Saturday, December 15, 2018

(13)Tsarin narka da tace abinci a jikin Dan Adam.

Tsarin narkawa da tace abinci,wani tsari ne da Allah ya shirya,a cikin jikin Dan Adam, Wanda aikinsa shi ne, narkewa da tacewa hadi da zuke albarkatun da ke abincin da mu ke ci,ta yadda zai amfani  kananun kwayoyin hallitun jikinmu.(cell). Kamar yadda mu ka sani cewa duk wani  kafcen motsi ko juiwi da zai faru a duniyar Nan ,ya na bukatar kuzari,shi kuma kuzari ba ya samuwa sai da makamashi , shi Kuma makamashi asalinsa  daga Rana ya  ke ,ita Kuma Ranar daga cikin taskokin   UBANGIJI  ta ke.
A takaice dai I'mma-kai-tsaye-I'mma-ba-kai-tsaye ba, kowanne nau'in makamashi da ke cikin sararin duniyar Nan daga Rana ya ke.ko Kuma a saukakkaken harshe mu ce daga  Allah ya ke.fakatt..
A takaice dai Tsarin Nika da tace Abinci , ,wani tsari  ne da ke darkake lomomin abincin da mu ka ci, da kuma nika shi,tare da tsotsaye sinadaran da ke cikinsa,sauran dusar Kuma sai ya antaya ta waje.wato ta fita ta dubura a matsayin Kashi.
Jiki kan yi Wanan aikin ne, tare da taimakon wa'yansu sinadaran kaifi wato acid,masu kaifin narke ko wanne irin abinci,ko da Kuwa kuli-kuli ne, ko Kuma jijiyar da hakora su ka kasa darkakewa,.to ballantana kuma wai wani biredi .,,,wai (kwace-goriba-a-hanun-kuturu).
 tsarin sarrafa abinci a cikin jiki. kan  tace ruwa da Kuma rukunan sinadaran  abinci nau'o'i hudu.
   domin  karawa nazarin namu armashi tare da saukaka fahimta.bara mu dauke su daya-bayan-daya,mu yi bayanin su, daki-daki.

,su ne kamar haka:

1)..sinadarin rukunin Gina jiki.(protein).:  

Wani sinadari ne da Allah ya tanadar Mana ya kuma ajjiyemana shi a cikin abincin da mu ke ci,na yau-da-kulllum.
amfaninsa shi ne;  Gina jiki domin Kara girma tare da habaka kirkirraren fasalin  gangar jikin.(mussaman a kananan yara). 
shi ne Kuma a ke amfani wajen cike duk wani gibi, da aka rasa,ta  sanadiyar jin rauni.hakan Kuma akan Yi amfani da Wanan rukunin sinadarin, wajen Samar da ruwan kaifi,(acid and enzymes) da Kuma wa'yansu ruwan-madarar-maganadisu wato (hormones).
a wasu lokutan Kuma, idan ta Kama a kan yi amfani da shi a matsayin makamashi domin Samar da kuzari.
Akan samu Wanan rukunin sinadarin abincin ne  a cikin abincin da mu ke ci ;kamar ; kifi, kwai, nama, wake,  gyada, Madara da kuma,hanta.

2).rukunin sinadarin bayarda kuzari .
(carbohydrates).

Wani rukunin sinadarin Abinci ne da Allah ya kirkira ya Kuma ajjiyemana shi a cikin daukacin dukan cimakarmu ta yau-da-kullum.musamman kayan abincin da ke  dauke da sinadarin sukari.
   amfanin Wanan rukunin sinadarin, a jiki, ,shi ne; Samar da kuzari ko karsashi a jiki.wanda shi ne ke taimakamana wajen gudanarda harkokinmu na yau-da-kullum.kamar dai amfanin fetur a cikin babur ko mota,.
A kan same shi ne,a cikin kusan  dukan kayan abincin da mu ke ci.kamar ; gero, dawa, masara,  shinkafa, alkama, da kayan lambu da kuma kayan marmari.kusan dai za a iya cewa duk wani- abinci ko abin sha Mai dauke da  dandanon sukari,to ya na dauke da wani nau'i na wanan sinadarin.

