Sunday, December 9, 2018

(19).Tsarin hayayyafa.

Tsarin hayayyafa wani tsari ne na mussaman da Allah ya shirya domin tabbatar da cigaba da wanzar da hallitar dan adam a doron wanan duniyar tamu.wanan tsarin shi ne tsarin da ya fi kusan kowanne tsari muhuimmanci  a jikin dan adam. Domin da a ce zai je yajin aiki daga yau,to Babu mamaki idan ka ziyarci duniyar a shekaru dari da hamsin (150)masu Zuwa, ba za ka samu wata hallita Mai Kama da dan Adam ko daya ba.,sai dai kawai ka samu dabbobin dawa sun yo hijira sun dawo cikin gari, su na ta baje kolinsu a saman titunan da mu ke zirga-zirga a Kai.wato su na ta   kodimo abinsu.tinda dai dama juyin mulki ne mu ka Yi musu. Sai su sheke ayarsu; ,babu karar ababen hawa, Babu hayaki Kuma babu sa Ido ta bangaren  yara.

MU DAWO KAN MAUDU'IN

kasancewar Allah ya tsara hallitun wanan duniyar tamu a turbar cewa, Wanan ya haifi wanan-wancan ya haifi wancan, ta haka dai har lokacinda zai dakatar da duniyar baki daya,inda za a tattaro kowa da kowa a waje daya,domin a gudanarda binciken,kwa-kwafff.
Wato a bayyane ya ke cewa
Allah ya na kirkiran Dan Adam ne ta hanyar amfani da bangarorin Wasu y'a'yan Dan Adam guda biyu,wato ta hanyar amfani da jinsina guda biyu ,wato daga  jinsin namiji da kuma jinsin mace.
Kamar dai a akwatin buga bulo na hannu.inda za ka ga cewa idan za a kera bulon,to dole a na bukatar bangarori guda biyun.hakan na nufin , daya ba ya da amfani idan babu daya.to haka shi ma a tsarin hayyayafa,; kenan a misalance Allah ya raba injunan haihuwa gida biyu,;ya baiwa jinsin mace Wanan akwatin buga bulon,shi Kuma jinsin namiji sai a ka ba shi wanan shantalin na ciki.a misalance dai hankalin Mai karatu zai hakaito masa muhimmancin kowanne bangaren jinsi wajen Samar da kamallalliyar hallitar Dan adam.
Amma domin saukaka fahimta, za mu dauki kowanne bangare daga cikinsu,  mu yi nazari da bayanin rawar da ya ke takawa.

TSARIN HAYYAYAFA A BANGAREN JINSIN NAMIJI.

A duk lokacin da issashen namiji ya Tara da issashiyar mace,kwayoyin hallita hade da wata madara kan fito daga 'ya'yan marainansa ya biyo ta cikin fuloginsa ya antaya cikin duniyar mace,inda a Nan ne zai hadu da Kwan hallitar mace,da zarar sun hadu kuma ,sai shigar ciki ya tabbata wanda,daga Nan Kuma sai cikin ya Fara girma,har dai izuwa lokacinda za a haife shi.
A kan kirkiri 'ya'yan haihuwar hallitar namji ne a  cikin 'ya'yan-marainansa, (spermatozoa).a kan Kuma kirkiresu ne a wa'yansu matakai guda biyu,;matakin farko shi ne aikin tallitawa,aikin tallitawa kuma ya na kasantuwa ne a wani bangare can kasan wasu zagayayyun kusurwai,da ke can kasan marainan.a kan kuma kirkire su ne a yanayin hadakar tawaga.massarafar 'ya'yan maraina su na da fikira da karsashin kirkirar 'ya'yan kwayar haihuwar hallitar namiji, da yawansu ya Kai akalla miliyan dari biyar(500,000000) a kowace Rana!!!. idan a ka kirkiresu,sai su shiga  matakin raino,Wanda shi ne mataki na biyu. Daga  Nan ne kuma za a Fara rainon kwayoyin hallitar har  su girma su Fara motsi da tafiya,a irin yanayin tafiyar kifi ko 'ya'yan kwadi.su kan Yi tafiyar ne da taimakon wata wutsiya,za ka dai gan su  kamar   'ya'yan kwadi,sai dai ba za su ganu da ido ba.dole sai da taimakon wata na'urar hangen kananun hallitu,wato(microscope).to a Wanan matakin ne  za su zauna su fara jiran Kira.
Akan  yi aikin tallitawa da rainon  'ya'yan kwayar hallitar namiji ne a cikin 'ya'yan maraina ne , kasancewar kananun kwayoyin hallitar namijin,ba  sa iya jure zafin da ke cikin cikimu.shi ya sa a ka zo daga waje,a ka ginamusu nasu muhallin.
idan ma su na bukatar dumi-dumi,sai jakar da  su ke cikinta ta tamure, ta janyo su kusa da cikin,ta  yadda za su dan Rabi cikin, domin ya dan dumama su.

