Friday, December 7, 2018

(21).Kididdigar abubuwan al'ajabi da ke tattare da halittar dan adam.


Duba da yadda wanan fanin ya ke da matukar Fadi, kasancewar kuma ba bu lokacin da za mu yi bayanin komai dalla-dalla,Wanda hakan ne ya sa na  Dan yi nuta izuwa kasan kogin ilimin hallitar ta Dan Adam domin tsakuro mana kadan daga cikin kiddiddigun abubuwan Al'ajabi guda 100, da ke tattare da hallitar Dan Adam, wa'yanda ba lallai lokaci ya ba mu damar kaiwa izuwa garesu ba.kasancewar kuma ga wa'yansu fannonin Kimiyyar  can  na daga mana hannu. Dan haka 
A,,ka,,f,,ta,,,

1.kwakwalwa ta kan yi aiki tukuru yayin da mu ke bacci fiye da lokacin da mu ke a farke.
2.Gashin da ke a fuskarmu ya kan girma da sauri fiye da na ko'ina a jikinmu.

3.  Kumbar tsakiyar yatsan kafa ce ta fi kowacce kumba saurin girma a jerin yatsunmu.

4.kumbar hannayenmu Kuma takan girma da sauri har linki biyar a kan ta kafa.

5. Karan gashin jikinmu yakan kasance a  raye ne na tsawon shekaru uku 3 zuwa 7.

6.  Ruwan kaifin(acid )da tumbinmu ke samarwa  domin aikin narka abincin da mu ka ci,ya na da kaifi da karfin da zai iya narka langa-langa (na rufin daki).wanan ne ma ya sa a ke sabunta bangon cike n tubin namu a kullum.

7.bugun zuciyar mace ya fi na namiji sauri .

8. Mace takan kyafta Ido sau biyu kafin  namiji ya kyafta sau daya.

9.tun a wajen haihuwa jariri ya fi jaririya girma.kuma hakan abin zai Dore har...

10.jikin namiji kan Kona kitse da sauri linki biyu akan na mace.

11. Gangar jikin namiji ya na dauke da Jini da yawansa ya Kai lita 6.5. yayin da ita Kuma mace ta ke dauke da Lita 5.5.

12 . Kwayar hallitta mafi girma a  cikin jikin Dan Adam shi  Kwan haihuwar hallitar mace

13.izuwa tsawon rayuwa ,bakin mutum ya kan Samar da yawun da za su iya cike 
kuddudufan wankan gida guda biyu. (Swimming pools)

14. Alokacin da aka haifi jinjiri, idanuwansa sukan zo need a yanayin shudi.domin sinadarin da ke Samar da launin Ido da launin fata,(melanin ). ya na daukar lokaci kafin ya Fara aikinsa.

15. Cikkaken namiji al'aurarsa ta kan sandare a tsakanin kowa'yanne sa'o'i biyu a yayin da ya ke bacci.dalilin faruwar hakan shi ne  kasancewar  zagayar jini da sinadaran mazantaka ne ke haifar da lamarin.

16.fasalin da zubin hanci kan taimaka wajen Samar da amon murya.

17. Harshenmu na dauke da wani nau'i na  kitse.

18.karar want Abu kan sa kwayar idanuwanmu ta Kara girma.

19.kowanne Dan Adam ya na da nashi nau'in kamshi da zanen yatsa,da Kuma zanen harshe.(wato kowa NASA daban ne.)

20.izuwa shekaru sitting 60 Dan Adam ya kan rasa  rabin kaifin dandanon harshensa.

21.idanuwanmu kan kasance a yanayin ma'aunin girma daya, tun daga ranar haihuwa har izuwa tsufa,Amma su hanci da kunnuwa, girma su ke tayi ba kakkautawa.

22.  A Wasu lokutan zafin Rana yakan raunata Muna kananun magudanan Jini.ba kakkautawa.

23.idan da za ka rinka auna tsawonka da safe da maraice  a kullum,to da za ka samu cewa,adadin tsawonka na safe ya kan dan ragu idan yamma tayi,da kimanin santi-mita daya.

24.tsokar da tafi kowacce tsoka wato  karfin cin tuwo a Jikin Dan Adam ita ce tsokar harshe.. 