3).rukunin daskarraren kitse da na maiko:(fat and oil)

:Wanan rukunin sinadarin Kuma ya kunshi duk wani abinci da ke dauke da sinadarin kitse ko maiko.
 Amfaninsa ,shi ne; ,ya kan je ne ya lullube duk wata masarrafa,(organ) a cikin jinkin Dan Adam.ya kan yi haka ne domin bata kariya.kamar dai yadda za ka gani a jikin Koda ko zuciyar lafiyayyar dabbar, da  aka fede.
Yakan je ya lullube su ne; domin ya zamarmusu,kamar katifa Mai laushi ,da Kuma bada kariya Hadi da dumama masarrafan.wani amfanin kitse shi ne; yakan taimaka wajen fito da sifarr mace,musamman a lokacin da ta Kai mizani. Inda zai kara bayyana mata da wa'yansu sassan,kamar  bayanta da ,kumatu, sai ka ga sun dan mulmule,.idanuwanta ma za ka ga sun Kara sheki,fatarta da mamanta duk za ka ga sun bayyana.
A hakikanin gaskiya Kuma, kitse ne ke sanya laushi da shekin fata a kowanne bangare jinsi.duk wa'yanan ayyukan ,kitse ne ya ke yinsu.domin a duk in da ka duba a wa'yanan wuraren, za ka gan shi kwance,a karkashi.
.haka Kuma a wasu lokutan idan jiki ya nemi sinadarin,kuzari bai samu ba (kamar a lokacin azumi).to jiki  kan narka Wanan ajiyyayen kitsen domin samarwa kansa  kuzari.
a kan samu Wanan rukunin sinadarin kitse da mako ne,a kayan abinci kamar ;  nama, gyada, kifi, madara, da Kuma kayan lambu.sai dai da akwai bukatar mu kula: ,kasancewar daskararren kitse ya na da I'll a ga lafiya idan ya yi yawa a jiki.,.Amma Sauran kamar man kifi, man zaituna,da manja,da na Sauran kayan lambu,duk sai ka ci abinka,,hani'an-mari'an.

4.rukunin sinadaran baitamin da kuma na albarkatu.;(vitamins and minerals).

 sinadarin baitamin da na albarkatu wa'yansu sinadarai ne da jiki  ke bukata domin gudanar da,ayyukansa cikin salama.daga, cikinsu akwai masu kara karfin massarafai da masu kara kwarin kashi da na hakora,akwai kuma masu karawa jini kuzari,hadi da taimakawa wajen kara karfin garkuwar jiki,domin kariya daga cuttutuka,musamman a kananan yara. 
Amfanin wa'yanan snadaran,shi ne Kamar amfanin taki a  gona. da a ke zuba wa shuka,domin karamata kuzari.
Sinadaran baitamin, a na samun su ne a cikin kayan abinci kamar madara ,kwai, da daukacin kayan lambu,Hadi da kayan marmari.
Su Kuma sinadaran albarkatu,(minerals).a na samun su  ne ,a cikin Madara gishiri, kanwa, da kayan lambu har ma da na marmari. 
A taikaice dai duk wani abinci da mutum zai ci a a duniyar Nan,to hadaka ce ta wa'yanan rukunan sinadaran 5.kuma duk wani Abu da za ka ci in dai bai kunshi wa'yanan sinadaran ba.to a yadda ya shiga ta bakinka ; a haka zai fita ta dubura.(wanan idan ba Mai cutarwa ba ne kenan)
Domin su hanji ba su ma San shi ba,ballantana su Yi kokarin tsotse shi.sai dai kawai su kalle shi ,su ce da shi "a sauka lafiya).haka Kuma wa'yanan sinadaran, da mu ka Yi bayanin su.jikinmu na bukatar su ne dai-dai gwargwado.idan ma ka antayo su da yawa.to zai kwashi iya bukatarsa ne Sauran Kuma ya ce"Allah-raka-taki-gona". Hakan na nufin idan ya kasance cimakar ba ta kitse ba ce,to za ta fita a mutunce. amma idan kitse ne to babu mamaki a jiyo ku a makota.kuma a duk lokacin da ya bukaci fitowa,dole ne  ka antaya izuwa makewayi, a gudane,idan ba ka so ya kwance maka Zane a kasuwa.

Tafiyar abinci, daga baki, Zuwa dubura.

