Thursday, December 27, 2018

Gabatarwa.

Da sunan Allah Mai rahama Mai Jinkai.
Yabo ya tabbatar ga Allah da manzonsa.

ina mai matukar farin ciki da lale-marhabin ga 
duk WandaYa samu damar ziyartar wanan shafin.Mai suna Kimiyya da hausa.
ko Kuma  ka ce kimiyya a hausance,a
 saukakakken harshe.
Na Gina wanan shafin ne Domin karatu da Kuma karantar
Da Dan abinda Allah ya sanar da ni a fannonin da suka shafi ilimin kimiyya,da ma wa'yansu fanonin daban.
Duba da yadda yarurruka irinsu Hindanci da sinanci ke
Kara samun ci gaba da habaka,a duniyar yau , ya sa  na ji na antaya izuwa duniyar kawazucin harshena .da kuma na tsaya kyam na yi nazari sai na ga cewa eh lallai ya kamata a ce idan da Hali , na Dan yi  wani Abu a Kai. Wanda  hakan ne  ya sa na
Ji cewa, Ya na da kyau a matsayina  na bahaushe ,na dan jarraba
bada tawa gudummuwar ko da kankanuwa ce ,tare da buri da kuma kwadayin  harshen nawa ya Kara samun habaka kamar sauran takwarorinsa.wanda hakan ya sa  na tambayi kaina da cewa, ta wace hanya kenan zan Yi hakan? Kuma ta Ina zan fara?.to a haka dai sai na ga cewa, ko dai zan Fara ne da  'yan rubuce-rubuce a fanonin da su ka shafi na'urar comfiyuta da ma  Wasu daga cikin ilmomin zamani, mussaman masu alaka da kimiyya,?.wato, ta amfanin  da yaren nawa. .domin kuwa a Dan karamin nazarin da na Yi ,a bisa manuniyar ci gaban harsunan duniya,na hakaito cewa duk wani harshe ko yare da  ya samu shahara a duniyar nan,to za ka samu cewa ya samu  nasarar ne a bisa  martabar da ya ke da ita a wajen al'umar duniya.  ita kuma martabar  harshe ya kan same ta ne a ma'unin zunzurutun alakantuwar sa da  rubuce-rubucen fannonin ilmomin da a ka yi amfani da shi wajen wallafa su.domin kuwa a bayyane ya ke cewa yaren ingilishi da larabci,da faransanci duk sun samu shahara da martaba ne a bisa manuniyar kasancewar ,su ne  yarurrukan da a ka fi yin amfani da su wajen wallafe-wallafen  daukacin ilmomin da Dan Adam ya mallaka a Wanan duniyar tamu. Kenan dai hakan kusan manuniya ce da ke nuna cewa ,iya sinkin-sinkin wallafe-wallafen da a ka Yi da harshe ne ke taimamakawa wanan yaren wajen  yaduwa da shahara a fadin duniya.wato ba adadin yawan masu magana da yaren ba.
To sai dai kuma hakan ba ya na nufin Wanan  ce kadai damar da harshe ke shahara ba ,wato da akwai wa'yansu hanyoyi ko damarmakin da a ke amfani da su wajen shaharantar da harshe. kadan daga cikin hanyoyin Kuwa, su ne kamar haka ;
1.fassarra.
2.rubuce-rubecen ilimi.( ta amfani da yaren.)

3.wake/waka.

4.wasan kwaikwayo.hadi da

 5 ..tafiye-tafiye.da Kuma 

6.harkallar cinikayya.

