Friday, December 21, 2018

(7).Sassan jikin Dan Adam da amfaninsu(3)

7).tsoka.

soka ita ce ta fi komai yawa a jikin Dan Adam. sai dai kuma duk da yawan da ta ke da shi ,wanan ba zai sa Masana sun  kirata da massarafa ba.sai dai mu martaba ta mu ce da ita tantashi.wato tantashin kulli,wanda a turanci a ke kira da .
(connective tissue).aikin  tsoka a jiki shi ne gudanarda kowanne motsi ko juyi na zahiri.wato duk wani motsi ko aikin da Dan Adam zai yi a zahirance,  ya na yin sa ne ta hanyar amfani da tsokoki  biyu ko fiye da hakan.domin kuwa a misalance ; tsokoki kusan dari biyu ne ke bada gudummawa,yayin da mutum ke yunkurin tako daya da kafarksa.

A kimiyance,
tsokokin da ke cikin jikin Dan Adam nau'i uku ne ..
1).ta farko ita ce, tsokar gautsi; wacce da ita a ka yi amfani wajen kera zuciya da murfin zuciyar.,
2).Ta biyu Kuma; tsokar moli: Wacce da ita ce  a ka Yi amfani wajen Samar da daukacin Sauran kayan ciki.kamar hanji, huhu,magudanan jini da dai sauransu.
3).Ta ukun Kuma ; ita ce matar Kashi.mun kira ta da hakan ne ,kasancewar , a duk inda za ka ganta,to za ka samu cewa, tana manne ne da kashi.ita ce Kuma Dan Adam ya ke sarrafata ta yanda ya ke so,Amma wa'yancan sauran biyun na farko,da bayaninsu ya gabata, ba da tunaninsa ya ke sarrafasu ba.hakan na nufin alhakin sarrafa wa'yancan tsokokin biyu an Mika shi ne kacokan  izuwa ga wani bangare na kwakwalwa.kasancewar aikin sarrafasu ,aiki ne da ke bukatar kulawa,ta dindindin wato babu zuwa hutun rabin lokaci ko na karshen mako.
Wanda hakan manuniya ce da ke nuna cewa ; idan aka barwa mutum alhakin sarrafasu,to wata rana  zai iya mantawa,ko yayi bacci,Wanda Daga Nan Kuma sai a samu matsala !!!.

domin taimakawa wajen tabbatar da lafiyar tsokokin gaba daya, sai mu lazimci motsa jiki.mussaman na zahiri.wato (physical exsercis)
7)Kashi:

kashi , ba massarrafa ba ce, tantashin kulli ne. A nazarance za mu iya cewa Kashi wata daskarrariyyar halitta ce Mai yanayin kam-kam a jikin Dan Adam.   amfansa a Jiki,shi ne  zamewa  gimshiki ko dirka wa gangar jikin Dan adam. wato shi ne ke taimaka wa  mutum wajen dogaro ,a tsaye ne waje daya ko Kuma a lokacin tafiya.wanda hakan ne ma ya  sa a duk lokacin da Kasusuwan mutum su ka Fara rauni (saboda shekaru).sai ka ga dole sai an nemi sanda ko katako domin yin dogaro.
masana sun ce kowanne mutum da za a Haifa a duniyar nan,ya kan zo ne da kasusuwa sama da Dari uku,Amma kuma da ya fara girma a hankali, sai su Fara canjawa da harhadewa da junansu, har dai su dawo Dari biyu da shida (206). (sunan wata mota kenan).
Amfanin Kashi a jikin mutum shi ne kamar haka:
kashi yana bada gudumuwa wajen yin kowanne irin aiki na zahiri.ya na  kuma bada muhalli tare da bada kariya ga wa'yansu sassan jiki ko massarafai,wa'yanda a irin yanayin hallitar su , ba sa iya jure gwagwarmaya. 
Wato kamar  irin su kwakwalwa, zuciya, hanta,da huhu.wasu  daga cikin Kasusuwan Kuma,   wato masu dauke da bargo. sukan bada gudummawa, wajen hayyayafar kwayoyin hallitar jini.

