawa kananan halittu cikakken gundarin-ruhin-rayuwa, ya Kuma damka mata cikakken'yancin gudanarda rayuwa, ta yadda za ta iya rayuwa ita kadai wato a yanayin tilo da Kuma a yanayin hadakar kawance. To sai dai ita ma ,
2).Romon kwayar hallitta.(cytoplasma).
kwayar hallittar, ta na gudanar da rayuwarta ne,tare da taimakon wa'yansu kananun hallitun da allah ya sanya a farfajiyar zagayyayen gangar jikin kwayar hallitar.inda kowanne daga cikinsu, da akwai gudummuwar da ya ke bayarwa wajen gudanar da 'yantaccen zagayyayen ruhi.muhimmai daga cikinsu, su ne kamar haka;
1).ganuwar kwayark hallitta.
(CELL MEMBRANE)
Ganuwar kwayar hallitta wata katanga ce, da ke zagaye da farfajiyar muhhallin kwayar hallitta.amfaninta shi ne daidaita fasalin kirar kwayar hallittar,da Kuma kula da shige-da-fice na duk wani sinadarin ruwa ko na maiko,Hadi da dakartar da duk wani bakon-haure da ke kokarin shiga ciki,ba tare da izini ko tikiti ba.
romon kwayar hallitta;wa'yansu ruwan yauki ne da ke cikin kawayar hallita,masu dauke da kananun sinadaran gishiri da sukari,da ma sauransu wa'yansu sinadaran. Romon na zube ne kamar karamin kogi,a cikin kwayar hallittar.amfaninsu, dai-dai ya ke da amfanin ruwan kogi a wajen kifi.ma'ana; da su ake amfani wajen wankewa da Kuma tsaftace wa'yanan kananun hallitun da ke cikin kwayar hallitta.
3).kundin sirrin zuri'ar hallitta.(nucleus).
kundin sirrin zuriya; wata karamar hallita ce mai kamar tamola(kwallo),a tsakiyar kwayar hallitta. Ita ce ta ke dauke da karan madarar bayanan siffa da fasalin zuri'a ,wato (DNA).a cikin madarar ne kuma dunkullalun zaruruwan bayanan gadon dabi'u da siffofi su ke.wa'yanda da za a warware su,to da a kiyasance tsawon zaruruwan zai iya Kai tazarar nisan mil miliyan goma.(10,000,000,). amfanin Wa'yanan zaruruwan shi ne; gadar da samfurin hallitar baya izuwa ga na gaba,wato sawwara fasali, daga kakkanni izuwa ga jikokin da za a Haifa Nan gaba.
kamar yadda bayani ya gabata cewa kwayar hallitta; wata rayyayar hallita ce da ke iya gudanarda rayuwarta ita kadai,(uni-cellular) ko Kuma a yanayin hadaka , inda miliyoyin kwayoyin hallita ne, da Allah ya hade su waje daya, domin Samar da wata kamallalliyar hallitta, Mai cike da hikama,wato (multy-cellular organisims).kamar dai ta Dan Adam. Domin a kiyasance kwayoyin hallittu triliyan talatin da biyar ne Allah ya zuba a cikin gangar jikin hallittar Dan Adam,.(35,000,000,000,000').inda ya rarraba musu ayuka daban-daban.
A takai ce dai hallitar Dan Adam ta ginu ne a wa'yansu matakai na hadakar hallittu guda biyar. matakin farko shi ne; matakin kwayar zarra,(atom,Wanda bayaninsa ya gaba, sai Kuma matakin kwayar hallitta,(cell)Wacce ita ma bayaninta ya riga da ya gabata.sai Kuma mataki na uku,wanda za mu Kira; da tantashi.(tissue).Daga Nan Kuma sai mataki na hudu wato massarafa.(organ).mataki na biyar kuma shi ne; tsarin gudanarwar jiki.
(human body system).
A bisa lamuncewar UBANGIJi,bayaninsu zai zo dai-bayan-daya.
MU KASANCE A ANKARE.
Kasancewar da a kwai wa'yansu kananun matakan gina hallittar, Dan Adam da ke kafin kwayar hallitta (cell) izuwa ga kwayar zarra(atom).
mun gutsure su ne kasancewar su ba rayyayu bane,sai mu ka Fara daga masu Rai.ita ma kwayar zarrar mun kawo ta ne domin bada misalin tushe.
Tantashi.(tissue).
MATASHIYA TA UKU.
Domin Allah ya Gina wata hallitar Mai cike da 'yanci da nagarta, wacce za ta iya jure gwagwarmayar Wanan duniyar tamu,sai Allah ya tattaro kwayoyin hallatta masu Kama da juna ya kullamusu kawance da junansu,ya Kuma kaddarta musu wani takamaiman aiki, Wanda zai bada gudummawa da kuma taimakawa wajen gudanarda nagarttaciyar hallitta.
tantashi kamar wani Dan yanki ne daga cikin wata massarafa,kuma iri hudu ne a cikin jikin Dan adam.su ne ; kamar haka;
Tantashin Kashi,
Tantashin tsoka,
Tantashin jini,
Masarrafa.(organ).
masarrafa wata halitta ce Mai fasali da aiki irin na na'ura,Kuma itama hadaka ce ta kwayoyin hallittu, da Allah ya hada a cure waje daya, ya kuma umarcesu da yin wani aikin a tare, da zai taimaka wajen tafiyarda rayuwar dan adam. Da akwai masarrafai da dama a jikin Dan Adam,wa'yanda adadinsu zai iya Kaiwa kimanin tamanin da bakwai,(87).
muhimmai daga cikinsu ,su ne kamar ; kwakwalwa ,zuciya ,huhu ,Koda, hanta da Kuma fata,.
A bayyane ya ke cewa Wa'yanan da mu ka zayyano,su ne su ka fi muhimmanci a godaben tafiyar da rayuwa.Dom su ne idan daya daga cikinsu ya kasa, gudanar da aikinsa,To faa sai... Ta Allah.
Idan Allah ya lamunce mana,za mu daukesu mu yi bayaninsu daya-bayan-daya. Daga nan ne kuma, sai mu antaya dodar izuwa ga matakin karshe,wato tsarin gudanarwa.
Idan Allah ya lamunce mana,za mu daukesu mu yi bayaninsu daya-bayan-daya. Daga nan ne kuma, sai mu antaya dodar izuwa ga matakin karshe,wato tsarin gudanarwa.
(HUMAN body system).
SAI A DAKACE MU,,,,,mu na Nan dawowa.....
Ga Mai bukatar karanta wa'yanan darussan a harshen turanci. sai ya ziyarci dayan shafinmu,Mai adreshi kamar haka;
www.simplegeneralscience.blogspot.com.ko Kuma ka antaya Nan ,domin a rage Maka hanya dodar,,,
Ga mai shawara ko neman Karin bayani, sai a aika sako ta Wanan lambar; 09035907765 /ko
a Wanan akwatin sharhin da ke kasan shafin.
No comments:
Post a Comment