Sai dai a bayyane ya ke cewa ; Fassara ita ce mafi muhimmanci daga cikin Wa'yanan hanyoyin yadawa da habbaka harhse.kuma da ita ce na ke ganin ya kamata mu yi amfani  wajen nemawa namu yaren martaba a idon duniya.wato mu karfafamin zuciyoyinmu wajen kokarin  fassarrawa Hadi da wallafa Wasu daga cikin jerin sinki-sinkin ilimomin da a ka riga a ka wallafa da wa'yansu yarrurukan.wato mu  fassara su izuwa namu yaren.musaman ma na fannonin kimiyya. 
Wanda hakan Kuma, ba Abu ne mai wahala  ba,domin za kusan mu iya cewa ; kowacce rayyayar kalma da ke a cikin kamus din manhajar yarurrukan duniyar nan,idan ka bincika za ka samu cewa da akwai Wacce za ta Yi kusa ko ma dai-dai da ma'anarta a yaren hausa, ta yadda za ta iya maye gurbinta.
Kasancewar yaren namu ya na da yalwar kalmomi daidai gwargwado.sai dai rashin tattalin kalmomin yaren namu,  da Kuma  karancin bincike,da mu ke da shi kan sa mu ga kamar rashin yuwuwar hakan.domin ai idan ka duba tare da yin  nazari a Kai,za ka ga cewa,yaren hausa ya fi yaren sinanci ma'ana da saukin fahimta.amma jajircewar da masu yaren sinancin ke da ita, da Kuma shantakewar mu ne ya taimamakawa yaren sinancin wajen Dame namu yaren ya shanye.domin kuwa a halin yanzu miliyoyin amurikawa da jamusawa hadi  burtaniyawa ne ke zuwa   birnin sin(chana).domin koyo da nazarin yaren sinanci.wanda hakan kusan shi a ke kira da.(, reshe ya juye da mujiya). 
Abinda na ke kokarin bayyanawa a Nan shi ne; matukar mu na so mu daga  martabar yaren  namu, a idon duniya to lallai yin wani abu a Kai ya wajaba a gare mu,,wato  hubbasa wajen ganin an Fara koyarda ilimin fiziya da na likitanci a harshen hausa,ba ma a najeriyar kadai ba,har ma da daukacin kasashen afirika ta yamma,wato(West African countries).

Wanda samun nasarar yin hakan ne zai bai wa harshen namu damar shiga 
 lungu da sako na duniya  a san da zamansa.bugu-da-kari ,kuma hakan zai karawa malam bahaushe martaba a idon duniya.
A takaice dai ,in -so -samu- ne, za mu so a ce;  a na  amfani da harshen hausa a sauran  nahiyoyin gabasci da na yammacin duniya.
(Europe, Asia, Australia, north and south Americans continents)


ASALI.

A ra'ayin wa'yansu da ga cikin malaman falsafar harshe ,na yankin girka,(Greek); sukan ce ; " shi
Harshe ko yare; shi da kansa ne ya ke Gina kansa ,ma'ana,
ba sarakai ko malamai ne ke zaunawa cikin zaure su ce,"
daga yau; a Rika Kiran  kaza da suna kaza ba."a'a, a cewar su ,"kawai dai
 mu'amala da Abu yau da kullum ne da Kuma kamanni da 
yanayin wanan Abin ke sawa a ba wa wanan abin suna mai Kama da yanayinsa.
Sai dai hakan baya rushe cewa ,a Wasu lokutan,a kan kira taron kasa-da-kasa,domin tattauna wa'yansu al'amuran da su ka shafi yaren.wato a kan dai zauna jefi-jefi a tsakanin masana yaren, domin a kakkabawa yaren dokoki da kuma ka'idojin rubutu Hadi da  tantance wa'yansu kalmomin.(wanan a 'yan baya-bayanan kenan ba wai tun a farkon zamanin kafuuwar  yaren ba))

.( Idan mu ka je a darasinmu na gaba Mai taken: 

(KA'IDOJIN KARATU DA RUBUTU A HARSHEN HAUSA,)
za mu Yi bayani Mai Fadi. za Kuma mu fa'idantu sosai.


 A falsafance kuma Idan mu   ka dubi wanan maganar da ke cewa yare ko harshe shi da kansa ne ya ke Gina kansa, , za mu ga cewa; eh lallai  da akwai  Dan kamshin gaskiya a cikin maganar,musaman ma a harshen hausa.domin kuwa idan mu ka kalli wa'yansu kalmomin,tare da yin nazarinsu a falsafance
,za  mu ga  cewa eh lallai kamar ("biri ya Yi kama da mutum").misali kamar ka ce ;
,langa-langa,, laulayi, maloho , mazgewa ,hamago, santalele, karyewa,  botorami, kankamo, suburbuda, da dai sauransu. To Ka ga a nan idan a ka cire son Rai irin na Dan Adam, aKa kuma yi tsai aka yi nazarin
wa'yanan kalmomin, da ma sauran ire'iren su, za  mu  ga cewa ;eh lallai
Sun yi kama da abinda a ka siffanta su da shi. 