SADUWA.

Ita kuma Saduwa ko tarawa, ta na farawa ne,daga lokacin da namiji ya darsawa kwakwalwarsa,tinanin kwadayin tarawa da mace.idan hakan ya faru,sai kawai kwakwalwa ta hargitsa jiki.wanda a wanan lokacin , a mafi yawa , hankali ya kan Dan Yi rauni.ko Kuma ma a neme hankalin, a rasa"ko a ina ya ke tafiya?",oho.da ga Nan  ne kuma kwakwalwa   ta ke umarni da a  juya akalar jini izuwa ga fulogi.dama shi fulogin namiji kamar soso ya ke,jini na zuwa,sai ya cika shi ta yadda zai Yi karfi.
Sai dai karfin ya danganta da karfin sha'awa.to daga nan bayan alkalamin ya cika da Jini,sai kawai a fara saduwa a tsakanin jinsuna biyun.a na haka ne za a Kai wani mataki,Wanda da hausa ba ya da suna.("me ya sa" domin ai shi yaren hausa,yare ne na masu  kawaici da Kuma tsabtace harshe.) Amma a turanci a na Kiran hakan da (climax).to a na cikin hakanne, dai  za a Kira wa'yancan 'ya'yan kwayoyin hallitar da ke cikin 'ya'yan-marainan . Wanda a  Nan take za su biyo ta wani kwararo,Wanda ya hada 'ya'yan maraina da turken fulogi ,inda a Nan ne za su hadu da wata Madara ,wacce ke taimaka musu ,domin ita ce ta ke zame musu abinci ta kan kuma taimaka musu wajen tafiyar tunkarar Kwan hallitar mace.to da zarar 'ya'yan kwayoyin  sun hadu da wanan mahadar,sai Wanan madarar  da mu ke Kira da maniyi, ta  lullube su,ta shigo da su cikin kwararon fulogi, a gudane,inda a karshe dai za su tsinci kansu cikin wata duniyar daban.shi Kuma namiji da ga lokacin,zai ji ya samu gamsuwa.su Kuma 'ya'yan maniyin,wa'yanda yawansu ya Kai miliyan dari uku,(300,000,000).za su Fara wasan tsere izuwa haduwa da Kwan hallitar mace.idan kuma a ka yi gam-da-katar cewa,Kwan hallitar mace ya na kan hanyarsa ta Zuwa ko Kuma ya ma Riga da ya zo,wato ya na nan  ya na jiran su, a sansanin cin amarci.to sai dai kuma duk a cikin wa'yanan miliyoyin kawayar hallitar namiji, daga cikinsu kwaya daya ne kawai zai samu damar damalmalewa da Kwan hallitar macen.daga nan  sai a yi kyankyasa  da shi, sauran kuma duk na annabawa za su dauka,wato(hakuri).ita Kuma Wanan  madarar da mu ke cewa maniyi,mahaifar mace ce za ta zuke ta,domin ta na da amfani ga lafiyar mace. A takaice dai ,da zarar an kammala Wanan kawancen,sai juna biyu,ya tabbata.to da ga nan, shi namiji ya kammalla bada tasa gudummuwar,.Sauran Kuma, duk mace ce za ta iyar.

Namuji ko mace?. 

Kamar dai yadda mu ke gani cewa ; a Wasu lokutan a kan haifi namiji,a Wasu lokutan Kuma sai ka ga an faifi mace.
Kenan ya abin ya ke ne???.
Yadda abin ya ke shi ne;ita mace akodayaushe Kwan hallitarta duk iri daya ne.ma'ana koyayen halittar da mace ke samarwa , su na  dauke ne da alamar, M.M.wato Mata zalla.su Kuma kwayoyin hallitar namuji ,an rabasu gida biyu.kaso daya da alamar,M wato mace.kaso daya Kuma da alamar,N.wato alamr  namuji.
To a cikin wa'yanan miliyoyin hallitar na namiji da ke shigowa jikin  mace yayin jima'i,su ne Allah ya dorawa alhakin Samar da jinsi.wato idan kwayar halittar namuji Mai alamar M.ne ya hadu da na mace Mai alamar M ,kenan Ya zama  M guda biyu,wato M.M. to hakan na nufin za a haifi mace kenan.idan Kuma Mai alamar; N ne ya hadu da na mace Mai alamar.M kenan hadakar ta zama;M.N.wanda hakan na nufin za a samu jinsin namiji.,,
bayanin tagwaye Kuma,ya na Nan tafeee.