Falallar Kashi ita ce ;  a gabadayan zubin Kasusuwan da ke jikin Dan Adam; sukan zaizaye  kansu su Kuma sake gina kan su a duk Bayan shekaru goma.
A saukakkaken harshe hakan na nufin Kasusuwan da ke jikinmu; Allah na  sabunta Mana su a bayan kowa'yanne shekaru goma.(amma a hankali-a-hankali ya ke Wanan aikin,ba Kai tsaye ba).

Cin abinci ko Abin Sha Mai dauke da Sinadarin kalshiyan (calcium) tare da motsa jiki a-kai-a-kai,  da kuma  gujewa mugun wargi ,,,wato idan a ka hade Wa'yanan al'amuran da mu ka zayyano ,sukan Kara karfi da lafiyar   kashi.
8)Fata:
fata massarafa ce mai matukar muhimanci a jikin Dan adam.ita ce ta kunshi kaso talatin cikin Dari(30% ) na zubi da nauyin halittar Dan adam. 
An shimfida Mana ta ne domin suturtawa da Kuma samarwa jiki kariya . An Kuma  ribanyata ne a sala-salan shimfida har  sala uku.
 Shimfidar  farko ; ita ce wacce mu ke gani  mu ke mu'amala da ita.ta biyu Kuma ita ce wacce  mutum ya  ke gani idan ya dan  kuje.ta uku Kuma ita ce wacce a cikinta ne turakunan gashi da rumbun kitse da magudanan jini da Kuma kanun wayoyin lakka su ka yada-zango.
amfanin fata shi ne ; suturta gangar jiki da Kuma bayar da kwakwakwarar kariya wa daukacin masarautar jikin Dan adam.hakan na nufin, Ita ce ke tabbatar da cewa ba wani bakon haure da zai samu damar shigowa cikin gangar jikin Dan adam balle har ya farmake ta. 
ita  ma fatar; A kan   sake sabunta wanan shimfidar ta farko ta sama,a duk bayan wata daya.
bayan duk Wa'yanan sinki-sinkin alfanu da fata ke da shi,
 ta kan kuma taimaka wajen dumama jiki da Kuma sanyaya shi, idan bukatar yin hakan ta taso.ta kan yi hakan ne ta hanyar fitar da gumi.bugu-da-kari Kuma ,fata wakiliyar kwakwalwace,
Domin ita ce ta ke karba da aikawa kwakwalwa sakon yanayin muhalli,sanyi ko zafi, da na tabi har ma da na Jin radadi.
9).ido:

 Maganar gaskiya har izuwa yanzu da na ke Wanan rubutun,ban Kai ga iya tantance banbancin kalmar idanu da Kuma idanuwa ba a tattaciyar hausa. ,kasancewar duka kalmomomin biyu ,su kan  bada  ma'ana kusan iri daya.kamar dai a bokiti da  botiki.
A bisa wanna ne na ke  fata cewa ; idan wata Rana hanya ta bisar da wani daga cikin malamai ko ya'n-uwana dalibai ta wannan shafin.to da Allah,a Dan yi kokarin nusar da ni,domin yin hakan zai taimaka wajen warware 'yar tantamar da ke gefen kaina. 
 Amma dai Yanzu za mu Dan ari kalmar idanu,kafin waccan amsar ta zo.sai mu ce;  idanu wa'yansu hallitu ne masu matukar amfani .domin, su ne fitila Kuma jagororin tafiyar da rayuwar Dan Adam.
amfaninsu, ba zai kirgu ba,domin, su na daga cikin manyan wakilan kwakwalwa.
Kasancewar kwakwalwa ta na da wakilai  har guda biyar,daga cikinsu Kuma akwai ido,kusan ma za a iya cewa su ne mafi muhimmanci daga ciki.
Domin su ne  ke aika wa kwakwalwar sakon haske na yanayin sifa da launi da  fasali.
Wato Idanu kan Yi wa kwakwalwa hidima ne ta hanyar sarrafa haske.
yadda abin ya ke shi ne; ido kamar madubi ya ke,ya na da wani karau ko gilasai a can daga tsakiyar sa.wato a cikin wanan bakar kwayar da mu ke gani.a cikinta ne haske kan ratsa ,idan ya ratso sai shi Kuma faranti idon ya dauki hoton wanan hasken.domin ai ,Wanan zagayen bakin na tsakiyar, ido da mu ke gani, asalin sa, ba baki  ne tilin ba,hasali ma fararen sala-salan gilashi ne,da ke a rubanye wato  ,wani- a- kan-wani, har sai ka gan shi kamar baki.amma Kuma   ai a wasu nau'in mutanen, masu fararen fata kamar ,turawan tsakiyyar tarrayyar-turai.(Russian federation). za ka ga wanan bakar kwayar a launinta na gaskiya, wato fari kalll.
A takaice dai,shi  ido yakan ga Abu ne ta amfani da hasken da ya ratsa shi.idan hasken ya shiga ta cikin idanu, sai ya je can ya daki bangon ido na baya sanan ya sake dawowa, a yanayin kasa-ya-koma-sama,wato (upside-down)daga nan Kuma da akwai  wa'yansu jijiyoyin lakka da suka fito daga bangaren kwakwalwa na baya, inda a Nan ne a ke karba tare da saraffa  wanan sakon hasken,wato a Nan me ake maida shi hoto,ta yadda hankali zai iya karanta shi. Kenan shi ido da zarar ya cilla Wanan hoton da ya dauka,to shi ke nan shi  ya Gama nasa aikin. Sauran  kuma duk kwakwalwa ce za ta Yi.