A bangaren daya Kuma , duk da
 cewar yaren hausa ba ya da harufa na kashin-kansa,  Wanda kuma  hakan ba
zai bada damar a kira Shi da gurgun yare ba.domin ai idan ka Ware yaren engilishi,da na sinanci da Hindanci da Kuma larabci,to a mafi yawancin yarrurukan da
Za ka ji ko za ka gani ,duk za ka samu cewa sun aro harufa ne a wa'yansu yarrurukan,sai Su ka yi wa harufan 'yar kwaskwarima,da nufin basaja.wato -kamar dai a
Yaren engilishi da faransanci,da Kuma yaren sinanci da japananci,haka-zalika,da yaren hindanci da urdanci.

to sai dai  Kuma a fasali da Zubi irin na siyasar duniya; shi aron  kalma ko  
harufa ,ba laifin ba ne a tsakanin al'umma.musamman ma idan da akwai 'yar wata harkakala ta kasuwanci ko kawance ko Kuma dangantakar addini 

Misalin  aron kalma shi ne; a duk sanda balarabe ya ji; bahaushe ya ce "aljani" to a nan take shi balaraben zai Gane cewa ai kalmar nan ce ta jinni, Wacce kakanin-kakaninsa,su ka kirkira Ko kuma,
suka gina shekara -da- shekaru.,sai ga shi yau wata
kabilar bakar fata , Wacce Babu dangin-iya-Balle-na- baba, ya zo ya sankami kalmar, ya
karye mata wuya da kafafu, ya murdata  domin  shigar da ita cikin 
Kundin jadawali,na manhajar yarensa.
to a Nan  gani kawai
za ka yi, balaraben Nan ya yi murmushi,ya kuma damalmale cikin farin ciki ,irin farincikin da Mai hoharas da Dan kwallo ke ji (coach) yayin da Dan kwallonsa ya Saka kwallo a raga..
Wato balaraben zai yi farin ciki ne ganin cewa harshensa ya zame Abin kwaikwayo,.
 Wanan shi a ke kira da aron kalma na gar-da-gar,domin ai shi mallam bahaushe bai iya nuku-nuku ,ba.to Amma bari ka ji shi gogan naka,,,"wa kenan?",bature Mana,,,"na gane,sai a kafta"...wato shi   mista kyam-kyam," a gimtse!!,ban gane ba,"wa ye musta kyamkyam Kuma?", ,,baturen Mana ,"da Kayau!! A kafta",,, "",,wato shi Mai jajayen kunnuwa,,"  a sake gimtsewa ,,,ni fa ban gane ba,,waye Mai jajayen kunnuwa kuma ?",,hallau dai baturen na ke nufi,",to yanzu Kam na gane,Dan haka  ci gaba kawai da antayo bayanai,ba kakkautawa ,wato a Yi ta antayo su ,ba gimtsewa ba kuma zuwa hutun rabin lokaci.
amma fa a gwari-gwari".

Ina Gaya maka cewa shi bature da ya ci karo da ayaba a wajen bulaguronsa  .,ya kuma duba a cikin kundin kamus din yarensa bai samu sunanta ba,sai kawai ya shiga lalube a  kundin kalmomin yaren larabci,sai kuwa ya same ta .to sai fai kasancewar mutumin naka ya na  da matukar wayo, wato a maimakom ya nema kalmar a larabci ya sankamota kai-tsaye izuwa cikin yarensa a matsayin aro,sai kawai ya ajjiya ta gefe, ya Fara neman sunan yatsun hannu a larabci,domin a hankalce ai yatsun hannu sun yi Kama da  zubin fasalin 'ya'yan ayaba. .sai kawai ya Fara binciken ya a ke Kiran   yatsun hannu a larabci,sai a ka ce masa  (al-ba-nan). A basajance sai kawai ya sankami wanan kalmar ta banan,wato sunan yatsu a larabci ya sankamawa ayabar,inda  ya maida ita banana,.Wanda hakan kenan dai manuniya ce da  ke nuna cewa yaren larabci shi ne gagara-badau a tarihance.