TSARIN HAYYAYAFA A BANGAREN JINSIN MACE.

Tsarin hayyayafa a bangaren jinsin mace ,ya Dan banbanta, ta fuskar tsari da kuma zubi ,idan aka danganta ta da tsarin namiji.duk da cewa dai duka biyun su kan Fara aiki ne yayin balaga.
 banbabcin da ke tsakaninsu shi ne; ita mace akan haifeta ne da daukacin adadin koyayen da za ta kyankyasa a it's tsawon rayuwarta.hakan kenan na nufin su na da adadi. idan su ka kare,to shi kenan ba maganar haihuwa ko kuma wai wata al'ada.
a kiyasance  akan haifi kowacce mace ne da kusan koyaye dari hudu Zuwa dari biyar.400-500).Kuma akan Fara raino da kyankyasar su  ne a lokacin da ta kai mizani.mazaunin koyayen na Nan  a bangarori biyu na mahaifa a cikin wani kwanso.da zarar mace ta Kai mizani, Wanan kwason da koyayen ke cikinsa,zai Fara raino da sakin kwai daya a kowanne wata. Kwan ya kan biyo ta wani kwararo har ya shigo ta farfajiyar mahaifa, a yanayin tafiyar tamaula,wato (ball).dama Kuma kafin ya iso a farfajiyar mahaifar ,tuni an Riga da an yi masa lafiyayyar shimfida.  a Nan ne Kuma  kwan zai yi ta zaman jiran abokin hadinsa,wato kwayar haihuwar hallitar namiji.a wasu lokutan ma tun a hanya su ke haduwa.idan su ka hadu a hanyar,sai su gangaro izuwa Wanan shimidar,domin cin amarcinsu.idan kuma ba su samu haduwa ba , Wanan Kwan zai jira na 'yan wasu kwanaki,idan bai ga abokin hadin nasa ba, sai kawai ya yi fushi ya harzuka ,idan matakin fushin nasa ya Kai wani munzali ,sai kawai ya rudduduge tare da Wanan shimfidar,daga Nan Kuma sai su antayo waje a matsayin jinin al'ada.hakan yakan faru ne akalla sau daya a kowanne wata.
kamar yadda Mai karatu zai gani a hoton sama,cewa mahaifa ta na da kwansunan koyaye a bagarorinta biyu.su kan saki koyaye biyu ne a cikin wata biyu.
Wato idan  kwanson da ke bangaren dama ya saki kwai daya a wanan watan,sai shi Kuma na hagun ya saki daya a  watan gobe.a kiyasance kuma su kan kammalla sakin Wa'yanan koyayen ne a dai-dai lokacinda mace ke kaiwa shekaru arba'in zuwa hamsin.(40-50).daga Nan Kuma Babu al'ada ballantana Kuma haihuwa.a dayan  bangare  Kuma ;idan ya kasance wanan Kwan ya hadu da kwayar hallitar namiji a wanan tafiyar da  ya ke yi ,(daga kwanson kwai Zuwa mahaifa).to a Nan ne a ke samun shigar cik,daga Nan Kuma sai a fara laulayi  da amai da tashin zuciya.hakan na faruwa ne sanadiyar sakin wa'yansu sinadaran-madarar-maganadisu(hormones) da kwanson kwai ke yi,a bisa umarnin turken kwakwalwa.
To A haka dai Wanan gamayyar Kwan Mai dauke da kwayar hallitar namiji da na mace,zai Fara rabuwa biyu,ya na hadewa,zai yi ta rabuwa,(Amma fa a dunkule waje daya).a haka dai Allah zai ci gaba da ikon sa,har dai izuwa lokacin da za  busa Masa Rai ya Fara motsi,har dai a zo haihuwa.inda kafin Wanan lokacin tuni an Fara Samar Masa da hanyar fita,wato ta inda ya shigo.
a lokacin da jaririn ke cikin ciki,yakan samu sinadarin abinci da na iskar oksijin ne a mahadar cibiyarsa ta mahaifa,wato a cikin na mahaifiyar ne a ke yaga masa.to da zarar lokacin haihuwar ya yi .sai a umarci massarafar sinadaran nono(mamary-gland) da ta Fara Samar da abincin jariri.a kan kuma kera abincin ne a mataki-mataki ,izuuwa har  kammalla shayarwar.

