Monday, December 10, 2018

(18).Tsarin garkuwar jikin Dan Adam.

tsarin garkuwaar jikin dan adam,wani tsari ne  na  mussaman da allah ya shirya a jikin dan adam, domin bada kariya, da kuma yakar kwayoyin cutar da ke kokarin kawo  farmaki wa masarautar jikin Dan  adam din.kammar   yadda za ka samu a  duk wani  kamallalen gari. za ka samu cewa da akwai jami'an tsaro na madakatai da Kuma masu sintiri a cikin garin. Aikinsu kuma shi ne,sankame duk wani bakon hauren da Basu tatance  asalinsa a  garin ba.,inda za su kwamashe shi, su Yi awon gaba da shi.to haka abin ya ke a  masarautar jikin dan adam. Wato duba da yadda duniyarnan ta ke cike  da bakin-haure, da kuma 'yan-sara-suka. Kasancewar Kuma hallitar Dan Adam hallita ce Mai matukar daraja.wato idan a ka ce , a bar ta kofa-a-bode,to Babu mamaki ya zama cewa Dan Adam din ba zai iya  samun damar gudanar da rayuwar sa ba, Koda kuwa na tsawon wata daya ne .domin kuwa  sararin Wanan duniyar tamu,cike ya ke da hallitun da Allah ne kadai ya San adadinsu. Da a kwai wa'yanda ido ke iya gani da Kuma wa,'yanda ido ba ya iya gani.kasancewar Kuma tsarin neman abincin hallitun duniyar Nan, ya  ,na tafiya ne bisa turbar dimukuradiyar cewa;  na sama ya cinye na kasa.sai dai kuma daga cikin hallitun duniyar, da a akwai wa'yansu kananun halittun.wa'yanda Ido ma ba zai iya  ganin su ba.kuma wasan da su ka  fi sha'awa shi ne; juyin-mulki.ma'anar juyin mulki shi ne; a ra'ayinsu su kan so su shiga cikin gangar jikin Dan Adam,ta karfi, su Kuma Yi kokarin kwace sarautar jikin daga kwakwalwa,tare da dagulawa sauran masarrafai da tsarurrukan jikin lissafi.ta haka dai  su ke dagewa domin ganin sun Kai mutum kwance,daga Nan Kuma sai .....ta Allah.
A bayyane ya ke cewa, domin Allah ya martaba Dan Adam a doron duniya, sai ya ba shi nagartar sarrafa hallitun da su ka fi shi girma da karfin-cin-tuwo. A dayan bangaren  Kuma domin Allah ya nunawa Dan Adam din cewa , shi Mai cikakken iko ne a kansa,sai ya hallici wa'yansu kananun hallitun da ido ma ba zai iya ganinsu ba, sai kuma ya Basu karfi da dubarun Kai farmaki, ta yadda kwaya daya daga cikin su, zai iya zama barazana wa lafiyar Dan Adam, da ma rayuwarsa bakidaya.woto kamar yadda shi dan adam din ya ke barazana ga wasu hallitun da su ka fi shi girma da karfi.to sai dai kuma a irin tsarin   Allah,za ka ga cewa a Wasu lokutan idan ya jarabe mu  da wata fitana ko masifa,to za ka samu cewa  a dayan bangaren kuma Allah ya ba mu  hanyoyin kariya ko  magance wanan fitinar.Wanda za ka ma samu cewa, maganin ne farko kafin fitinar ta kunno kai.
To hakan ne dai ,da Allah ya tashi hallittar Dan Adam,sai ya gina masa wani tsari na mussaman a jikinsa,Wanda zai zamewa Dan Adam din garkuwa domin kiyaye lafiyarsa,ta yadda zai samu ya bautawa Allan a cikin nutsuwa da salama. Kamar dai yadda za ka gani a tsarin tsaron kasa ,inda za ka ga an rarraba  jami'an tsaro a madakatai da na bakin iyakar gari da masu sintiri a cikin garin.to kamar haka shi ma tsarin garkuwar jikin Dan Adam ya ke.
Wanda hakan manuniya ce da ke nuna cewa,rundunonin tsaron farko da na karshe masu Kare farmaki ,sun kwaikwayo salo da dubarun tsaronsu ne da ga irin fasalin da Allah ya tsara a Jikin  Dan adam.
Wato a Jikin Dan Adam, Allah ya hallici wa'yansu kananun hallitu da masarrafai ,wa'yanda aikinsu shi ne sankamewa Hadi darkake  duk wata kwayar cutar da ke yunkurin kawowa jikin Dan adam farmaki.
Hakan na nufin gangar jikin hallitar dan adam ta na dauke  da sojojin-kare farmakin magauta. ba Kuma  a waje daya su ke dinkim ba,a rarrabe su ke.wato Daga cikinsu akwai  masu tsaron kofa ,da masu kula da madakatai,da Kuma masu sintiri. Domin mu samu saukin fahimtar lamarin  , Za mu dauki muhimmai daga cikinsu mu Yi bayanin a Kai.

