Saturday, December 8, 2018

(20).Tsarin mabbubugan madarar maganadisun umarni.

Tsarin mabbubugan madarar maganadisu,wani tsari ne da allah ya shirya a jikun dan Adam musamman domin ragewa kwakwalwa aiki.ta hanyar nada wasu wakilai da ta ke aikawa izuwa ga wa'yansu sassan Jikin ,domin gudanar da wani aiki na dindindin ko Kuma na wani Dan lokaci.kamar dai a  rijiya ko marmaro,inda  za ka samu ruwa na ta bubbugowa ta wa'yansu kananan ramu,Wanda a saukakkaken harshe mu ke Kira idon ruwa.to a jikin Dan Adam ma haka abin ya ke,da a kwai wa'yansu kananun massarrafai da  ke fitar da wa'yansu ruwan sinadarai.wa'yanan ruwan sinadaran,su mu ke Kira da;  ruwan-sinadaran-madarar-maganadisu wato (hormones),ruwan sinadarai ne  nau'i daban-daban,da su ke  amfani daban-daban.kamar dai a tsarin ma'ajiyar kudi(bank).,inda za ka samu cewa an saita na'urar-cirar-kudi(ATM),ta yadda za ta  Yi ta baiwa mutane kudi ba-dare-ba-rana.amma Kuma ai ta na yin Wanan aikin ne a bisa umarni na dindindin da a ka shigar Mata da manhajarsa,wato ,(app) an Kuma shigar Mata da bayanan ne a yaren da zata iya ganewa,wato(programming language) to,a haka za ka ga cewa ai ta ragewa ma'aikatan banki aiki. tunda alokacin da ta ke yin Wanan aikin,ai ba kowa a cikin banki.me yiwuwa ma manaja ya na can ya na bacci abinsa.to haka ita ma kwakwalwa ta ke shirya wa'yansu bayanan sirri ta wani irin yare Wanda zai karantu ne kawai ga massarrafar da aka aikawa shi.
Wato yadda abin ya ke shi ne: kwakwalwa bayan sakonnin lantarki da ta ke aikawa izuwa ga sassan jiki,ta kan kuma aika wani nau'in sakon izuwa ga wa'yansu masarrafan ko sassan jiki,ta hanyar amfani da wa'yansu ruwan-madarar-maganadisu.duk da cewa ruwan ba Kai tsaye su ke fitowa da ga kwakwalwa ba,Amma dai ita ce ke ba da umarni ga masarrafan da ke fitar da ruwan.misali,a duk sanda mutum ya ga abin tsoro, har ya firgita,to Nan take kwakwalwa za ta bada umarni ga wata mabbubugar madarar maganadisun da ke saman Koda,(adrenal gland) da cewa ta saki madarar-maganadisun-kara-kuzari.Wanda amfanin Wanan madarar shi ne, ta zaburar da kowacce masarrafa domin ta kawo dauki ta yadda jiki samu damar tsallake hadari.to a irin Wanan yanayi,da zarar madarar ta fito,za ta shiga cikin magudanan jini,inda za su bazu ta ko'ina,har su Kai ga zuciya su harzukata domin ta harba jini da sauri,daga Nan sai ga huhu,shi ma su harzuka shi,.sai su sake ba wa jiki umarnin da Cewa a juya akalar jini izuwa ga inda a ke bukatar shi,wato izuwa tsokar Kashi,(skeletal muscles). ta haka dai za su ankarar da duk daukacin jiki,har a samu a tsallake Wanan hadarin.da ga Nan Kuma sai kwakwalwa ta sake bada umarnin cewa kowa ya  koma a bakin aikinsa,(irin na yau-da-kulllum.)
 Kenan dai A takaice za mu iya cewa amfanin madarar maganadisu shi ne ; gudanar da wani aiki Wanda tuni Allah ya Riga da ya tsarawa madarar yadda zata ta Yi shi ,da Kuma a Ina za ta Yi shi har ma da wanne lokaci  za ta Fara da Kuma yaushe za ta Kare aikin.
