zubi da fasalin surar gangar jikin Dan Adam, ta na gudana ne a bisa wa'yansu tsare-tsare, da Allah ya shirya, masu cike da al'ajabi.domin a kowanne inji ko na'urar da za ka gani a duniyar Nan,za ka samu cewa ,da akwai Wanda ya ke kula da ita da kuma bata umarni akan kowacce gaba ta aikace-aikacen da na'urar ke yi.wato da akwai Wanda ya ke bibiya ko jagorantar aikin Wanan na'urar, Wanda shi ya ke bata umarnin,kaftawa da Kuma gintsewa,.wanda umarnin zai iya kasancewa a rubuce ne ko Kuma a aikace.
Falallar tsare-tsaren gudanarwar jikin Dan Adam.
Falallar a Nan ita ce ;
A duk tsawon rayuwar da mutum zai yi,a duniyar Nan,duk Wa'yanan tsare-tsaren gudanarwar jiki Dan Adam,kan kasance ne masu aiki tukuru, dare-da-Rana,Ba tare da direba ko jagora ba,Wanda hakan na nufin,Babu hutun Rabin lokaci ballantana Kuma na karshen mako.
A takaice dai duk Wa'yanan tarin ayyukan Allah ne ke kula da kayansa. Wanda
A cikin rahamarsa kuma ,sai ya yassare Manu su a kyauta.
Domin da a ce ikon sarrafa su a hannun wani kamfani ya ke. To da ba mamaki ya zama cewa, sai ka rinka siyawa kowanne tsarin katin gudanarwarsa,.(recharge card). a kowacce Rana. Ko Kuma a ce sai ka rinka biyan kudin lantarki a kowanne wata."eh,!!! lallai Kuwa da, akwai cakwakiya.."
tsare-tsaren, dai su ne kamar haka:
1).tsarin gamayyar sadarwa.
2).tsarin zagayar jini.
3)tsarin numfashi.
4).tsarin Nika da tace sinadaran abinci.
5).tsarin Kashi da gabobi.
6).zubi da tsarin tsokoki da motsi.
7).tsarin garkuwar jiki.
8).tsarin wanke jini da tace fitsari.
9).tsarin hayayyafa.
10).tsarin mabubugan sinadaran madarar
maganadisu.
A bisa lamuncewar UBANGIJi ,za mu dauke su dai-bayan-dai,mu Yi nazari da bayaninsu a yalwace.
ga Mai bukatar karanta wa'yanan darusan a harshen ingilishi,sai ya ziyarci dayan shafimu Mai adireshi kamar haka
a Nan na ke cewa fatan alkhariii.sai kuma mun sake jamewa adarasi na gaba,,,
No comments:
Post a Comment