To dan haka ne dai 'yan-uwana hausawa na ke Mai Kira a gare mu, da cewa ;mu Kara karsashi da hubbasa wajen fadadawa hadi daidaita tsayuwar yarenmu, ta yadda zai zamo,zakaran-gwajin-dafi,a cikin harsunan wanan duniyar tamu.
A karo na biyu Kuma wato  a jaddadance na ke kara janyo hankalinmu izuwa ga Wa'yanan hanyoyin , da za su taimaka wajen karawa yaren namu karsashi.wato , su ne dai kamar haka.

1).mu Rika amfani da inganaciyar hausa,wajen rubuce-rubucenmu, na yau-da-kullum, da ma wajen magana..

2).mu yawaita nazari da bincike tare da kokarin kirkiro sababbin kalmomin da za su iya maye gurbin wa'yansu daga cikin kalmomin da mu ka aro daga wa'yansu yarrurukan.
wanda yin hakan Kuma zai  karawa harshen namu fadi da karsashi .wata falallar yin hakan a nan  ita ce; a hukumance ba a biyan harajinl na adadin kalmomin da yare ya mallaka,Wanda kuma hakan a wani kaulin,  manuniya ce da ke nuna cewa ba a fitar musu da zakka ko wakafi.


3).Mu rinka cike dokoki da ka'idojin rubutu ,a rubuce-rubucenmu na yau- da-kullum,.
wato kada  mu bada dama ko taimamakawa wajen a keta-hadin yarenmu,Wanda hakan kusan daidai ya ke da in ce; kada mu bada dama har a samu damar assassa  karyayyar hausa,wato kamar yadda al'umar kudancin najeriya su ka assasa karyayyen ingilishi wato (broken engilish).

4).mu kuma Rika nanatawa da Jan hankali izuwa ga hukumomin da abin ya shafa, kan cewa  a rika maimaita kokarin Nan na jarraba maida tsarin koyar da daukacin ilimomi a yarenmu na uwa, wato hausa.idan  Kuma hakan zai Dan-tada kura ,to sai a Rika karantarwar da dukan yarukan biyu, a lokuta mabanbanta, ,domin yin hakan zai yi matukar saukaka wa yara fahimtar ilimin da a ke so su fahimta a cikin sauki.
Wato ba  lallai sai a tsohuwar turbar da turawan mulkin-mallaka su ka bar mana ba.
domin ai su turawan sun yi hakan ne domin cigaban yarensu da Kuma al'adunsu.kuma ai idan ka duba a kasashe masu tasowa,kamar Hindu,(India).za ka ga cewa da mu da su kasa daya ce ta mulkemu ,wato burtaniya.
 to Amma saboda tsananin kishin kasar su da kuma harshensu da su ke Yi ne,ya sa su ka yi kokarin fassarawa hadi da taskance dukan  fannonin ilimomin da ke da amfani ga rayuwar Dan Adam ,su ka maida su da yarensu na hindanci, wanda samun damar yin hakan ne da su ka Yi,ya  taimakawa kasar tasu wajen cika -da-batsewa a fannonin ilimimomi,mussaman a bangaren kiyon lafiya.
sai dai Kuma hakan ba daidai ya ke da cewa  ba a koyarda karatu da yaren turanci a indiya ba,a'a ,sukan yi hakan domin nishadi. 
Wato hakan daidai ya ke cewa ; ba'indiyen kirki yakan koyi turanci ne domin gudanar da harkallolin Kasusuwanci a ciki da wajen indiya.ba wai domin ya Yi tinkaho da ya iya turanci ba.domin kuwa rinjayen da su ke ba yarensu ne ya sa duk yadda ba'indiye ya shahara wajen iya furta kalaman turanci,da zarar ya Yi turancin za ka gane cewa lallai shi ba'indiye ne.domin akwai kalaman da yarensa na uwa ya Riga da kwace wa harshensa ragamar alhakin furta su.