25.kashin da ya fi kowanne kashi kwari a jikin dan adam, shi ne kashin haba.

26. Hannaye da kafafuwanka ne ke kunshe Rabin adadin kasusuwan da ke jikin Dan adam.

27.  Kimanin kwayoyin batiriya(bacteria) miliyan talatin da uku ne ke samun muhhali a duk tazarar inci daya na  fatarmu.sai dai ba dukansu ne ke da illa ga  lafiya ba.wato da a kwai salihan bayi daga cikin su.

28.fatar da ke jikin Dan Adam takan sabunta kanta a duk tazarar wata daya.

29.su ka ce " kwayar hallitar da ta Fara bayyana a wanan duniyar tamu ita ce wata nau'in kwayar hallita ce da Bata da cikkaken shaukin rayuwa,"wato,( Prokaryotic cell.)

30.iya yanayin sanyin da muhhalin kwanciyarka ya ke dashi iya miyagun mafarkan da za ka iya,damalmale dasu,a yayin da ka ke bacci. Wanda hakan ne ma ya sa za ka ga cewa mukan yawaita mafarkai a yanayin sanyin fiye da na zafi.

31.a cikin hallitun duniyar Nan kaff,dan adam ne kadai ke iy fitar da hawayen kawa-zuci,yayin da ya ke cikin want yanayin. (emotional tears.)

32. Idanuwan kowanne jariri  kan ga komai ne a launin baki ko fari.wato su kan ganmu ne a irin yanayin da mu ke kallon majigi shekaru ashirin da su ka gabata.wato (black and white)

33.bangaren Jiki da Jini ba ya kaiwa izuws gare shi ,shi ne malfar Ido. Ya kan samu sinadarin oksijin dinsa ne kai-tsaye daga sararin wanan duniyar tamu.

34. Lafiyayyen mutum kan iya rayuwane na tsawon kwana ashirin ba tare da ya ci Abinci ba.amma ruwa damar kwana biyu kacal su ke bayarwa. Idan a ku wuce hakan, to fa...

35. Aka ce ba zai yiwu mutum ya iya kashe kansa da kansaba ta hantar yagar Naman jikinsa da hannuns.

36. Kowanne mutum idaniyar sa daya ta fi da ya kaifin gani,sai da ba a iya tantancewa kai-tsaye.

37. Allah yakan sabunta hallitar Kasusuwan mu ne a duk bayan shekaru goma.

38. Tafin kafarmu ya na da ramukan fitar da gumi,ko mu ce ya na da masuburbudar gumi har guda,500,000.

39.gudun sakon lantarkin da kwakwalwa ke aikawa ko karba,a yanayin tafiyarsa,ya kan iya  Cin tazarar mil 200    cikin sa'a daya. 

40. Kwayoyin hallittarmu miliyan dari uku ne 300.000.000.kan Riga mu gidan gaskiya a kowanne minti daya.

41. Mutane masu farin launin gashi sun fi  masu baki yawan gashin.

42. Kwayoyin hallitu biliyan dari uku ne 300,000,000,000, jikinmu ke kyankyasa a kowacce Rana.

43.jikin Dan Adam na dauke da sinadaran karfen da zai iya Samar da kusa mai tsawon inci uku.

44.  Jini Mai dauke da nau'in o ,shi ne ya fi kowanne nau'i saukin samu.a cikin al'umar duniyar Nan.

45. Hawaye da majina,su na dauke da wani nau'in na sinadaran da ke yakar kwayoyin cuta.

45. A falsafance muta ne masu rinjayen hanun dama sukan Dan fi masu rinjayen hanun hagu tsawon Rai,na  kusan shekaru Tara,( right-handed people anda lefties.)

46.kunnuwanmu kan Samar da sinadarin dankon kunn idan Muna a firgece,fiye da yanayin nitse.

47.zafin da jikinmu ke samarwa a cike n Rabin sa'a,idan aka alkinta shi ,zai iya tafasa Rabin galan na ruwa .

48. Mu kan ga Lebenmu a yanayin Kore ne kasancewar yawaitar kananan magudanan jinin da ke wajen.

49. Idan za a you la'akari da nauyi,kashinmu ya fi karfe kwari.

50.yayin da ka ke kokarin tako daya da kafarka,kakan nemi tallafi ne da ga wajen tsokoiki dai dai har guda dari biyu. 

