Thursday, December 13, 2018

(15).Tsarin kasusuwa a jikin Dan adam.

Tsarin kasusuwa ko Kuma tsarin kwarangwal.wani tsari ne da aka shirya domin ya zama gimshiki ko dirka wa hallitar gangar jikin Dan adam.kamar dai a zubi na fasalin kirar lema.inda za ka ga cewa,wa'yanan karafunan da ke cikin lemar ne ke sarrafawa  Hadi da baiwa  gangar jikin lemar kariya.
kashi wani nau'in ne na kwayoyin tantashi,masu tauri, da su ke aikin taimakon kai-da-kai domin zamewa gangar jikin Dan Adam dirka,ko majingina da Kuma bada kariya ga wa'yansu muhimman massarafai da basa iya jure cakwakiyar wanan duniyar tamu.(organ).

Amfanin kashi.
Kamar yadda bayani ya gabata, amfanin kashi shi ne:tallafewa da sarrafa motsi na zahiri Hadi da bada kariya ga jikin Dan Adam.yakan Kuma taimaka wajen ajiye wa'yansu sinadaran albarkatu,da su ke Kara kwarin  da Kuma GIRMAN kashin,wato (calcium).a wasu Kasusuwan Kuma wato masu dauke da bargo su kan taimakawa wajen  kyankyasar kwayoyin halittar jajayen jini,har ma da fararen.wani nau'in na Kashi Kuma kan ajiye maiko domin amfanin gaba.
 muhimmai da ga cikin Kasusuwan jikin Dan Adam su ne kamar haka;

1).kashin kokon Kai.:

kasusuwa ne guda ashirin da biyu,22,da su ke manne da juna domin samarwa kwakwalwa muhalli tare da Bata  kariya.sai Kuma kashin habar kasa, da mu ke aikin tauna da su,da Kuma wa'yansu kananun Kasusuwan da ke can cikin kunne.ko me ye aikinsu??? "ohho".Amma dai idan karatun namu ya je ta kan kunnen,za mu ji amfanin Wa'yanan kananun Kasusuwan.

2).kashin baya.

Kashin baya hadaka ce ta guntayen kasusuwa Hadi da dandatsi a tsakaninsu ,su na aiki a goye da juna ne domin samarwa jelar kwakwalwa muhalli,da Kuma samar da dirka daga kashin kwankwaso izuwa ga kashin kokon Kai.

3).Kasusuwan hakarkari.

Kasusuwan hakarkari wasu kasusuwa ne,,da aka yiwa  huhu da zuciya rumfa ,da ma Sauran hallitun da ke cikin kirji.an haka rumfar ne, domin Samar musu da muhalli Hadi da Basu kariya.an kafa kasusuwan ne, daga kashin baya,izuma ga kashin dandatsin kirji.ta yadda za su iya ba huhu damar kumbura da Kuma sacewa.

4).Kashin zira'in hannu.

Kasusuwan zira'in hanu, wa'yansu kasuwa ne guda talatin, masu tsawo guda uku ,3, da Kuma gajeru guda ashirin da bakwai ,27,amfaninsu shi ne samar da motsin hannu da Kuma tallafawa wajen baiwa hannu damar gudanarda ko wannne irin aiki, musamman ayyukan da a ke yi da karfin cin tuwo.dogayen kasusuwan na hannu masu dauke da bargo Kuma kan taimaka wajen kyankyasar jajayen kwayoyin hallitar jini.

5).kashin zira'in kafa.

Kashin zira'in kafa,wasu kasusuwa ne guda talatin.su ma dai guda uku 3,dogaye ne .guda ashirin da bakwai ,27 Kuma gajeru.amfaninsu shi ne;  tallafe jiki, da Kuma bada damar tafiya Hadi da dai-daito.su ma Kuma , su na  dauke da jajayen bargo a cikin su,Wanda hakan na nufin a cikin su ma a na kyankyasar kwayoyin jini.

6).Kashin kwankwaso.

Kashin kwankwaso:wani Kashi ne da ya hada kasusuwan cinyoyi da kashin baya,Kuma shi ya ke taimakawa wajen dai-daituwar mutum,atsaye ko  a zaune.a duk cikin Kasusuwan da mu ka yi bayaninsu,duk iri daya ne tsakanin na namiji da na mace,sai dai ka samu dan banbancin girma.Amma a fasalin kashin kwankwaso,za ka iya samu cewa, na mace, ya na da Fadi sosai, fiye da na namiji,an Yi hakan ne,domin a fadada kunkurun mace, ta yadda idan ta zo wajen haihuwa,ya kasance cewa kan jaririn zai iya fitowa a  cikin salama.

6).girtsi da dandatsi.

Girtsi wata hallita ce da a ke kullawa kasusuwa kawance da shi.
kamar dai  yadda aka kulla kawancen Kasusuwan Nan na kaashin baya.an sanya faifan zagayen dandatsi,a tsakanin kowa'yanne Kasusuwa guda biyu, ta yadda za ka iya lankwasa jikinka,ka Kuma jiuya shi na kusan 180% a ma'aunin zagayen saiti, wato .(Cardinal direction). da  shi ne kuma a ka kera faifan kunne, da karan hanci, da kuma makogwaro.
A jikin jinjiri ma za ka samu  cewa Rabin kasusuwansa duk girtsi ne,domin a kan haife shi ne da kusan kasusuwa dari uku,300,Amma a hankali, ya na girma, sai su rika canjawa su na harhadewa, wayo su na za ma kasusuwa,har dai su dawo dari biyu da shida,206.

DANDATSI.

Shi Kuma dandatsi wata hallitta ce mai gautsi hadi da sulbi da za ka samu a duk wata guiwa  ko mahada da  ke jikin Dan adam.ta na aiki ne da wa'yansu ruwan Romo,domin Samar da
kyakykyawan yanayi,da zai baiwa kowacce mulmullalliya da rammammiyar gaba damar  jujjuyawa,iya son ranta.

Kamallawa.
A takaice dai tsarin kasusuwa,tsari ne da ya ke ba wa jiki majingina Hadi da bashi Kariya da Kuma yarjemasa wajen gudanarda motsi da tafiya.

Domin gyara ko sharhi,sai ka sankama su ta cikin Wanan akwatin sharhin.

Domin neman Karin bayani Kuma,sai ka antaya sakon Tex ta wa'anan lambar 09035907765.

No comments:

Post a Comment