I ta ma dai  kasar sin wato (chana) da kusan irin Wanan dabarar ta yi amfani wajen inganta kirkire-kirkirenta na kimiyya da fasaha. 
A taikaice dai kusan za mu iya cewa ; duk wata kasa ko al'umar da ka ga ta samu ci gaba,to za ka samu cewa hakan na da nasaba da martabar harshenta, da Kuma baiwa ilimi muhimmanci da al'ummar ke Yi.inda za ka ga cewa tunani da burin gama-garin 'yan kasar da masu mulkin kasar ; shi ne ; TA YAYA ZA A YI KASA GABADAYA TA CI GABA.

Kenan dai mu ma a kasarmu ta najeriyar idan ya kasance cewa;
 mu gama-garin 'yan kasa mu  ka canja kidan,ta hantar baiwa ilimi muhimmanci, to su ma shuwagabanin namu dole ne su canza rawar.
wanda hakan zai ba kasar tamu damar tafiya kafada-da-kafada da wa'yancan takwarorin nata. 
A takaice dai ya na da kyau mu gano  cewa a cikin jerin jadawalin matattakalar cigaban al'umma, ilimi ne kan gaba,ba yawan jam'iyun siyasa  ko adadin al'umar kasar ba.
wato bai kamata mu matasa mu rinka auna gobenmu a ma'unin turbar  shugabaci ko yin arziki a dare daya  ba.
 A saukakkaken harshe hakan na ishara ne da cewa; mu rage bibiyar nasara  kai-tsaye,wato mu fara neman kwarewa da gogewa a wa'yansu fannonin Rayuwar daban-daban.domin idan mu ka ce za mu rinka bibiyar   nasarar kai-tsaye , Kuma a gudane.to faa ,ba za ta bari mu riske ta  cikin sauki ba.amma idan mu ka jajirce muka nemi kwarewa ta wani fanin, to ita nasarar ce da kanta za ta antayo izuwa gare mu.daga nan kuma sai cimma buri  ya kawo kansa izuwa garemu.
Domin da yawa za ka samu cewa  jajirttacin mutane  da dama,a kasashe daban-daban ,ba wai da jadawalin karatun da su kayi a jami'o'i ne kan sa a Basu shaidar darajar karatun dakta ko cansilo ba,.kawai dai ita jami'ar ce da kanta ke yin nazari a bisa fafutukarka a rayuwa,sai tl kawai ta Kira ka ta martaba ka a bisa jajircewar ka wajen ganin ka kawowa kasa ko al'umar ci gaba.
Daga cikin wa'yansu ma za ka samu cewa ba su taba halartar makarantar boko ba,Amma a bisa kyakykyawar zuciyarsu da Kuma kishin a'umarsu da su ke da shi,sai ka ga an Gina jami'a kacokan an  rattaba Mata sunansu.

  wato dai  ita rayuwar Nan kamar ginin bene ce ,shi Kuma bene a mahangar hankali da hangen nesa,zai fi kyau ka jajirce ka nemi hawansa ta mattatakala wato ba ta mahaya ba,(lifter),domin a Wasu lokutan mahar kan iya lalacewa a wani matakin da ba-ka-kasa-ba-ka-sama,Wanda a wani kaulin za mu iya Kiran hakan da tsaka-mai-wuya.daga Nan Kuma saiii...ta Allah
A dayan bangaren Kuma wato idan ka Yi aiki tukuru ka Kuma jajirce ka hayo ta mattatakalar benen ,to lallai ka na da kwarin guiwar cewa: komai daren-dadewa za ka cimma gaci ,a bisa lamuncewar UBANGIJi..

(,,,Amma fa duk wanan 'yar karamar falsafata ce,,,)

 A takaice dai matsalar kasarmu ta najeriya, ba ilimin ne ba mu da kwakwalwar daukar sa ba,a,a. Domin Kuwa a maimakon haka, Kusan za a iya cewa duk wani ilimin Kimiyya da fasahar da ke duniyar nan, za ka iya samun sa kwance a daskare, ya na ta hutawa abinsa a cikin kwakwalwar dai-daikun mu,.sai dai  kasa-a-guiwa da mu ke Yi wajen yadawa da wallafa wanan ilimin izuwa ga sauran al'umar,wanda kuma hakan ne kan zamo sanadiyar rashin morar wanan ilimin.

