Friday, December 14, 2018

(14).Tsarin numfashi a jikin Dan Adam.

tsarin shakar numfashi a jikin Dan Adam,wani tsari ne na mussamman da aka shirya domin samarda iskar sinadarin oksijin (oxygen) da kwayoyin hallita ke bukata domin gudanarda rayuwarsu. Hallau dai Wanan tsarin ne ke da alhakin fitar da iskar kabon (carbon dioxide).da jiki ba ya bukata.kamar dai a mota ko a babur.inji ya kan zuko iska daga sararin duniya ne ya cakuda shi da makamashi ya tarwatsa su domin samarda kuzari. 
Iskan kan shigo ne ta  matatar iska,wato (filter). domin a tace shi.a dai-dai lokacin ne Kuma ingini ke zuko abincin motar,wato makamashinta (fetur). ya kan zuko iskar da fetur din  ne a irin  yanayin da sirinji ke zuko ruwan magani a cikin kwalbar magani..daga nan Kuma sai ya garwaya su ya Kuma matse su a cikin kusurwa fistin, (bolck engine and top cylinder) daga Nan Kuma sai fulogi ya harbo tartsatsin wuta,sai fetir da iskar su damalmale su Yi bindiga,daga Nan sai iskar bindigar ta harba pistin ya Yi baya da karfi. A sa'ilin ne shi Kuma sandar inji (crank-sharp) ta ke  juyawa sakamakon Harbin da  fistin ya Yi mata.to ta haka ne inji ke samun karsashin juyawa,sai kawai ka ga mota ta samu karsashi,da kuzarin fizgawa.hakan Kuma zai Yi ta maimaituwa har sai daya daga cikin ukun Nan ya daina Zuwa.wato ko fetur ko iskar ko Kuma wutar fulogi.to a jikin Dan Adam ma wani Abu Mai Kama da Wanan ne  ke faruwa.duk da cewa za ka ga mutum ya na ta ko-dimo Abin sa , ko ma ya na ta sharar bacci, Amma  a can  cikin jikinsa  biliyoyin kwayoyin hallita ne ke ta aikin kona sinadaran abinci da Kuma na iskar sinadarin oksijin, domin Samar  Maka da kuzari.ta yadda zai, samu ya wanzar da nutsuwarsa, a cikin yanayin salama.

Yadda abin ya ke shi ne; kwayoyin hallitar da suka taru suka Gina Dan Adam, su na bukatar muhimman abubuwa guda uku ,domin gudanar da rayuwarsu.
1).Na farko su ne ,ruwa: a kan Yi amfani da ruwa ne wajen gudanar da rayuwa.
Domin ai  ; kaso saba'in cikin dari na jikn Dan adam,duk ruwa ne,,(70%). 
2).na biyu kuma shi ne,abinci; a kan Yi  amfani da sinadaran  abinci ne wajen  Samar da kuzari ,da Kuma gina jiki,domin habbaka girman jikin.
3).na uku Kuma shi ne iskar sinadarin oksijin , ita Kuma akan Yi amfani da ita ne,wajen Kona sinadaran abinci ,domin Samar da kuzari da  karsashi.wato,(cellular-respiration and ATP. 
 A takaice dai Wa'yanan su ne sinadaran tafiyar da rayuwar dan adam. Wanda  hakan na nufin   idan a ka rasa daya daga cikin su , to rayuwar ma za ta tsaya cak!!!!.

