Wednesday, December 19, 2018

(9).Sassan jikin Dan Adam da amfaninsu(5).

11)Mahaifa:
mahaifa wata  hallita ce da Allah ya kirkira a jikin mace.mazauninta na nan kasa da cibiya.ta na da kamanni irin na hatimin likitanci.akan kuma haifo ko wacce mace da ita, tare da adadin koyayen da za ta kyankyasa a iya tsawon rayuwarta .amfaninta shi ne kyankyasa da rainon jinjiri, tun daga matakin Dan tayin har I Zuwa haihuwa.ita ce kuma ke Samar da wa'yasu sinadarai na macantaka, wato (estrogen).sai dai ta kan Fara Wanan aikin ne bayan mace ta kai shekaru goma Sha uku Zuwa Sha biyar da haihuwa.
12)'ya'yan maraina.:

ya'yan maraina wa'yansu kananan hallitu ne da allah ya hallita a jikin Dan adam , domin kyankyasa tare da rainon 'ya'yan halittar maniyin namiji.mazaunin su na Nan kasa da ciki.dalilin kuma da ya sa ba a yi su cikin ciki ba , shi ne: su suke rainon 'ya'yan hallitar maniyi (spermatozoa). ,wa'yanda a yanayinsu  na rauni ,ba za su iya jure zafin da ke cikin ciki ba,shi ya sa a ka dawo da ga waje a ka Yi musu karamin aljuhu,a ka sanya su a ciki.wata hikima da a ka Yi a wajen shine: a duk sanda mutum ya ke cikin yanayin sanyi, za ka ga wanan aljihun ya tamure. ya janyo 'ya'yan maraina sun makalkalewa ciki, domin ya Dan dumama su, haka-zalika Kuma a duk lokacin da ka ke cikin yanayin zafi sai ka ga sun warware sun nesanta kansu daga bangaren ciki.domin kada zafin ya illata su.
  amfanin 'ya'yan-maraina, shi ne; su ne  ke kerawa tare da renon 'ya'yan kwayar hallittar maniyi,.su na kuma da kuzarin kera kwayar halittar namiji, dai-dai har guda miliyan dari uku, a kowace rana.Kuma su ne ke kirkiran wasu ruwan sinadarai na mazantaka wato (protoestereon).su ma dai sukan Fara Wanan aikin ne bayan shekaru goma Sha biyar Zuwa Sha bakwai,da haihuwa.
13)Jini:

jini wani nau'i ne na kwayoyin hallita, da suka hadu waje daya domin gudanarda aikin rarraba albarkatun abinci da  na sinadarinan  iskar da mu ke shaka.wato (oxygen)  .a takaice dai jini Dan dako ne.
muhiman kananun  kwayoyin hallitu uku ne  ke cikin jini.na farko shi ne; kwayar -2). jajayen-jini: (red blood cells),aikinsa shi ne, rarraba iskar sinadari, tare da kwamaso iskar kabon,(carbon dioxide). daga cikin kwayoyin hallita, ya yi waje da ita,shine Kuma ya ke rarraba sinadaran abinci, ya baiwa ko wanne bangaren jiki hakinsa.sai dai Shima ya kan Ware nasa rabon tun a hanya.
Sai nau'in hallitar jini na biyu,wanda  shi ne 
2).fararen kwayoyin hallita: (with blood cells) . aikinsu a cikin jini shi ne ; bayarda kariya tare da lakume duk wata kwayar cuta da ke kokarin antayowa izuwa cikin jikin Dan adam.na uku Kuma shi ne: 
3).kwayoyin dankon jini.(platelets).kwayoyin dankon jini , amfaninsu shi ne kawo dauki yayin da mutum ya ji rauni,na yanka ko Kuma yagewa.  su kan Yi kawance su ,zagaye wajen, domin tabattar da cewa jinin mutum bai tsiyaye gabadaya ba.shi ya sa  za ka ga cewa idan ka samu rauni a kafa ne ko hannu,jini zai tsiyayo ne na Dan wani lokaci,daga Nan Kuma sai ka ga wurin ya Fara daskarewa.

Tunatarwa.
duk wa'yanan bayanan da mu ka Yi na sassan jikin Dan Adam da amfaninsu,mun Yi su ne a gajarce, domin saukaka fahimta.amma a darasinmu da ke tafe,za mu fadada bayani.za Kuma mu Yi su ne a karkashin wanan babin,wato 
(Tsare-tsaren gudanarwar jikin Dan Adam) 

wato (human body systems) 


ga Mai bukatar fadada nazarin wa'yanan darussan a harshe turanci,sai ya ziyarci dayan shafina ta wanan adireshin.
www.simplelifescience.blogspot.com

No comments:

Post a Comment