Wato idan da a ce sinki-sinkin darussan  ilimin da kowannenmu ya fi kaware ne ya ke dabbakawa   tare da yadawa a shafukanmu na yanar gizo da Kuma shafukanmu na sada zumunta,wato a maimakon hotuna da labaran kintacen abin kunyar da wani ya aikata, da mu ke yadawa,to da yanzu an wuce gurin.
domin ai karantarwa tsakanin dalibi da dalibi ta fi inganci fiye da ta malami da dalibi."dalili?",, Dalili shi ne, ai shi dalibi Dan uwanka nee matakin hankali, wanda hakan manuniya ce da ke nu na cewa; za a iya samu cewa kaifin hakaitowa da budewar kwakwalwarku kusan su iya kasancewar a zango da ya .
amma a tsakanin malami da dalibi , za  ka samu cewa da akwai rata mai dan tsawo .kenan dalibi dan uwanka ne zai iya yi maka bayani tiryan-tiryan a irin yaren da za ka fi fahinta ,wato a saukakkaken harshe.

KAMMALAWA.

 A takaice dai 'yan'uwa,  Kira na a gare mu shi ne ; mu maida shafukan sada zumuntarmu su zamo mana makarantunmu.,,, A Nan na ke cewa,,, "a kafta,,,,,

Ga Mai bukatar cancare darussan da ke tafe ,wato ga Mai sha'war karanta wa'yanan darusan da ke  wanan shafin,a harshen turanci ; sai ya antaya  izuwa Wanan adireshin;
www.simplegeneralscience.blogspot.comwww.simplegeneralscience.blogspot.com
ALLah ya sa mu Dace.ameen

Domin neman Karin bayani ko sharhi ,sai a tattaro su a sankama su a cikin akwatin sharhin da ke kasan kowanne darasi.
Ko Kuma a aikace sako izuwa 09035907765.


.

Wednesday, December 26, 2018

(1).KA'IDOJIN KARATU DA RUBUTU A HARSHEN HAUSA.

KA'IDOJIN KARATU DA RUBUTU A HARSHEN HAUSA.

MATASHIYAR FARKO.

Kasancewar tun kafin yanzun ina mai lura da kura-kuran da muke ta tafkawa a wajen rubuce-rubucen da mu ke Yi a  harshen  Hausa. Na lura da hakan ne a sakamakon karance-karancen mukalolin da na ke karantawa da ake rubuta a  harshen Hausa, da Kuma littattafan Hausa, da littattafan hikayoyin da aka rubuta cikin harshen namu na Hausa, da Kuma sakunan sharhi da  tambayoyi da a ke rubuto mini, kai har ma da rubuce-rubucen da ake yi a jikin motocin hawa, irin su manya motoci, kamar rokoki, Daf-Daf da dangoginsu, har ma izuwa mashina da kekuna da muke hawa. Na sake lura da wa'yansu kura-kuran da mu ke yi a rubuce-rubucen da mu ke yi a gaban shagunanmu domin talla, da kuma rubuce-rubucen da mu ke yi a jikin allunan kan hanya,wato (billboard).

MATASHIYA TA BIYU.

Hallau dai
            Kusa-kuran sun hada da harhade kalmomi a wajen da ba a nan a ake hadawa ba, da kuma raba kalmomin a wajen da ba a Nan ake rabawa ba, wato (Word margins and divisions), da kuma rubuta kalmomin da su ka kunshi bakake iri daban-daban, wanda a ka’ida ba a haka ya kamata su zo a rubutu ba, da kuma cusa kalmomi ba a muhallin su ba, wani lokaci kuma rashin amfani da alamomin rubutu (Orthography) a wajen da suka dace, ko kuma rashin amfani da su ma kwata-kwata da mu KE yi, da dai sauran matsalolin da kan Iya zamewa barazana wajen keta-hadin yarenmu namu.