Kamar a tsarin mulki su ma mabubbugan maganadisu ,mataki-mataki su kegudanarda aikinsu,wato kamar a tsarin sarauta.da akwai sarki da hakimi har  izuwa Mai anguwa.kenan akwai mabubbugan, koli akwai ta tsakiya akwai Kuma ta kananun masu karamin karfi.wa'yanda su na yin aikinsu ne a bisa umarnin ta tsakkiya.wanda ita Kuma ta tsakkiyar ,ta na yin aikinta ne a bisa umarnin turken kwakwalwa da ke can saman haba.
duba  da karancin lokaci,za mu dauki muhimmai daga cikinsu mu Yi bayaninsu dai-dai gwargwado.
1).Mabubbugar turken kwakwalwa.(pitotary glan)
Mazauninta na nan ta a tsakiyar Kai ,a ta karkashin,amfaninta shi ne bada umarni ga Sauran kananun mabubbugai, da ke sassa daba-ban a cikin jikin Dan Adam.
2).Mabubbugar tauro.(thyroid gland)
Mazauninta na nan kasan akwatin sauti manne da makogwaro.ta na fitar da sinadaran maganadisu da dama,daga cikinsu a kwai masu daidaita zafin jiki da masu saita bugun zuciya da Kuma masu habbaka girman jiki da dai sauransu.
3).mabubbugar andanal.(adrenal gland)
Mazauninta na Nan a saman kodoji.su ma su na fitar da sinadarai da dama,daga cikinsu akwaia na zaburar da jiki,da Kuma na Kara kuzari da na saita kaurin Jini,da dai sauransu.
4)Mabubbugar saifa.(spleen)
Mazauninta na Nan kusa da hanta,domin ita ma massarafa ce Mai zaman kanta,domin ita ce ke Samar da madarar-maganadisun-daidata sukari a cikin jini,wato (insulin)da Kuma wa'yansu asid..ita ce ma idan ta samu tangarda wajen fitarda Wanan sinadarin-maganadisun,sai ka ji an ce ka na da ciwon suga.
5).Mabubbugar makyankyasar mahaifa.(ovaries).
Mazauninsu na Nan a bangarori biyu na kafadun mahaifa. Su ma dai  su na fitar da sinadaran maganadisu da dama.  su ne su ke fitar da madarar maganadisun macantaka,wato (estrogen). amfaninsu shi ne bayyana sifar mace tare da jujjuya hallitun jikin mace.
  (musamman a lokacin balaga).su na kuma fitar da sinadaran da ke kula da kyankyasar Kwan mace da Kuma na shayar da nono har ma da masu kula da al'ada.
6).mabubbugar 'ya'yan maraina.(testicle)
Mazauninta na Nan cikin 'ya'yan-maraina.ita ce ta ke fitar da sinadaran-maganadisun-mazantaka.(frototestereon).amfaninsu shi ne bayyana sifa da dabi'un namiji,musamman a lokacin balaga.su su ke da alhakin bayyana hallitar namiji,hadi da jujjuya ta.kamar zaburarda girman jiki yayin balaga da kuma kausasa murya,hadi da fitar masa da gashi a wasu wuraren,da bijiro Masa da sha'awa,wanda daga Nan sai tunanin aure ya Fara bijirowa.

Ga Mai bukatar karanta Wanan makalar a  harshen su kyam-kyam,sai ya latsa nan domin a rage Masa hanya,dodar izuwa ga dayan shafin.
www.simplegeneralscien.blogspot.com.
Domin shawara ko gyara ko tsokaci Kuma ,sai a antayasu a Wanan akwatin sharhin ko Kuma sankama sakon kai-tsaye da,09035907765.idan Kuma Babu ko days,,sai. In ce Sai mun jamee...a darasi na gaba...kafin nan Kuma na ke cewa fatan alkhariii.

No comments:

Post a Comment