51. A  daukacin sassan halittar Dan Adam ,sashe daya ne wanda idan tsautsayi ya gifts har ya samu gibi , baya iya cike gurbin kansa ,wanan sashen kuwa shi ne  hakori.

52.mu kan yi amfani da guntayen tsokoki 43 ne yayin da mu ke kokarin juya yanayin fuskarmu izuwa fuskar shanu, (turbuke).Amma Kuma mu kan yi amfani da stokoki 17 ne kacal  a yayin da mu ke murmushi. Hakan kenan ya na nufin farashin murmushi ba ya da tsada,Wanda hakan Kuma manuniya ce da ke nuna cewa ...


53. Kaso Tara daga cikin goma na rashin lafiyoyin da ke addabar mu,su na da alaka da rashin samun hutun kwakwalwa,wato (stress)

54. Su ka ce "akan samu yawaitar hatsarin bugawar zuciya a ranar litinin,fiye da kowacce rana".(heart attack).domin kaso ashirin cikin dari 20% na bugawar zuciyar da a ke samu a fadin duniya GABADAYA, wai a ranar litinin ce.ko me ya sa haka,, ohoo,,,.

55.a duk mutanen duniyar nan ,tagwayen jarirai  ne kadai ne ke da yanayin kamshin jiki iri daya.

56.hancinmu kan iya tantance nau'o'in kamshi dai dai har   50,000.

57.yanayin zubi da fasalin hancunanmu, nau'i goma-Sha-hudu ne .((wato akwai zubin bunburutu,da zubin botoromi ,,,kamar na ....))

58. Daya bisa ukun mutanen da ke rayuwa a duniyar yau,idanuwansu kan iya tatance nau'o'in launuka ashirin ne kacal 20.

59. Kowannenmu kan rayu a matsayin kwayar hallita daya na tsawon sa'a daya.wato a lokacin da a ka yi kyankyasa a cikin mahaifa.

60.daya daga cikin jarirai dubu biyu,2000  da a ke haifa,kan zo da haurensa kwaya daya a cikin bakinsa.

61. A kowacce shekara Jikinmu yakan amayar da kwayoyin hallita, da nauyinsu ya Kai kilo giram  4kg .

62. Hakorin jinjiri kan Fara tsirowa da girma ne tun wattani shida kafin haihuwa.

63. Lafiyyaye Kuma natststse kamallalen mutum, kan bayar da  iska na akalla sau 12 a kowacce rana.

64. Kaso 75% cikin dari na sharar da jikinmu ke fitarwa , duk  ruwa ne.

65. Mafitsarar Lafiyayyen mutum kan iya kumbura domin aje fitsari,har kusan girman kwallon-kafa.wato ta-mola.

66. Kwayoyin cuta kan fito daga cikin bakinmu, yayin da mu ka yi tari a rin matsiyacin gudun da kan iya cin tazarar mil 60 a cikin sa'a daya.

67.  Wato gashin da ke tsirowa a jikin Dan Adam , ya na da karfi da izzar da ba Abinda ba zai iya hudawa ba,a hanyarsa ta fitowa duniya, wato domin shi ma a ci duniyar da shi.

68. Hadakar  Kananun hanji su ne massarrafa mafi girma a cikin massarafan kayan cikin  Dan Adam.

69. Iskar da ke fitowa  daga bakinmu yayin da mu ke atishawa,ta kan fito ne irin gudu  da karfin cin tazarar mil dari 100,a cikin sa'a daya.

70.  Idan shekarunka su ka ja, Sai bayan  ka rasa rabin gashin jikinka ne da kafin mutane su  ankare.

71. Jikin Dan Adam na dauke da magudanan Jini,wa'yanda idan aka Mike su ,za su iya Kai wa nisan mil   60,000.

72. Idan  A ka warware farfajiyar-huhun Dan adam ,fadinsaa zai iya kaiwa fadin farantin kwallor hannu.(table-tenist)

73. Hanta na samar da alfanai a Jiki ,da yawansu ya Kai 500

74.  Massafar da ke Samar da ruwan madarar maganadisun kuzari,kan cigaba da girma ne na tsawon rayuwa. (adrenal gland)

75. Tsagin huhu na dama ya fi na hagu girma.

76. Kwakwalwar Dan Adam kan iya taskance gabadayan bayanan da ke makare a yanar ankabuti  ,wato  (yanar gizo.)

77. Ita kwakwalwa da kanta ba ta Ji ko fahimtar radadi.

78.ba gumin da mu ke yi ne ke da wari ba,sai dai sinadaran da gumin ke dauke da su ne ke warin.