1)Karan gashin hanci.: 

Karan gashin hanci wa'yansu karan gasu ne da a ka shuka  a cikin hancimu, su na bada Kariya ne wajen tace duk wani datti ko bakon haure da ke boye a cikin iskar da mu ke shaka. Bakin hauren kan buya ne a cikin iskar da mu ke zukowa yayin numfashi,sai su biyo iskar da nufin  antayawa cikin huhu tare da Wanan iskar sinadarin oksijin da mu ke zukowa yayin numfashi.su na kuma kokarin  shiga huhun ne da nufin tayar da zaune-tsaye wato da nufin wanzar da akin ta'addanci.domin kuwa shigar su ke da wuya na Dan wani lokaci, za ka ji ka Fara tari,to daga Nan kuma bayan kwana biyu  sai kawai ka ji ka a warwas.
Wanda hakan zai tilasta dole sai an Nemo sojojin haya daga wata kasar,wato,ta hanyar antaya 'yan kwayoyin magani,har dai a samu a ci karfin bakin hauren.

2).yawu.:

a cikin yawun da bakinmu ke fitarwa  ,da,akwai sinadaran da ke kashe  kwayoyin cutar  da ke , kokari antayawa cikin jiki, da nufin Kai farmaki.

3).hakin wuya.

:a can wajen karshen harshe,da akwai wata 'yar karamar hallita,wacce aikinta shi ne,sankame duk wata kwayar cuta da ke kokarin shiga cikin jikinmu,."wajen me?" da nufin daukar  fansa Mana,"wace fansa Kuma?",fansar 'yan-uwansu Mana,"kamar ya?",wa'yanda mu ke yiwa kisan kiyashi yayin da mu ka zo  tsaftace ruwan da mu ke Sha, ta hanyar amfani da madarar sinadaran kashe kwayoyin cuta,ko Kuma Kona su da wuta."okkk".a kafta,,"

4).majina:

majina wata madarar Danko ce da jiki ke fitarwa domin wankewa Hadi da share duk wani datti Mai dauke da kwayoyin cuta,har ma da Wanda ya shigo a hannu-rabbana,idan majinar ta sankame kwayoyin cutar, sai ta Dan yage mu haka.inda daga nan mu Kuma sai mu fara kokarin tari domin antayo su waje tare da majinar,sai kawai ka ga sun fito a muzance,.a Wasu lokutan Kuma atishawar da mu ke yi ce ke harbo kwayoyin cutar.

5).sifililis:

Sifililis , wata 'yar karamar hallita ce a gefen hakarkari hagu ,amfaninta shi ne Samar da wa'yansu nau'in sinadaran yakar kwayoyin cutar da  ke kokarin kawo Mana farmaki.domin ai duk da tsaron da  ke bakin kofofin shiga jikin, wa'yansu kwayoyin su kan samu damar shigowa,ta cikin jiki,a barauniyar hanya,wato ta cikin abincin da mu ke ci,ko Kuma ta gurbattatun ruwan da mu ke Sha.

6):tamashi: 

shi ma dai  wata hallita ce mai fasali irin na mallam-buda-littafi.mazauninta na can manne da makogwaro. ita ma aikinta shi ne gano duk wani bakon haure da ya keto ta cikin jiki,ta hanyar Jin rauni ko kuma ta basaja.

7).fararen kwayoyin Jin:

fararen kwayoyin jini wa,'yansu kwayoyin hallitu ne na mussaman masu aikin sintiri a ciki n Jikin Dan Adam, da aka hallitta domin yaki da kwayoyin cuta.amfaninsu shi ne hadiyewa gami da darkake duk wata kwayar  cutar da ta samu shigowa ta cikin jikin Dan Adam.
Idan a na maganar karfin nukiliyar jikin Dan adam. To fararen kwayoyin Jini,su ne sojojin gasken,
  Domin a wasu lokutan idan su na fafatawa da wa'yansu kwayoyin cutar , za ka ji jikinka ya dauki zafi,wanda mu ke kira massassara. Wato massassara ba komai ba ce face zafin turnuku. A Wasu lokutan kuma idan  rauni ne mu ka samu,zuwa Dan wani  lokaci kadan ,idan Jinin ya tsaya,za ka ga wa'yansu fararen ruwa na fitowa ta cikin raunin.to wa'yanan fararen ruwan,ai gawarwaki ne na sojojinmu,wato fararen kwayar hallitar jini. domin ai su dama kwayoyin cutar su na Nan biye da mu ta ko'ina a Jikinmu ,jira kawai su ke dama ta samu. da zarar mun Dan kuje ko yanka,to Nan ta ke za su antayo cikin jikin. To A Nan Su Kuma kwayoyin fafararen jini sai jiki ya Yi shelar cewa  ;da a kwai fa matsala a waje kaza,sai kwayoyin fararen Jini da kuma kwayoyin dankon Jini su taru a je wajen a Fara tafka gumurzu.kwayoyin dankon Jini wato,(platelets),za su Fara kokarin tsaida zubar jinin,su Kuma fararen jinin ,za su Fara caskalewa,da Bakin-hauren. To a Nan ne dai za a samu gawarwaki, ta kowanne bangare.wato  atakaice dai  Wanan zafin da jiki ke yi yayin rashin lafiya, wanda  mu ke cewa massassara,ba komai ba ne face zafin turnuku,da caskale a tsakanin, sojojin fararen jininmu da kuma kwayoyin cuta., idan kuma ka ji zafin ya wuce kima,to alamu ne da ke nuna  cewa, wa'yanan kwayoyin cutar sun kusa cin galaba a kan sojojinmu,wato,(fararen hallitun jininmu). Ana haka ne sai kawai ka ji ka a warwas. Wanda hakan manuniya ce da ke nuna cewa fa dole da bukatar a nemo hayar sojoji masu karfin tsiya daga wasu kashen,wato ta hanyar antaya magunguna da allurai.har dai a samu a fattataki kwayoyin cutar.su tattara-nasu-ya-nasu su fece.wanda hakan kuma zai baka damar cancarewa,  ka cigaba da ko-dimo abinka,,,

RIGAKAFI.
RIGAKAFI,:wani nau'in ne na bada kariya ga lafiyar Dan Adam,mussaman a kananun yara.,kuma Allah ne ya hore ilimin yin hakan ga Dan adam.kamar dai yadda a ke horar da  jami'an tsaron soji ko na 'yan-sanda.to haka shima RIGAKAFI wani nau'i ne na baiwa sojojin  jiki horo.(anti-bodies). Kuma kamar yadda mu ke gani, RIGAKAFI ba nau'i daya a ke Yi ba,akan Yi wa yaro kusan nau'o'i goma ko fiye da hakan.dalilin yin hakan shi ne ; kowacce kwayar cutar da nata horon daban.kenan iya adadin allurai iya adadin kariya. Akan ba sojojin jiki horon ne ta yadda za su yiwa kwayar watar cutar aika-aika ko Kuma mu ce sambadebade wato idan tsautsayi,ya hada su,a wata ranar.  Sai dai za ka ga cewa ita allurar ko maganin RIGAKAFI,an fi yin ta ne ga kananun yara.dalilin hakan shi ne ; bahaushe kan ce "a kan lankwasa geza ne yayin da ta ke danya".domin ai shi a babban mutum,jikinsa ya wuce daukar horasawa.
 Wato yadda abin ya ke shi ne,;a kan kamo wata kwayar cuta ne,wacce ta ke matukar addabar yara,sai a daure Mata kafafu da hannuwa,ta yadda ba zata iya koda wani dogon motsi ba,sai a antaya ta cikin jikin yaro , ta hanyar allura ko magani , a kan kuma yi hakan ne a lokacin yarinta,wato a dai-dai lokacinda jikin yaron ke kera sojojin-garkuwar-jiki.to da zarar an sanya Wanan kwayar cutar a daddaure.da zarar ta shigo Jikin yaron,sai kawai jiki ya ankare da ita,sai kawai Nan take Jikin  ya fara kera sojojin da za su Yi watandar wanan kwayar cutar, wato su kundumeta.
to daga Nan ita wanan nau'in kwayar cutar idan aka sake jamewa watarana,to jiki ba ma ya kallonta a matsayin wata barazana,.wato Koda ma ta samu damar shigowa cikin jikin yaron , ba za ta sa ke yin tasiri a jikin yaron ba,har-gaba-da-abada.
Wato 
Kenan dai sai...ta Allah .

ga Mai bukatar sake jamewa da Wanan makalar, a harshen ingilishi, sai ya ziyarci dayan shafinmu,a
Ga Mai shawara  ko gyara ko neman Karin bayani, sai ya antayo sako Kai-tsaye izuwa 09035907765.
Ga Mai Sharhi ko tsokaci,kuma sai ya antayasu a cikin akwatin sharhin.da ke kasan shafin ,daga karshe Kuma Ina mai
Fatan alkhariii izuwa gareka/ki,,,

sai Kuma mun sake  jamewa a darasi na gaba.

No comments:

Post a Comment