Monday, December 17, 2018

(11).Tsarin gamayyar sadarwa A jikin Dan Adam.

Tsarin gamayyar sadarwa ,wani tsari ne wanda shi ne  ke mulkar jikin Dan Adam,.shi ne ke karbar bayanai  da sarrafa su ,Kuma shi ne ya ke zartar da kowanne umarni  a cikin jikin Dan adam.tsari ne da ya ke karbowa da sarrafa bayanai da ga kowanne bangare na jiki.,kamar dai a irin tsarin masarauta, 

inda a misalance a cikin tsarin mulkar jiki, kwakwalwa ita ce a matsayin sarauniyar masarautar jikin gabadaya.a misali na biyu Kuma  ,za mu  iya cewa gangar jiki, ita ce mota ,kwakwalwar kuma ,ita ce  ke da alhakin tuka motar  ,wato ita ce direba.
A takaice dai a tsarin gamayyar sadarwa , kwakwalwa ita ce ke tafiyar da komai,sai dai ta kan Yi hakan ne tare da taimakon wakilanta guda biyar, da su ke karbo Mata sakonni daban-daban daga kowanne bangare na jiki.

fata ita ce Babar masarrafar da ke karbowa kwakwalwa sakon yanayin zafi ko sanyin muhalli ko Kuma duk wani Abu da ya jibinci jiki.ita ce Kuma ta ke karbo sakon radadi ko yanayin fasalin siffar wani abu.,idan ta karbi Wanan sakon, sai  ta aika shi Kai tsaye izuwa kwakwalwa ta hanyar wa'yansu wayiyin lakkar da suka fito daga cikin kashin baya na jelar  kwakwalwar,(spinal cord).sakon yakan tunkari kwakwkwarar  ne a yanayin tafiyar siginar lantarki. Ya kan tafi ne Kuma a wani irin masiffafen gudu,ta yadda idan da a  fili ne zai Yi tafiyar , to da zai iya cin nisan  tazarar kilomita dari uku (300).a cikin sa'a daya.,da zarar sakon ya Isa ga kwakwalwar,Nan take it's kwakwalwar za ta karanta shi, ta kuma Yi nazarinsa. sai kawai ta Yanke hukunci sa'anan ta mayar da martanin sakamakon abin izuwa  ga bangaren da abin ya shafa.duk Wanan zirga-zirgar takan  faru ne cikin akalla dakika biyu.(2.second).shi ya sa ma idan ka taka garwashi,ba za ka ji zafin kai-tsaye ba,domin ai sai sakon ya je ga kwakwalwar ne,za ka Ankare.
 Misalin yadda kwakwalwa  ke karba da aika sako shi ne:a duk lokacin da wayar salularka ta fada a cikin kududufi inda idonka ba zai iya ganin kasan kududufin ba. sai  ka shiga ciki ka na lalube da kafafuwanka domin nemanta,ka na cikin tafiya sai kawai ka ji ka taka wani abu,daga nan ai fatar da ke kasan kafarka ce za ta karbi sakon, ta Kuma antaya shi izuwa sarauniya wato kwakwalwa. Ita Kuma kwakwalwar nan take za ta karanta sakon da fatar kafarka ta turo Mata.zai kuma riske ta ne a matsayin siginar lantarki ,sai ta karanta sakon ta  gano cewa eh lallai Wanan yanayin tabin,  ya na da alamar da fasalin wayar salula.to daga nan sai i ta kwakwalwar ta umarci kashin baya da cewa ya sunkuya , ta kuma sake umurtar hannu da ya dauko wayar ,idan hannu ya taba wayar,zai kara tabattarwa da kwakwalwar  cewa ; eh lallai wayar ce, da zarar hannu ya dauko wayar sai kwakwalwar ta sake umartar idanu da su maida hankali izuwa ga abinda hannu zai dauko,da zarar ido ya dauki hoton wayar da yanayinta zai cilla shi izuwa  ga kwakwalwa,a yanayin haske, ita Kuma nan take zata karanta hoton ta gane yanayin lafiyar wayar,daga nan kuma sai ka  ji ka samu natsuwa.wato idan hankalinka  a tashe ya ke, sai kwakwalwa ta umarci sauran gabai da masarrafai,da ce wa ,; kowa ya koma a bakin aikinsa irin na yau-da-kulllum.to daga nan za ka ji ,ka samu nutsuwa, mussaman idan ka samu wayar a lafiyayyen yanayi. 
