masarrafan da ke Wanan aiki , su ne kodoji guda biyu da huhu da kuma fata Hadi da mafitsara.kodojin, su ne su ke tace rarar ruwan da ke cikin jini , su ne kuma ke dai-daita kaurin jinin,wato su ne ke tace duk wani sinadarin da ya yi yawa a cikin jini, da kuma wanda jiki ya kare amfani da shi .kodojin su na yin Wanan aikin ne da taimakon wa'yansu kananun rariyoyi da ke can cikinsu a jere.
Yadda aikin ke gudana ya , shi ne , A Wasu lokutan; ,idan jini ya fito daga hanji , zai biyo ta hanta ne , a acikin wata babbar magudanar jini , bayan hanta ta kamalla bincike a kan sa, ta kuma dai-daita sinadaran da ya zo da su ,sai kawai ta antayashi izuwa ga kodoji,su Kuma Kodojin sun Riga, da sun san yawan ruwa da sinadaran da jiki ke bukata,.domin ai sinadaran madarar maganadisu wato,( hormones) sun Riga da sun baiwa Kodojin jadawalin yin aikin. To daga Nan kawai sai Kodojin su wanke jinin, su Kuma tace miyagun sinadaran da jiki ya Kare amfani da su .bayan sun kamallawa Wanan,sai Kuma su dai-daita kaurin jinin,dai-dai gwargwadon kaurin da jiki ke bukatarsa.daga nan sai su tura lafiyayyen jinin, izuwa ga wata babbar magudanar jini, da ke komawa izuwaga zuciya.sauran rarar ruwan,hade da tarkacen sinadaran guba da jiki ba ya bukata kmua ,kodojin ne za su Yi awon gaba da su, izuuwa ga wani kwararon, da ya hada Kodojin da mafitsara.inda a Nan ne ruwan wanke-wanken, za su Yi Dan zaman makoki na Dan wani lokaci ,kafin 'yan baya su riskesu,da da zarar mafitsarar ta ji abin ya Fara fin karfinta,sai kawai ta aika sakon korafinta izuwa ga kwakwalwa.cewa kayanan fa sun Dan taru ,harma su na so su rinjayi karfina.to a Nan take ita Kuma kwakwalwar, za ta Fara nanatamaka,da bukatar fitsari. inda a Nan take Kai kuma za ka antaya izuwa makewayi.
idan Kuma ka na cikin wani uziri ne,to za a baka 'yar kankanuwar damar dakatarda fitsarin ,sai a cigaba da baiwa mafitsara hakuri na Dan wani lokaci.da zarar damar fitar da fitsarin, ta samu, sai kawai ka gan sa ba kaukautawa.
A bangaren huhu Kuma ya na taimakawa ne wajen fitar da wacan iskar ta kabon Hadi da fitar da wa'yansu ruwan a yanayin tururi,ko Kuma ka ce suraci. A Wasu lokutan idan ka kula, za ka ga cewa idan ka shi ga wani muhalli, Mai sanyi sosai, ko Kuma a kasashe masu dusar kankara,zaka ga Wanan turiri ko hayakin ya na fitowa daga bakinka, yayin da ka ke magana,hakan ya na faruwa ne, kasancewar,iskar wajen a damsashe ta ke.
ita Kuma fata ,ta na fitar da wa'yanan ruwan ne a yanayin gumi .Wanda mu ke yi ,idan mu na cikin zafin Rana, ko kuma yayin da mu ke yin wani aikin karfi.kasancewar jikin Dan Adam kamar inji ya ke.,maimakon a goyamasa lagiroto da fanka a gadon bayansa ,domin rage Masa zafi.wanda a maimakon haka sai Allah cikin hikimarsa ya shimfidawa Dan Adam wata irin fata, Mai cike da hikima.ta na aiki ne ta yadda a duk lokacin da zafi ya doki mutum, sai kawai fatar ta yi wa kanta yayyafin ruwa, inda da zarar iska ta kada sai kawai ka ji jikinka ya yi sanyi,.daga Nan Kuma sai ka jika a yanayin, cancarancasss. kuma ai wa'yanan ruwan da su ka fito ta karkashin fatar a matsayin gumi, dama jiki ya Riga da ya Kare amfani dasu.ka ga kenan an rage wa mafitsara aikin ajjiye su, da Kuma yunkurin da ta ke Yi yayin da su ke bankwana da fitsarin.
ga Mai bukatar karanta Wanan darasin a harshen ingilishi sai ya ziyarci dayan shafinmu,ko Kuma ya shiga nan domin a rage Masa hanya.
Ga Mai neman Karin bayani Kuma,sai ya aika sakon kar-ta-kwana.ta Wanan lambar09035097765.
No comments:
Post a Comment