Sunday, December 16, 2018

(12).Tsarin zagayar jini a jikin Dan Adam.

Tsairn zagayar jini a jikin Dan Adam wani tsari ne da a ka shirya musamman domin rarraba sinadarai da albarkatu hadi da kayan alatun da ke cikin abincin da mu ke ci.,Kuma shi ne ya ke rarraba  sinadarin nan da jiki ya ke bukata na oksijin.(oxygen)wato shi ne ya ke raba duk wata ganima da mutum ke antayawa izuwa ga rumbun cikinsa.wato Jini ne ke raba duk wata garabasa da a ka samu izuwa ga biliyoyin kwayayen halittar da ke sassa daban-daban a cikin jikinmu.kuma shi ya ke  kwamaso iskar sinadarin kabon.(carbon). da jiki ba ya bukata, ya yo awon gaba da ita,ta fito ta hanci,
(can Allah raka taking gona.)
 duk da cewa dai iskar ta na da amfani ga shukoki da tsirrai.
A Wanan tsarin,zuciya ita ce uwar tafiya,domin ita ce ta ke harba jinin ya shiga kowanne lungu da sako na jikin Dan Adam.
zuciyar kan  yiwanan aikin ne a bisa umarnin kwakwalwa na dindindin.duk da cewa dai ita  ma zuciyar ta na da nata sinadaran lantarkin da su ke bata kuzarin yin hakan.ta na kuma harba jinin ne ta hanyar kumbura da sacewa,.jinin kuma kan bi ta wa'yansu manya da kananun kororai, ko magudanai ne har ya riski  kowanne lungu-da-sako na jiki.
Wato hakan na nufin; su
manyan magudanan jinin, su na da 'ya'ya.su Kuma ' ya'yan su na da jikoki. ,jikokin ne  ke isar da kayan da jini ya dauko kai tsaye izuwa ga kwayoyin hallitar.
sai dai kuma idan jinin zai dawo,ba ta wa'anan magudanan jinin da ya je ya ke dawowa ba,ya kan dawo ne ta wasu magudanan jinin daban.,suma dai sak iri  daya ne da wa'yancan.
Idan ya dauko lodin iskar sinadarin ,a hanyarsa ta tafiya, za ka ganshi da launin ja.amma da zarar ya sauke wanan lodin na sinadarin iskar oksijin,ya kuma sankamo wacan iskar kabon, sai ka ga ya canja launi,ya dan yi duhu-duhu haka. A haka kuma zai kaiwa zuciya jinin, domin ta sake yi masa garambawul,tare da sake aiko shi.
 Yadda Tsarin ke gudana  shi ne; zuciya ta na da wa'yansu kusurwowi ko ramuka guda hudu,.
A bangaren dama rame biyu,a bangaren hagu ma rame biyu.,ta na Kuma da matsukai, da su ke tsukewa a kofar kowanne ramen.sukan wangame kofar ne a duk sanda zuciyar ta Basu umarnin yin hakan. Wato a duk lokacin da sinadaran lantarkin zuciya su ka ratso ta kansu.
Tsarin zagayar jini yakan fara ne daga lokacinda, jinin da zai fito daga cikin jiki (,Mai dauke da iskar kabon), ya  shigo zuciyar  ta ramen sama na dama,daga Nan sai ita Kuma matsukar ramen kasa na daman ta bude, ta yadda jinin zai fada cikin ramen kasa na daman, ya na shigewa, sai matsukar ta rufe a dai dai lokacin da zuciya zata matse.,ta na matsewa sai kawai ta harba jinin izuwa ga wani baban kwararo, da ya hada zuciya da huhu.(Wanan matsewar ce ke sa jinin ya fito daga cikin zuciyar da karfi).,da zarar Wanan jinin ya Isa ga huhu.wato ,a daidai lokacin da mutum ke zuko numfashi, Mai hade da  iskar Nan mai sinadarin oksijin.(domin ai mukan zuko iskar ne ta kofofin hanci, har izuwa cikin huhu).da ga Nan Kuma sai  iskar sinadi ta Kara sauka can kasan huhu,cikin Wa'yansu kananun, zagayayyayun ramuka ko koyaye ,inda a Nan ne iskar za ta hadu da Wanan jinin da ya fito daga zuciya,sai su rungume juna, cikin shaukin soyyaya da kauna,inda a Nan ne dai iskar sinadarin oksijin din ke narkewa a cikin Wanan jinin da zuciya ta Aiko, a dai-dai Wanan lokacin ne ita ma  iskar kabon, da jinin ya  yo guzurinta da ga can cikin sassan jiki,ta ke  daka tsalle ta fito daga cikin jinin  ta biyo Wanan iskar da  mu ke amayowa a yayin saukar numfashi,sai mu antayo su waje , izuwaga sararin uwa duniya.inda a Nan mu ke cewa da su .( A saukakkaken lafiya).
To da ga Nan ,shi kuma Wanan jinin da zuciya ta Aiko ,domin wanan musayar,zai dawo mata,da guzurin sinadarin da ta turo shi ya karba, wato sinadarin oksijin.
sai dai kuma a kofar da ya fito daga zuciya zuwa huhu, ba ta Nan zai shigo ba,zai shigo ne ta kofar zuciyar ta ramen sama na hagu.shigowar sa ke da wuya ,sai  matsukar kofar hagu ta kasan ta bude Masa kofa ya shiga ramen zuciyar na kasa na hagu,ya na shiga nan, sai kawai  zuciyar ta sake tatso shi tare da ingiza shi  izuwa ga sassan jiki,domin rrarraba Wanan iskar sinadarin da ya karbo daga huhu.yakan biyo ta wani babban kwararo ne, da ya hada zuciya da Sauran sassan jiki gabadaya.inda kwararon zai Yi ta rabuwa,ya na yin rassa,har dai a samu jinin ya isar da kayan sinadarin izuwa ga dukan  kwayoyin hallitun da ke jikinmu gabadaya.daga nan Kuma jinin zai sake sankamo wanan iskar kabon din ,da ya ke karbowa daga cikin koyayen hallitun jiki,wato (cells) .domin ita ai kamar  shara ce ko hayakin da jiki  ke fitarwa ,yayin da ya ke Kona sinadarin makamashin Abinci , domin Samar mana da kuzari,,wato (cellular respiration and ATP wast ).
kenan,idan ya bayar da waccan ya Kuma sankamo Wanan shaarar, sai ya sake dawowa da zuciya da Wanan Sharar.zai Kuma shigo zuciyar ne ta wanan kofar zuciyar  ta kusurwar sama ta dama.haka dai abin zai yi ta maimaita kansa har sai iya lokacinda allah ya dakatar da shi.