KAMANNI.
Kamar yadda ya ke a bayyane cewa, za ka ga  jariri ko jaririya kan yi matukar Kama da mahaifi ko mahaifiya ,ko ma  kakkaninsa,na gefen uwa  ko  na gefen uba.hakan na faruwa ne kasancewar an hada kwayoyin halitta guda biyu ne domin a fitar da wata hallitar daya.
Yadda abin ya ke shi ne , akan duba cikin kundin kwayar hallitar kowwane bangare .(DNA)  sai a yanki karan sifar kowanne bangare ,domin a Yi sabuwar hallitar Mai kammani daban.  kenan a kowanne tsagi za a yankin Rabin karan-sifar- halitta(chromosomes) guda ashirin da uku(23).a hada su waje daya domin Gina wata  kamallalliyar hallitar.idan a ka hada na uwa da na uban,Wanda su ma sun gado su ne daga nasu iyayen.to idan a ka hada Karan-sifar,na jinsunan biyu, sai a tallita wata kamallalliyar hallitar Dan adam,Mai dauke da karan-sifar hallita arba'in da shida.(46). .to sai dai ba komai a ke rabawa dai dai ba.me yiwuwa fuskar da launin fata da fasalin jiki ya zama na uwar,.yanayin hallayar da dabi'u Kuma, zai iya zama na uban,ko ma duk a zube su gefe,a je can a dauko hoton wani kakansa, da ya rayu shekaru dari a baya ,a sawwarra shi,wato(photocopy).domin fitar da wani irinsa.wanan ne ma  ke sa a Wasu lokutan idan a ka haifi wani jararin,sai ka ga a gabadayan danginsa da ke Raye,Babu Mai  irin fasalinsa.sai ka gan shi da wata fuskar Wacce a tarihance an Dade da daina yayinta. 

A takaice dai Allah ne ya ke jujjuya al'amarin gadon dabi'u da siffofi,ta yadda ya ke so.

TAGWAYE.
Kamar yadda mu ke gani.a wasu lokutan za ka ga mace ta haifo 'ya'ya biyu ko sama da haka.a wasu lokutan tagwayen kan zo a tawagar mace da namiji  ,a wasu lokutan Kuma,sai ka ga Mata biyu masu Kama da juna ko Kuma  maza biyu masu Kama daya.hakan na faruwa ne a bisa wasu sauye-sauye da a ke samu a yayin shigar ciki da Kuma lokacin rainonsa.
Yada al'amarin ya ke shi ne;a akan samu tagwayen jinsi daban-daban ne, masu kamanni mabanbanta ko Kuma tagwayen jinsi daya amma mabanbanta;a  duk lokacin da wa'yanan  kwansayen Kwan mace su ka sako koyaye a tare a cikin wata daya.a ka Kuma Yi nasarar cewa kowannensu ya samu  damar damalmalewa da kwayar hallitar namji.
A bangaren daya Kuma ,
A kan samu tagwayen masu kamanni daya ne; idan Wanan hadakar kwan na kwayar hallitar mace da ta namijin ya rabu gida biyu,kuma kowanne ya Kama gabansa.domin idan Mai karatu bai manta ba,mun yi bayanin  cewa akan samu shigar ciki ne,idan Kwan hallitar mace ya hadu da na namiji,a kan hanya, ko Kuma a kan hanyar zuwa shimfidar da a ka yi musu domin cin amarci.mu ka Kuma yi bayanin cewa Wanan hadakar koyayen guda biyu da ke cure waje daya, kan Fara rabewa ya na rubanya kansa,tun daga biyu , hudu, shida , har dai Zuwa.... amma fa duk Wanan rabe-raben da ya ke yi, ya na dunkule ne a waje daya.to a wasu lokutan idan Allah ya tashi nuna ikonsa, sai  ya raba kwan gida biyu ko uku ko ma huda,daga Nan Kuma sai kowanne tsagin ya kama gabansa.wato iya adadin rabuwar Kwan iya adadin 'ya'yan da za a haifa.kuma a irin Wanan tagwaicin ne a ke samun y'an biyu masu Kama da komai iri daya,.sai dai Banda zanen yatsa.shi Wanan kowa NASA daban ya ke.

Ya na da matukar muhimmanci cewa mu Dan Yi tsokaci a kan Abinda ya shafi

 TSARIN IYALI DA TAZARAR HAIHUWA
Sai dai kasancewar na ga lokaci na harara ta,ga Kuma wa'yansu darusan can da ke gabamu, su na daga min hannu,Wanda hakan ne zai tilastamana dasa aya a Nan,,,sai dai a wani jikon.,,

ga Mai bukatar cancare Wanan darasin a harshen su musta kyam-kyam,sai ya ziyarci dayan shafinmu,Mai adireshi kamar haka,
www.simplegeneralscience.blogspot.com.
Domin  neman Karin bayani ,ko gyara, ko shawara,sai a antayo  sako ta Wanan lambar.09035907765/ ko Kuma ka sankama albarkacin bakinka ta Wanan akwatin sharhin..
A Nan na ke ce da ku,, sai mun sake jamewa a darasi na gaba..

No comments:

Post a Comment