Falallar idanuwa

.(mu Dan aro wancan kaulin ba )


A kiyasance idon Dan Adam ya na da karfin tangaras, da ya Kai mega fesal 750. (750,mega pixel).
 ya na Kuma da fikirar tantance launuka kala dai-dai har kala miliyan goma(10,000,000,). 
Hakan Kuma ido ya kan  kifta akalla sau dubu goma Sha daya da dari biyar,(11,500,).a kowace rana,wanan a jinsin mata kenan . A maza kuma (10,600). 
ya kan Kuma Yi wanan kiftawar  ne domin wanke kwayar idon da Kuma sanyayata da ruwan sanyi masu sinadari. 
A falsafance za mu ga cewa;
Ya na da matukar amfani  mu nisanci mugun wargi da Kuma kurawa na'urori masu kaifin haske sosai ido,hadi da kauracewa,haske nan Mai yanka ido,wato (ultraviolet light). Wato iri hasken Nan da ke fitowa kai-tsaye Daga Rana da Kuma hasken tartsatsin walda,wanda ke fitowa yayin da Karan walda  ke barbarar kulla zumunci a tsakanin karafa.
duk za mu Yi hakan ne domin ingantawa tare da Kare lafiyar fitulunmu..
10).hanci:
shi ma dai wata halitta ce Mai cike da Al'ajabi, hanci ya faro ne tun daga kofofin hanci na waje, har IZuwa makogwaro ya hauro wajen kunnuwa, har  dai IZuwa can saman goshi.shi ma wakilin kwakwalwa ne.   Shi ne ke aika wa kwakwalwa sakon kamshi ko na akasin hakan.  ya na da wa'yansu kananan na'urori  masu kamar Karan gashi a cikinsa. su ke shinshino sinadarin yanayin kamshin ko na wari har ma da na  hamami,sai ya aika su IZuwa ga kwakwalwa, a yanayin lantarkin .
Hallau dai Hanci ne ke yin kokari wajen tacewa, tare da dumama iskar da mu ke Shaka , a yayin da mu ke zuko iskar numfashi.

Falalar hanci.

: hanci ya na da fikira da nagartar  da zai iya tantance wari kala dai-dai har kala dubu goma.(10,000).

 domin kulla da lafiyar hanci, sai mu nisanci maidashi kamar salansar tsohon babur...ko kuma zukar shaken i gargajiya ,ba bisa ka'idaba.
ga Mai sha'War karanta Wanan darasin,a harshen turanci, sai ya garzaya kai-tsaye izuwa Wanan shafin.
www.simplegeneralscience.blogspot.com

Domin gyara,ko sharhi,sai a cike wanan akwatin tsokacin.wato,(commen box).ko Kuma ka aika sako Kai- tsaye izuwa 09035907765. ,,,
,A Nan  Kuma na ke cewa ; sai mun sake jamewa a darasi na gaba,,,

No comments:

Post a Comment