Wednesday, December 12, 2018

(16).Zubi da tsarin tsoka a jikin Dan Adam.

Tsarin tsoka a Jikin Dan Adam wani tsari ne da a ka Yi domin sarrafawa da jujjuya jikin Dan Adam gabadaya.masana falsafar jikin dan adam ,sun rarraba  tsoka izuwa nau'i uku.su ka ce kamar haka:
1).tsoka Mai laudi.
Tsoka Mai laudi: ,ita ce tsokar da aka yi amfani da ita wajen Samar da daukacin masarrafai da sassan da ke cikin kusurwar jikin Dan adam.wato,kamar hanji, huhu, tumbi,dubura da dai sauransu.amfanin Wanan tsokar shi ne amfanin wa'yanan masarrafan.kwakwalwa kuma ita  ce ke kula Hadi da sarrafa ayyukan Wa'yanan tsokokin.wanda aiki ne Kuma na dindindin.ya kan Kuma gudanu ne,ba tare da saninmu ko umarninmu ba.
2).tsoka Mai gautsi.
Tsoka Mai gautsi wata tsoka ce mai gautsi da santsi Hadi da kuma laushi, da aka yi amfani da ita wajen kera zuciya da murfinta.amfaninta shi ne harba jini izuwa ga sauran sassan jiki .ta na Kuma karbar umarnin Wanan aikin ne daga kwakwalwa Kai tsaye,a yanayin lantarki,duk da cewa dai ita ma zuciyar ta na da nata masuburbudar lantarkin. A wani binceke ma da a ka fitar a kwanan baya,ya nuna cewa zuciya  ta na sarrafa wani nau'in tunanin Hadi alkinta wani nau'i na dawwammamen tunani.
(3).tsokar Kashi.
Tsokar Kashi, wata tsoka ce mai laushi da gautsi hadi da tauri,da aka yi amfani da ita wajen tallita gundarin surar fasali da zatin  Dan adam.tsokar kashi da ita ce  mu ke amfani wajen gudanar da duk wasu ayyuka na zahiri a harkokinmu na yau- da kulum.kuma an kirata da tsokar Kashi ne, kasancewar a duk inda za ka ganta,to za ka samu cewa,ta na manne ne a jikin wani Kashin.hakan kuwa manuniya ce da ke nuna cewa su biyun abokan aiki ne , na kut-da-kut.woto daya daga cikin su, ba zai iya gudanar da aikinsa ba idan ba daya.hakan ne ya sa , a duk inda za ka ga Kashi a jikin Dan Adam,to za ka samu cewa an kulla Masa kawance ko aure  da tsokoki guda biyu ko  fiye da hakan. hakan ne  ma ya sa  adadin tsokoki a jikin Dan Adam ya ribanya adadin kasusuwa.inda adadin tsoka ya ke, dari  shida da ashirin da biyar(625,).yayin da shi Kuma adadin Kasusuwan, ya ke( ,300).(a kiyasance).
yadda abin ya ke shi ne; tsokar Kashi ta na yin aikin motsa jiki ne,ta hanyar dunkulewa  ko tamurewa,da Kuma warwarewa.kamar dai yadda za ka gani a irin motar Nan da ke sankamar kayan nauyi,wato (cran).to ita ma tsoka kusan a irin haka ta ke gudanar da nata aikin.sai dai su tsokoki a nasu tsarin , sukan gudanar da aikin motsi ko tankwara Kashi ne a hadaka ko kawancen tsokoki akalla biyu, ko  fiye da hakan. ko wacce tsokar daga ciki ,za ka ga an kafa Mata turakun jijiyoyi biyu  a jikin kasusuwa,(kamar a irin daurin cingam).. za ka ga an  shimfida tsokokin, daya a saman kashin, daya kuma a kasa.su kan motsa kashin ne a duk sanda daya ta tamure,domin tallafo kashin, ita kuma dayar, a dai-dai Wanan lokacin ta ke warwarewa.misalin shi ne;  a zira'in hannu.idan ka duba a zira'in hannu za ka ga cewa tsokoki biyu ne ke manne a Jikin damtsen, da ya a saman dantsen hanun, daya Kuma a kasan damtsen.tsokar saman dantsen, za ka ga an kafa Mata turaku, guda biyu, turke daya a karshen kashin kafafa,dayan Kuma an kafa shi ne a can wajen karshen kashin damtsen,wato can wajen guiwar hannu. Hakan na nufin kenan a duk sanda za ka daga hannunka sama,to Wanan tsokar ta sama ce ke dunkulewa,wanda a dai-dai lokacin ne ita Kuma tsokar da ke kasan damtsen ke warwarewa domin ta baiwa tsokar saman dantsen damar tankwara hannun,Wanda hakan Kuma,zai bawa hanun damar dagowa da ga yanayinsa na warwas..to ita ma dai tsokar saman damtsen hakan  ta ke yi wa ta kasan irin Wanan karar,idan ta bukaci janyo hanun izuwa kasa.
A tsarin tsokar Kashi ,duk Wani juye-juyen da tsokar Kashi za ta Yi a jikin Dan Adam,ta na yin sa ne a bisa umarni da Kuma kulawar tunaninmu.wato ta na aiwatar da ayukanta  ne a bisa tunani da yanke hukunci da ke fitowa daga kwakwalwa.umarnin kuma na zuwa ne  a yanayin lantarki.shi ya sa ma idan ka duba a cikin tsoka za ka ga wayoyin lantarkin  lakka a warwatse.
A takaice dai a gabadayan tsarin gudanar da tsokar Kashi,hankalin mutum ne ya ke ba da cikakken umarnin  kaftawa da gintsewa.

ga Mai bukatar karanta wanan darasin a harshe turanci,sai ya latsa Nan, domin a rage Masa hanya dodar izuwa dayan shafin.
Domin yin sharhi ko gyara,sai a cike akwatin sharhin da ke kasan shafin..
A Nan na ke cewa sai mun sake jamewa a darasi na gaba ,,,,

No comments:

Post a Comment