RARRABA ALBARKATUN ABINCI.

A bangaren rarraba sinadarai da albarkatun abinci Kuma.ya kan Fara gudana  ne , daga lokacin da kananun hanji  da ke aikin narkawa da zuke sinadaran abincin da mu ka ci su ka zuko sinadaran abincin,idan suka zuko sinadaran sai su tura sinadaran  izuwa ga hanta,ita Kuma hantar , Nan take za ta  tace shi ta sanya mishi kayan armashi, ta kuma kintsa shi Hadi da daidaita mizanin sukari da gishirin abincin, ta yadda kananun  kwayoyin halittun jiki za su iya sarrafa shi  su kuma amfana da shi cikin salama,wato ba tare da ya yi musu illa ba.
bayan hantar ta kammalla Wanan aikin ne.sai ta aikawa zuciya jinin Mai dauke da lodin kayan sinadaran abincin inda a Nan take it kuma zuciyar , zata sake lodawa kwayoyin jajayen jini wa'yanan  sinadaran,domin a kaiwa kowa rabonsa.,sai dai shima jinin, ya kan lakume nasa rabon, tun a hanya.
Bayan wa'yanan tarin ayukan , da tsarin zagayar jini ke Yi .shi ne kuma a ke baiwa sakon ruwan madarar maganadisu wato (hormons) ya kai su inda a ke bukatarsu.
A takaice dai duk wani Abu da za a Yi watandar sa a cikin jiki,to tsarin zagayar jini ne  ke rabawa ya Kai wa kowa rabonsa.
domin ai hakan ne ke sa   ka  ga mutum ya na ciwon kunne Amma Kuma sai ka ga an Yi Masa allura ta mazauninsa.

HAWAN JINIIII.