Tsarin Nika da tace abinci: ,ya na farawa ne daga lokacin da mutum ya yanki Loma ya antaya ta a baki,da ga Nan hanci ne zai shaki kamshin abincin,ya tura sakon izuwa ga kwakwalwa,Nan ta ke ita Kuma za ta umarci mafitar yawu,da ke kasan harshe, da, ta saki yawu,hakora Kuma su Fara darkake abincin,daga  Wanan matakin idan sinadaran yawun su ka hadu da abincin, za   su Fara saraffa abincin, su fito da wani nau'in, na sukari.,da zarar hakora sun darkake abincin,harshe, Kuma ya cakuda shi da yawu.sai harshe ya ingiza garwayyayen lomar abincin, I Zuwa ga makogwaro,da zarar abincin ya je  daf da kofar makogwaron, sai kofar ta rufe,ta na rufewa,sai a canjawa abincin hanya inda za a tura shi ta wani kwararo,(jannai). Wanda a kodayaushe ,a tsuke ya ke.da zarar abincin ya shiga cikin Wanan kwararon,sai kwararon ya tura abincin izuwa kasa,a irin yanayin tatsa,ta yadda ko da kan mutum ya na kasa, kafafu na sama, (upside-down)   abincin ba zai dawo ba,,idan abincin ya je can kasa,za a bude Masa wata kofa,sai ya fada cikin tumbi.daga Nan Kuma tumbi zai Fara jujjuya abincin Hadi da narka wasu sinadaran, kitse ,ta hanyar amfani da wa'yansu sinadaran kaifi da hanta  ke samarwa,.da ga Nan bayan abincin ya niku, sai a sake Buda Masa wata kofar,ya Kara shiga,ya na shiga Nan ma za a Kara Nika shi hadi da  tace wa'yansu sinadaran ,a Kuma sake tura shi izuwa ga wata kofar inda zai tsinci kansa a wani yanayi na ha'ula'i.domin a Nan ne zai hadu da wa'yansu sinadaran kaifi wato (acid)-wa'yanda karfinsu ya fi na can baya.to bayan an narka abincin gabadaya.sai wa'yansu kananun halittu,masu Kamar tsiro,da ke cikin kananan hanjin ,su fara zuke sinadaran abincin, wa'yanda a turanci a ke kira(villi).ta hakan za su tsotse duk wani abu Mai  amfani da ke cikin abincin, bayan sun tsotse komai.sai su tura sinadaran izuwa ga hanta,ta wani kwararo da ke tsakanin hanjin da hantar. daga Nan ita kuma hantar ,za ta daidaita sinadaran abincin, ta tace duk wata guba, da sinadaran ke dauke da ita.ta Kuma sanya masa, madarar maganadisun saita sukari,da saifa ke samarwa.wato (insulin hormones).to  da ga Nan hantar zata lodawa kwayoyin ijni kayan sinadaran abincin, ta tura su izuuwa ga zuciya ,inda a Nan ne ita Kuma zuciyar , za ta harba jinin mai dauke da sinadaran,izuwa ga sassan jiki gabadaya.
Shi Kuma sauran tukar abincin da ke cikin hanji, bayan kananun hanji sun Gama tsotse komai ,sai  su tura Sauran tukar abincin izuwa ga manyan hanji,inda a nan ne , su Kuma za su Kara tsotsaye duk wani abinda ya rage,a ciki har ma da sauran ruwa-ruwan da ke ciki.,sai Kuma su sake tura Sauran tukar izuwa ga dubura inda a Nan ne miliyoyin kwayar batiriya,(bacteria). za su Kara darkake Wanan dusar,,su maida ita Kashi domin sai a Nan ne ma ta ke Fara wari.inda daga karshe Kuma, a nan ne,za a Yi bankwana, a fitar da Wanan dusar,a matsayin Kashi,,,,,,,sai Kuma wani jikon...


OLSA/GYAMBON CIKI.

OLSA : ko gyambon ciki,ita ma dai za mu iya Kiran ta ne da tangarda.ko Kuma muce kasawar bangon tumbi ko hanji.domin ai ita ba cuta ba ce,wato
Akan same ta ne a duk lokacin da bangon cikin jikin tumbi ko bangon cikin jikin hanji ya samu rauni,ko jimuwa ko Kuma konewa.ya kan samu raunin ne idan ruwan kaifin da hanta ke samarwa su ka raunata shi.duk da cewa dai a kan sabunta shimfidar tumbi a duk tsawon sa'o'i talatin. To wanan gyambon nee ke haifar da matsalolin zafin ciki, kwarnafi, amai, kumburin ciki, yawan jin yunwa,da dai sauran su. a wa'yansu lokutan Kuma har da kwayoyin cutar bakiteriya kan shiga cikin gyambon su Kara cabe lamarin.sai ka ga an yi ta shan magani amma gyambon ya ki warkewa.musamman ga wa'yanda bangon tumbinsu ba ya da kwari.da Kuma masu Shan sigari ko barasa.

ga Mai bukatar karanta wa'yanan darussan, a harshe turanci,sai ya ziyarci dayan shafin,Mai adireshi kamar haka;
www.simplegeneralscience.blogspot.com.
Domin sharhi,ko tsokaci ;sai ka antaya su a cikin Wanan akwatin sharhin.
Ga Mai neman Karin bayani Kuma,sai ya turo sako ta.....,09035097765.fatan alkhairiiii.ga masu karatu...sai Kuma mun sake jamewa a darasi na gaba,,,,,

No comments:

Post a Comment