tsarin samar da iskar sinadari ga jikin Dan Adam,yakan fara gudana ne  daga lokacin da mutum ya zuki numfashi ta hanci ko ta baki,ko kuma ta duka biyun.
kasancewar, ba duka iskar da mu ke Shaka ce sinadarin ba. Hakan na nufin, da a kwai Sauran iskokai da hayaki da Kuma kura,har ma da wa'yansu nau'in  kwayoyin cuta,da ke baje-kolinsu a sararin Wanan duniyar tamu.hakan ne ya sa, Allah a cikin hikimarsa, ya shiryawa tsarin yadda zai tace iskar ,a mataki-mataki, tun daga kofar hancin, har izuwa cikin huhu.,inda a can ne a ke  gudanarda harkallar musayar sinadaran iskokan guda biyu.
matakin farko da iskar ke shigowa,shi ne ta hanci.
hanci ne  ke tacewa da Kuma dumama   iskar da ke ratsowa ta cikinsa.ta hanyar amfani da wa'yansu kananun gasu da ke shuke a cikinsa,da Kuma Wanan 'yar majinar Mai danko-danko.shi ya sa ma ba a  so, a na aske wanan gashin na cikin hanci,da wanzamai ke yi .domin duk wata kura ko wani datti da mutum ke zukowa yayin numfashi,tun a Nan a ke tace ta.daga Nan Kuma sai iskar ta antaya can  cikin Kai, inda za ta tunkari  kofar makogwaro. Idan ta fada cikin makogwaron to ,daga Nan Kuma da akwai wa'yansu kananun magudanan majina. "majina Kuma!!!".eh majina,, a zahiri mukan dauki cewa , majina kamar kazanta ce,cewa kuma ba ta da wani amfani a garemu,sai ma takura mana da ta ke Yi.. amma kuma a gaskiyar lamari,ba mu fahimceta dai-dai ba.domin ai ita majina Jikin kan Samar da ita ne domin bada kariya ga lafiyarmu.ba wai dan ta takuremu ba.majina wani sinadari ne,mai dauri-dauri,ko Kuma danko--danko,takan kwamashe duk wani bakon-haure ko datti  har ma da  kwayar cuta da ke kokarin antayawa cikin huhu.idan ta  Tattara datin da yawa,sai ta dan mutsuneka sai ka Dan ji kaikayi.daga Nan Kai Kuma sai ka fara kokarin Yin tari ,ko kuma atishawa ,domin fito da wa'yanan bakin hauren, da majinar ta sankame ta kuma daure su waje daya.to daga Nan ne iskar ke ratsowa, ta cikin wani akwati,
Wato akwatin sauti.shi wanan akwatin sautin amfaninsa shi ne Samar da sautin magana.ya na aiki ne iri daya da na usur,wato mabusa. sai dai ya kan Yi amfani da iskar da ke fitowa daga cikin huhu ne,ba wacce ke shiga huhun ba.dan haka Wanan  iskar da mu ke magana a Kai (Mai shigowa), za ta shiga cikin Wanan akwatin ne ta wuce, cikin salama.za ta yi ta  antayawa cikin makogwaron har izuwa inda za ta rabu gida biyu.wato rassa biyun farko na huhu.idan ta Kara yin kasa kadan sai ta  sake rabuwa,har dai ta fada can kasan huhu, cikin wa'yansu kananun koyayen huhu.,inda a Nan ne iskar sinadarin za ta hadu da wancan jinin da zuciya ke aikowa, Mai dauke da sinadaran kabon-da-ozaye,wanda  zuciya ke aikowa domin ya amayar da wanan iskar sinadarin.ya Kuma karbo Wanan tattaciyar iskar  sinadarin oksijin.wacce mu ka zuko da ga sararin duniyamu.to daga nan dai da zarar iskar sinadarin ta hadu da Wanan jinin sai su rungume juna cikin shauki da kawazucin soyyaya. Daga Nan Kuma kafin ta Ankara har ta gama narkewa a cikin jinin.,shi Kuma jinin bayan ya amayar da wacan iskar da ya zo da ita da ga sassan jiki.   sai ya sankami Wanan ta oksijin din, ya lodawa wasu kananan jajayen kwayoyin jinin.(hemoglobin ).
To a takaice dai ita ma iskar kabon, a dai-dai lokacinda iskar-sinadarin oksijin ta narke a cikin jini.to ita ma  a lokacin ne ta ke daka tsalle ta fita daga cikin jinin.daga Nan Kuma,sai a antayata  waje.,,,,(sai Kuma wani jikon).,,,.shi Kuma jinin da ya karbo Wanan sakon sinadarin daga huhu; zai dawowa da zuciya Wanan sinadarin,da ya karbo.daga Nan ,,ita kuma zuciyar za ta  yanki  nata kason.Sauran Kuma , sai ta harba jinin dauke da Wanan lodin na iskar sinadarin izuwa ga Sauran sassan jiki, domin a kaiwa kowa rabonsa..
ASASAMA.
Asma wani nau'i ne na borin Jini,inda kwayoyin garkuwar jiki ke yakar junansu,ko yakar wani sinadarin marar illa da ya shigo jiki.wanda hakan ke haifarda matsewa da tushewar magudanan huhu.ta yadda numfashi zai Yi wahala ga Mai ita.
A takaice dai tsarin numfashi yakan Fara ne tun lokacin da a ka busawa mutum rai
 zai kuma Yi ta maimaituwa har na iya tsawon Rai,ko Kuma lokacin da Allah ya dakatar da shi.
hayakin sigari,ya na da matukar I'll , ga lafiyar huhu da ta zuciya. dan haka sai  mu kiyaye.
ga Mai sha'war cancare Wanan darasin a  harshen ingilishi, sai ya ziyarci dayan shafinmu.Mai adireshi kamar haka:
Ga Mai shawara kuma ko gyara ko Sharhi,sai ya antaya su a cikin Wanan akwatin.
Ga Mai neman Karin bayani,Kuma sai ya turo sako ta Wanan lambar.09035907765.

No comments:

Post a Comment