 Hawan Jini wani nau'i ne na tangarda ko tarzoma da ake samu a jikin Dan adam a wa'yansu lokutan.
domin ai shi hawan Jini ba ciwo ba ne,tangarda ce.kuma Maganar gaskiya ba jini ne ke da alhakin miliyoyin rayukan da ke salwanta a sanadiyar Wanan tarzomar da a ke Kira da hawan Jini ba.
 Abinda na ke kokarin bayyanawa a Nan shi ne ;shi hawan-Jini ; wata 'yar tarzoma ce da a ke yawan samu a tsakanin, zuciya da kwakwalwa da Kuma magudanan jini,wanda hakan ke sa har a cutar da sauran massarrafan jiki.

A lokuta da dama, tarzomar ta kan shafi Wasu sassan jikin ko massarrafan da ba su da hannu  a faruwar lamarin.
 Kuma maganar gaskiya idan har za a yi adalci a lamarin cakwalkwalin cakwakiyar hawan Jini, ba hawan jini ya kamata a kira hatsaniyar ba.sai dai a ce boren kwakwalwa da zuciya ko Kuma a ce tsukewar magudanan jini.idan Kuma fadar hakan zai tada jijiyoyin wuya,sai a ce KASAWAR ZUCIYA. 
domin ai shi jini,Dan aike ne kawai.
Wato Abinda na ke kokarin sake bayyanawa a Nan shi ne matsalar hawan jini da a ke fada. Maganar gaskiya abin ba laifin jini ba ne,(shi kadai) ba Kuma laifin zuciya ko kwakwalwa ba ne (ita kadai). 
A misalance za mu iya cewa :iska ce ta kada,shi Kuma fure ya tsinke daga jikin reshe ya fado."kenan laifin na waye": sai mu ce ba laifin  fure ba ne, ba kuma  laifin reshe ba ne ,haka-zalika ba  laifin iskar ba ce.
  Wato gaskiyar Abinda ya ke faru  shi ne ; ,jini yakan Yi aikin sintiri ko zagayen sa ne a cikin farfajiya da tsarin titunan magudanan jinin da aka shirya masa.to a Wasu lokutan idan aka samu wata 'yar matsalar , hankalin mutum ya dan tashi , har ya firgita ko kuma idan ransa yai matukar baci.to a Wanan yanayin kwakwalwa ce ta ke   harzuka ,ta Kuma harzuka sauran sassan jikn,inda za ta bada umarnin gaggawa ga Sauran sassan jiki,ta hanyar bada umarnin sakin Wa'yansu ruwan madarar maganadisu,(hormones) wa'anda su ke da alhakin  sanya wa'yanan magudanan jinin, su matse. 
su ne Kuma ke da alhakin harzuka zuciya,ta  yadda za ta tattaro iya karfinta domin ganin ta tursasa  jinin ya tafi,ta kowane Hali. To a Wasu lokutan, a irin Wanan halin ne magudanan jinin ke tushewa,jinin ya kasa samun damar Isa a wa'yansu wuraren, a Wasu lokutan kuma magudanan jinin ne ke fashewa,shi Kuma jinin ya balle,inda a nan yakan riski wa'yansu  wuraren da ba a so ya shiga.to a haka ne a ke samun wanan matsalar da a ke Kira da buguwar jini wato,(stroke).sai mutuwar baren jiki ta biyo baya.idan Kuma a zuciya ne a ka samu matsalar toshewar wa'yanan kananun magudanan jinin,sai a samu buguwar zuciya.wato (heart attack). A Wasu lokutan Kuma tsokar zuciyar ke yin rauni ta saduda sai ta bada gari wajen kokarin ingiza jinin.wanda a Nan ne a ke samun matsalar da a hausa za mu iya kiranta  da kasawar zuciya,Wacce a turanci kuma a ke cewa (heart-failure)
To a irin Wanan tarzomar ce a ke samun wa'yanan matsalolin. 
Amma Kuma  ,idan ya  kasance cewa kai lafiyyayen mutum ne .to wanan tarzomar  za ta saita kanta bayan wani Dan lokaci.
To a haka ne dai idan wanan tarzomar na yawan  faruwa a gare ka, sai a ce ka kamu da hawan jini.idan hakan na faruwa kuma ya   dauki lokaci Mai tsawo bai lafaba,to a irin Wanan yanayin ne ,sai kawai ka ji an ce!!!!!.
Kenan dai kwakwalwa ce ke Fara tayar da tarzomar daga Nan, sai zuciya ta karba,yayin da su Kuma magudanan jinin  ke matsewa jinin lamba,shi Kuma jinin idan ya ji ba  sauki ta bangaren zuciya da Kuma ta bangaren magudanan jinin,sai kawai ya fasa magudanan jinin,domin yiwa kansa mafita.faruwar hakan ke da wuya,musamman idan a kwakwalwa ne,sai kawai ka ga mutum ya fadi!!.a wasu lokutan kuma zuciyar  ce ke kasa tursasa jinin .sai ta tsaya cakkk!!!!!.wato kasawar zuciya,wanda hallau dai a wani kaulin a ke cewa  (heart-failure)
A Wasu lokutan kuma,
 , hanyoyin jinin ne ke tushewa,da kansu,sanadiyar mummunar kiba ko taruwar kitse a magudanan Jinin ko ma a wa'yansu wuraren. faruwar hakan kuma ke da wuya,sai kawai ka ji an ce !!!!!.Allah gafarta masa.

