Saturday, December 22, 2018

(6).Sassan jikin Dan Adam da amfaninsusa.(2)

Hanta.:

hanta ko anta wata massarafa ce babba a cikin jikin Dan adam.mazauninta na Nan kasa da huhu,a tsakiyyar ciki.masana sun ce" hanta ta na yin ayuka dai-dai  har guda dari biyar,,   tirkash!!!.
muhimmai daga cikin ayyukan, su ne kamar haka:
1).ita ce ta ke samar da ruwan  kaifi wato ruwan daci,da a ke amfani da su wajen konawa da kuma narka  gundarin abincin da mu ka ci.

2). ita ce ta ke  sarrafawa tare da tace sinadaran abincin da kananun hanji  ke Aiko Mata,wa'yanda su kananun hanjin ke zukowa daga cikin albarkatun  abincin da mu ka ci.wanda bayan ta daidaita mizanin sukari da sauran sinadaran,   sai ta tura tsafttatun sinadaran I Zuwa magudanan jinin da su ka fishing zuciya, domin rarraba amfanin  izuwa ga Sauran sassan jikin gabadaya.
3).Ita ce kuma ta ke taskance wani sinadarin kuzari na sukari domin amfanin ko-ta-kwana,.( glucose)
4).Ita ce kuma ta ke  tace wasu miyagun sinadaran guba daga cikin jini.
5).ita ce take Samar da wa'yansu sinadaran bitamin da jiki ke bukata domin inganta nagartar lafiyarmu.
wanan a takai ce kenan.
wata falallar da Allah ya baiwa hanta,ita ce ; a duk sanda a ka samu wata 'yar matsala har ta Kai ga lalacewa ko rasa wani sashe na hantar.to an hore mata baiwar sake tsirowa da renon kanta har ta samu  ta cike Wanan gibin da a ka rasa. 
  sai dai itama kamar sauran sassan  jikin, yawan shan barasa da kwayoyin magunguna ba bisa ka'ida ba,  kan yi matukar Yi mata illa.
sai a kula.
5).kodoji.
kodoji wa'yansu hallitu ne guda biyu masu kama da fasalin  wake ,da su ke aiki tare, wajen tacewa da wanke jini.mazauninsu na nan a kasan hakarkarin baya,daya a bangaren hagu daya Kuma a bangaren dama.amfaninsu shine; tacewa da daidaita kaurin Jini tare da wanke shi da fitar da duk wata kazanta da sinadaran guba da jiki baya bukata ko Kuma wacce ya Kare amfani da su.su kan  yi wanan aikin ne dare-da-Rana.wato ,sukan tace duk wani datti da kazanta, su antaya shi izuwa mafitsara daga nan be Idan ya tari sai mu kuma  mu antayashi waje a amatsyin fitsari.wa'yansu daga cikin rara ruwan wanke-wanken Kuma, sai su fita ta kofofin fata a mastayin gumi da mu ke yi a yayin da jikinmu ya yi zafi.

6) masarrafar Nika da tace abinci.:

kamar dai yadda Mai karatu ya gani a sama,masarrafar nika da tace abinci, hadaka ce ta sassa da dama.
Amma dai ta yadda abin zai yi mana saukin fahimta , za mu karkasa sassan izuwa gida biyar.
na farko shine
1). jannai;
jannai wani kwararo ne a cikin wuya a bayan makogwaro.,wato wata  rariya ce da ta hada  baki da tumbi.amfaninsa shine karbowa Hadi da turo abinci ko ruwan da mutum ya hadiya.ya na yin hakan ne a yanayin tatsowa , ya kan ingizo lomar abincin har i Zuwa tumbi . na biyu  Kuma shine 
2).tumbi;  tumbi wata jaka ce mai fasali kamar na mangwaro.  aikin tumbi shi ne  ; darkakewa Hadi da cakuda lomomin abincin da mu ka ci. ya na yin wanan aikin ne tare da taimakon wa'yansu ruwan kaifi masu daci,(acid) da hanta ke samarwa domin yin wanan amfanin.
sai  Kuma na uku, shi ne

3). kananun hanji:wa'yansu kananun korarai ne da ke laulaye a rubanye, tsawonsu ya Kai  kafa 22 . a cikin su ne ake markadewa Hadi da zuke  duk wani  sinadari mai amfani ,da ke cikin abincin da mu ka ci.
daga Nan Kuma sai 
4).manyan hanji; manyan hanji ; su mu ke Kira da umbullulluki,za ka gan su a zagaye da kananun hanji.  aikinsu shi ne su Kara tsotse duk wa'yansu  ragowar sinadarai da Kuma sauran ruwan da su ka rage a cikin Wanan nikakken dusar abincin.daga nan Kuma sai su tura Sauran I Zuwa zango na gaba.
wanan zangon Kuwa shi ne 
5).dubura,inda a nan ne ake   yin bankwana da dusar, sai a fitar dashi a matsayin Kashi.

domin kula da lafiyar manikar abinci sai a rika cin abinci lafiyayye mai kunshe da sinadaran da jiki  ke bukata,wato (balance diet).tare da yawaita cin kayan marmari da kuma kayan lambu.

ga Mai bukatar karanta Wanan darasin, a harshen ingilishi,sai ya shiga ta nan,.

Ga Mai neman Karin bayani kuma ko sharhi ,sai ya cike wanan akwatin.ko ya  aika sakon tex ta 09035907765.

No comments:

Post a Comment