wata hikimar a Nan ita ce; idan ya kasance cewa wannan abin da ka lalubo da kafarka zai iya illata jiki.to a irin wanan yanayin ba sai an yi Wanan dogon barkwancin ba,da zarar fata ta karbi  sakon,za ta Yi sauri ta cilla shi izuwa ga kwakwalwa,.wato a irin Wanan ujilar idan a ka ce sai sakon ya je  can saman Kai,za a yanke hukunci kafin a dau mataki . to da abin zai iya haifar da matsala ga lafiyarka. Amma a Maimakon haka, sai kawai jelar kwakwalwa da ke cikin kashin baya , ta Yanke hukuncin (domin ai a Nan ne sakon ya ke bi kafin ya Isa ga kwakwalwar,).sai kawai ita jelar kwakwalwar ta Yi kokarin karanta sakon ta yanke hukuncin Hadi  da mayar da martanin matakin da za a dauka,da cewa kafa ta Yi sauri ta daga,domin kaucewa Wanan hadarin. 
Wanan ne ma ya sa a wasu lokutan idan ka taka garwashi, ba za  a ba ka damar yin tunani a Kai ba, kawai sai dai ka ji ka, ka yi na 'yan chana wato tsalle. Domin 
Shi tunani , dole sai a kwakwalwa a ke yinsa.
shi kuma ido ya kan karbi sakon hoto ne ta hanyar haske ya aika shi izuwa ga kwakwalwa, ita Kuma sai ta karanta tare da nazarin hoton ta Kuma zartar da hukuncin da ya da ce ta aika shi izuwa ga bangaren da abin ya shafa.
misali shi ne: idan idon mutum ya ga maciji , to Nan take ido zai dauki hoton macijin , ya aika shi izuwa ga kwakwalwa, nan take ita Kuma kwakwalwar, za ta gane eh lallai fa ga macijinan Kuma fa ya na da hadari ga rayuwa.,sai kawai ta umarci zuciya da cewa ta harba jini da sauri ta Kuma juya akalar magudanan jinin izuwa ga tsokar Kashi.takan Yi hakan ne, ta hanyar umartar wata mabubbugar madarar maganadisu,  da ke saman kodoji,da cewa ta saki Wa'yanan sinadaran. Amfanin Wa'yanan madarar maganadisun (hormones).shi ne;  karawa mutum kuzari  fiye da ko yaushe.kuma a wanan lokacin jininka ma zai iya hawa,amma na dan wani lokaci.to da ga nan Kuma sai ka ga, ba ka ma San ta Yaya aka Yi,har ka samu ka tsira ba.to daga nan Kuma sai kwakwalwa ta gayawa Sauran sassan jiki  cewa , an tsallake rijiya da baya.,inda daga nan ne kuma kwakwalwar za ta sake  umartar daukacin masarrafan da su ka fita hayyacinsu, da cewa, kowa ya dawo a bakin aikinsa,irin na-yau-da-kullum.sai ka ji nutsuwarka ta dawo.
Hallau dai daga cikin masu aikawa kwakwalwa sakonni bayan fata da ido sai Kuma  hanci. Hanci shi ne   ya ke aika mata da sakon kamshi da na doyi.sai kuma harshe,: wanda ya ke aika sakon dandano.da Kuma kunne,da ya ke aika mata da sakon sauti.
hanyoyin karba da aika sakonin, duk iri daya ne da na fata,da ido. wato ta hanyar wayoyin lantarki na lakka ,da suka fito daga kwakwalwa.

tsarin sadarwar gamayyar Dan Adam, ya na da bangarori guda biyu.
 (A mahangar zubi).

1).jigon Tsarin gamayyar sadarwa.
(centeral nervous system).
Hallau dai shi ma ya kasu gida biyu.
 
1).bangaren farko shi ne:bangaren dunkullaliyar kwakwalwa, .(brain).da ke cikin kokon Kai. Amfanin wanna tsagin na gundarin kwakwalwa shi ne ;karba  da sarrafawa ,taskancewa ,hadi da yanke hukuci da Kuma bayar da umarni.