To a Yanzu kenan wa ya kamata a tuhuma a bisa faruwar wanan lamarin???

 A  yanzu dai hukunci a bayyane ya ke...
A bisa hakan ne  na ke mai tunatarwa ga kungiyoyin  Kare haken jini,da su wayar da kan al'umma,a kan wanna lamarin ,domin ganin an dawowa da jini martabarsa.wato a daina cin zarafinsa a na doramasa,alhakin da ba NASA ba. 

AWON JINI.

Lafiyayyen mutum,a na so ma'aunin auna Jini ya nuna karfin harbin jininsa  a  maki 120. Zuwa 130,a mahangar mizanin kumburin  zuciya,wato (systolic)
A ma'aunin sauka ko sacewar zuciya Kuma,;a na so ya tsaya 80-zuwa-90..( diastolic).

Adadin bugun zuciyarka Kuma a na so ya zama akalla sau saba'in 70-100,zuwa  dari a cikin minti daya.
Idan awon hauhawar karfin jininka na yau-da kullum ya haye Wanan mizanin,to hakan manuniyace da ke alamantarda cewa da akwai 'yar matsala.sai dai kuma hakan ba ya na nufin rayuwa ta zo karshe ba.a a . matukar dai  za a kiyaye Shan maganin da likitanka ya doraka a Kai,to in Allah ya yarda lafiyarka za ta gudana kamar ta sauran mutane.

Har izuwa yanzu dai Masana ba su tantance hakikanin me ke kawo tangardar hawan jini ba,.sai dai sun zayyano abubuwan da  ke alakantuwa da shi,su ne kamar haka:
1).gado
2).kiba
3).shekarun manyanta
4).yawan cin gishiri fiye da kima
5).rayuwar kunci
6).rashin motsa jiki
7).karancin bacci
8).karancin samun nutsuwar kwakwalwa,.
(idan kuma ni ma zan iya tofa albarkacin bakina ,sai in ce; da
9).son-maso-wani)

FADAKARWA.

babban kalubalen da HAWAN Jini ke tattare da shi shi ne;
A mafi yawanci Ba ya nuna alamun kamuwa da shi.wanda hakan ne ya sa ya ke da matukar amfani cewa mu Rika Zuwa cibiyoyin kiyon lafiya na kusa da mu domin auna jininmu akalla sau uku a shekara.
Bayan wa'yancan sabbuban da ke ta'azzara hauhawar jin,da akwai wa'yansu hanyoyin da ke Sanya Jini ya  hau. Domin a wa'yansu lokutan,mutum ya na bacci zai Yi mafarki,a cikin mafarkin ne Kuma ransa zai baci ko hankalinsa ya tashi  Daga Nan Kuma sai jininsa ya hau,sai ka ji an ce an kwanta da shi Amma an tashi ba da shi ba.
hanya ta farko domin kaucewa hawan Jini shi ne:MOTSA JIKI.
ga Mai neman Karin bayani ko yin sharhi, sai ya antaya su  cikin akwatin kasan shafin.ko ka aiko da sakon kar-ta-kwana ta wanan lambar;09035907765
idan kuma ka fi gane  harshen ingilishi, a kan na hausar,sai ka ziyarci dayan shafin 
www.simplegeneralscience.blogspot.com.

No comments:

Post a Comment