79.digon Jini kwaya daya ,na dauke da kwayoyin dankon Jini, kwaya dai-dai har 250,000 (platelets.)

80. Bacin saman harshe , da akwai Wa'yansu bangarorin Jiki ,masu dauke da tsiron hakaito dandano ,da ke hakaito santin dandano.

81.  Harshenmu na dauke da tsiron hakaito dandano har guda 2000.(taste buds).

82. Kananun yara kan girma da sauri a cikin yanayin damuna.

83. Daidaituwar tsayuwar ka, woto idan ka na tsaye ko ka na zaune, kowanne mukami a acikin su ,na da alhaki wajen sarraffa karfin kwakwalwarka.

84.kwakwalwar fan aram kan iya jiyo masa sautin bugi,idan ya fada a cikin wani barkattacen yanayi da a ke kira,
 ( 'exploding head syndrome'. )

85.namiji ma ya na da wata 'yar karamar mahaifa Wacce har yanzu masana ba su gano amfanita ba,ta na kwance ne a saman mararsa,ta na ta hutuwa abinta. 

86.zubi da fasalin kwakwalwa,kan canza a lokutan balaga.

87.daya bisa ukun Kasusuwan da ke jikin Dan Adam duk su na a kafafuwansa.

88.madarar maganadisun zaburarda kuzari ,wato na adrenaline,kan bawa mutum kuzarin wuccin-gadi na karfin mutum 6.

88. A duk lokacin da a ka bar  tabon cizon hakorin mutum a jikin wani , ba tare da daukar mataki ba,wanan tambon kan harbu da kwayoyin cuta ne,Nan take.

89. A daukacin halittar Jikin  Dan Adam,da akwai kwayoyin halittar batiriya atattare da shi,da nauyin su ya Kai kilo giram,k2.

90.jikin Dan adam na dauke da jinin da zai iya kosar da sauraye,1,200,000.

91. Idanuwanmu kan ga abubuwa ne a yanayin kasa-sama, wato (upside-down),amma kwakwalwar mu ce kan juya abin ta  yadda za mu gan shi daidai.

92. A cikin wakilan kwakwalwa da ke karba Mata sako,kunnuwa ne ke Fara aikinsu a makare,a yayin da mu ka farka daga bacci.

93.kwakwalwarmu kan Samar da sinadaran kuzarin lantarkin ,da za su iya tayar da kwan lantarki daya.

94. A iya tsayon dai-daittaciyar rayuwar dan Adam ,zuciyar sa kan harba ne sau biliyan dari uku,.300.070.000,0211.

95.kwakwalwar Dan Adam na dauke da kwayoyin halittar lakka da yawansu ya Kai biliyan 
86,000,000,000,.

96. Dunkullalun zaruruwan da ke cikin Karan sifa da dabi'ar Dan Adam,(DNA), idan a ka warware su, tsawonsu zai  iya kaiwa tazarar mil miliyan goma.(10,000,000).

97. izuwa lokacin da Dan Adam kan Kai shekaru 70,a na sa ran cewa ya lakume abincin da yawansa ya Kai tan 350,000

98. Idan a ka warware kananun hanji tsawon su zai iya kaiwa kafa 23.

99. A falsafance idan a ka auna,za a samu cewa kafarka ta hagu ta Dan fi ta dama tsawo,Amma hakan a sakaye ne.

100. A gabadayan daukacin gundarin hallitar Dan Adam , na kunshe ne da kwayoyin hallita (human cell) ,da yawansu ya Kai tiriliyan talatin da biyar.(35,000,000,000,000,).

Domin cancare wanan darasin a harshen turanci,sai a antaya kai-tsaye izuwa dayan shafin,Mai adireshi kamar haka; 
Domin neman Karin bayani ko sharhi,sai a cike akwatin sharhi da ke kasan shafi,ko Kuma a aika da sakon tex  izuwa 09035907765.

No comments:

Post a Comment