2). jelar kwakwalwar :,(spinal cord). Wacce ita Kuma ke a cikin kashin baya.a wasu lokutan mu hausawa mu kan Kira ta da lakka.
Amfanin jelar kwakwalwa, shi ne ;isar da duk wani hukuncin da kwakwalwar ta zartar izuwa  ga sassan jiki,na ciki da wajen Dan Adam .sakon kuma yakan tafi ne a yanayin lantarki.ita ma dai jelar a wa'yansu lokutan ta kan Dan bayar da wa'yansu umarnan.

 
Tsagi na biyu (a bangaren Zubi) .shi ne 
2). bangaren rassa. 
(peripheral nervous system).
bangaren rassa wani bangare ne na gamayyar sadarwa, Wanda ya kunshi wayoyin lakkar lantarkin da suka hada Sauran sassan jiki da jelar kwakwalwa,da Kuma wa'yanda suka hada kwakwalwa da masarrafai Kai tsaye,(kamar daga ido izuwa ga kwakwalwa da na kunne)su ma dai bangare rassa,sun kasu iZuwa gida biyu 

1).masu karbo sako daga sassan jikin,su antaya shi izuwa ga jelar kwakwalwa ko Kuma izowa ga kwakwalwar Kai tsaye,da Kuma 
2).wa'yanda  ke karbo yankkaken  umarni daga kwakwalwa izuwa ga sassan jiki.

A tsarin aiki ko amfani Kuma an raba Wanan tsarin gamayyar sadarwa,izuwa gida biyu.

1)na farko shi ne; aikin da  Dan Adam ya ke da cikakken ikon saraffawa da tunaninsa ,kamar ; magana ,tafiya, da gyada-Kai, da dai duk wani aiki na motsa gangar jiki.
2)sai Kuma bangaren ayukan  da a ka kwacewa Dan Adam ragamar saraffa su,kamar ; numfashi da bugun zuciya da aikin Nika tare da tace sinadaran abinci. Hikimar yin hakan shi ne ; kasancewar  Wa'yanan ayukan,ayuka ne na tafiyar da rayuwa.wanda hakan na nufin ,su na bukatar kulawa ta  dindindin ,wato  dare-da-rana, babu hutun Rabin  lokaci balle  na karshen mako.su kan kuma yi wanan aikin ne,  daga lokacin da aka busawa mutum rai ,har 'izuwa karshen Rayuwa. To kasancewar an yi Dan adam da mantuwa , ga kuma bacci, da gyangyadi,dan haka  sai Allah acikin hikimarsa, ya daukewa Dan adam  kula da Wanan bangaren, domin kada mantuwa ko bacci  su sankame shi a samu babar matsala.
Wata hikimar  da ke cikin Wanan tsarin kuma ita ce: ba wai an kera jikin Dan Adam da Jin zafi ko radadi ba ne Dan a azabtar da shi, 'a'a.an dai Yi hakan ne da nufin  a Rika ankarar da da shi a duk lokacin da a ka samu wata matsala.domin ai wanan radadin ne ke gayawa kwakwalwa cewa fa da akwai matsala a wani bangare na jiki.hakan Kuma , zai bada damar daukan matakin gaggaw.domin da a ce ba a yi hakan ba, to da idan wata masarrafa ko wani sashe na jiki ya samu wata matsala.to kenan da ba ma za ka ji alamar mtsalar ba ballantana ka Yi yunkurin  Daukar mataki.
Hakan na nufin,  sai dai kawai a ga ka fadi ka mutu.
Amma cikin hikimar Allah yanzu da zarar ka ji cikinka na ciyo ,ko ka ji radadi daga wani sashe na jikinka,sai kawai ka antaya a guje izuwa ga likita.domin a gano me ke faruwa,tare da daukar matakin da ya Dace wa Wanan matsalar.

ga masu bukatar karanta Wanan darasin a harshen ingilishi,sai su ziyarci dayan shafina,Mai adireshi kamar haka:
www.simplegeneralscience.blogspot.com.
 ga Mai neman Karin bayani kuma ,sai ya aika sako izuwa Wanan lamber.09035907765.domin a  share Masa ya'r tantamar da ya ke da ita.

No comments:

Post a Comment