kamar Sauran,harshe ma wakilin kwakwalwa ne,da ke karba da tantance nau'in dandano,ya tura sakon I Zuwa ga sarauniyar jikin wato kwakwalwa.ya kan yi wanan aikin ne da taimakon wa'yansu kananan hallitu da ido ba ya iya ganinsu,da su ke warwatse a jikin harshen.
Wa'yanda daga cikinsu da akwai masu tatance nau'in dandanon Zaki.su na nan ta wajen tsinin harshen.sai kuma masu tantance sakon daci, su kuma su na nan a tsakiyyar harshen.
Da Kuma masu tatance sakon gishiri, su Kuma su na Nan a gefe-gefen harshe.
A sakaye kenan hakan manuniya ce da ke nuna cewa duk wani nau'in dandano da za ka ji bayan wadanan hudun, to hadaka ce ta wa'yanan hudun.
10.kunne:
10.kunne:
kunne Shima wata babbar na'urar ce da Allah ya shiryata a gefen kokon kawunanmu, domin karba tare da daidaita sauti.wato kunnuwanmu ne ke tacewa hadi da juya amon sauti ,ta yadda kwakwalwa za ta iya karantawa ta kuma fahimce shi. A takaice dai amfanin kunne shi ne;karban yanayin amo da juya shi izuuwa sauti,.wato kunne ne ke tattaro amo ya ingiza shi tare da kintsa shi I Zuwa ga kwakwalwa,ta yadda zai karantu a hankalce.
Amfanin kunne na biyu Kuma, shi ne; yakan taimaka mana wajen kintsi da tsayuwa da Kuma daidato.
Masana kunne sun ce "kunne ya na da bangarori guda uku",bangaren farko shi ne ya ke tattaro sakon yanayin amo ko sautin magana ko kuma kida.
Saututtukan kan riske shi ne a yanayin tafiyar ruwa.(wave). da ga Nan Kuma sai ya tura Wanan karfin amon a yanayin girgiza izuwa cikin kunne .daga nan sai motsin sautin ya tunkari bangare kunnen na biyu, inda a nan ne sautin zai daki wata ganga da ke can cikin dodon kunne.ita wanan gangar ta na dauke ne da wa'yansu ruwan amo.a gaba kadan Kuma sautin zai zagaya cikin wa'yansu kasusuwa,masu kamar kwararo.inda a Nan ne za a tace Wanan sautin tare da turashi I Zuwa sashe na uku,inda a wanan sashen ne za a daidaita sautin tare da antayashi izuwa ga kwakwalwa,domin sarrafawa.
Falallar kunne;
Wata hikima da Allah ya sanya a wajen halittar kunne,ita ce; kasancewar an hallice shi a wani waje da ba zai yiwu ida ya yi datti a sanya ruwa da soso a wanke shi ba. Wanda a maimakon haka,sai Allah ya shirya masa yadda zai Rika wanke kansa.ya Kuma bashi hikimar Samar da wa'yansu ruwa masu kamar Danko,da ake malalawa a kofar kunnen,ta yadda duk wani datti ko kura da ya/ta tunkaro kofar kunnen,ba zai samu damar shiga kunnen ba,domin Wa'yanan ruwan dankon ne za su lakume dattin. idan su ka Tara dattin,sai su Dan mutsune mu,ta yadda za mu dan ji kaikayi. Jin Wanan kaikayin ke da wuya,sai kawai ka ji ba ka ma san lokacin da hannunka zai Kai kwamashe wa Wanan dattin ba.a Wasu lokutan ma yayin da ka ke aikin share Wanan dattin za ka ji,har wani dan layi ka ke yi, saboda dadin abin.a Wasu lokutan ma za ka ji kamar dai kar a gintse.
domin gujewa matsalolin kunne, sai mu nisanci wuraren da a ke amfani da manyan injuna da kuma sautin kida mai karfi sosai.
Domin karanta Wanan darasin a harshe ingilishi ,sai a garzaya izuwa dayan shafinmu,Mai adireshi kamar haka,
Ga Mai neman Karin bayani kuma,sai a turo sakon tex ta 09035907765/. Ya aika sakon ,... a junaiduumar2233@gmail.com.
Da wanan ne na ke cewa sai mun sake jamewa a darasi na gaba,,,kafin Nan Kuma fatan alkhariii,,,,,,
No comments:
Post a Comment