MATASHIYA TA UKU.

     kasancewar faruwar hakan na da alaka da  cewa ba asalin Hausawa ne, su ka fitar da Manhaja ko Jadawalin rubutun Hausa ba. Domin Idan mu ka koma a can tarihin baya , za mu tarar cewa irin su Farfesa Neil Skinner, wato Daraktan Hukumar NORLA da George Percy Bargery, Mawallafin Kamusun Hausa da Hanns Vischer, wanda ake kira Dan Hausa da Dokta R. M. East, Shugaban Hukumar Talifi da Mista. L. C. Giles, Editan farko Bature na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da sauransu, su ne suka fitar da yadda za a yi rubutun Hausa. Kasancewar kuma su ba Hausawa ba ne, bugu-da-kari kuma ,ba su san furucin Hausa da kuma kalmomin hausar sosai ba.wanda hakan ne ya sanya ,rubutun Hausa ya taso cikin hajijiya da kuma rudani, wanda ya janyo har izuwa yanzu mu ke ta tafka kura-kurai, a rubuce-rubucenmu. , Wanda kuma hakan ne ya janyo yaren namu   ke ta tafiya da dingishi, face wa'yansu Daga cikin malamanmu da kuma dalibai iri na da ke tashi tsaye, don neman fahimtar yaya ka’idojin rubutun Hausar su ke kafin su yi rubutun Hausar.

MATASHIYA TA HUDU.

      To a baya-bayanan Nan dai da a ka ga cewa  matsaloli sun cunkushe rubutun Hausar, sai aka Fara shirya manyan tarrurrukan kasa-da-kasa,inda izuwa yanzun da na ke wanan rubutun.(15-02-2019)  an samu damar gudanar da  manyan taruka guda uku.an Yi su ne Kuma , domin daidaita KA’IDOJIN KARATU DA RUBUTU a HARSHEN hausa. Taron farko an yi shi ne, a Birnin Bamako da ke kasar Mali, daga 28, ga watan Fabrairu, zuwa 5, ga watan Maris a shekara ta 1966. Taro na biyu kuma an gudanar da shi ne, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a ranar 21, ga watan Yuni a shekarar 1970, sai kuma na ukun da aka yi a Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, a cikin Jami’ar Bayero da ke Kano, a watan Satumbar shekarar 1972. A cikin wadannan tarurrukan an yi gyare-gyare wa littafin nan na'yanttatun kalmomin Hausa wato (hausa Spellings book’,)Wanda shi ne littafin da turawa suka dora mu a kansa domin yin rubutu a HARSHEN hausa, wanda kuma shi ke dauke da Manhaja da Jadawalin rubutun Hausa.

MATASHIYA TA BIYAR.

            Sai dai duk da gyare-gyaren da aka yi wa ka’idojin rubutun da kuma kalmomin Hausa, sai ya zamanto duk da hakan dai tsugune-ba-ta-kare ba, wato ba-a-rabu-da-Bukar-ba-an-haifi-abu, inda al’amarin ya koma ana kukan targade sai ga karaya, domin an dada rikita mutane ne, wanda ya sa a rubutu guda sai ka ga ana amfani da tsohuwar ka’ida da kuma sabuwar ka’ida a wake daya.
To Haka dai abubuwa suka yi ta tafiya a kudundune, ba tare da kuma an samu mafita ba, wannan matsalar ta ci gaba da ci-wa-masana ilmin harshen Hausa tuwo-a-kwarya. Da dai tura ta kai bango ne, ganin ruwa yana neman karewa dan kada bai gama wanka ba, ma’ana ganin rubutu cikin harshen Hausa na neman ya ci tura, sai masana ilmin harshe na kasar Jamhuriyar  Nijar suka gayyaci takwarorinsu na Najeriya, inda a nan suka shirya wani gagarumin taro a birnin Yamai, a Cibiyar Harshe da Tarihi ta Sarrafa Adabin Baka Wacce  a Turance a ke kira da (Centre for Linguistic and Historical Studies by Oral Traditions ), a karkashin jagorancin Majalisar Hadin Kan Afirka (OAU), wanda yanzu ta
dawo Tarayyar Afrika (AU), an yi taron ne tun daga ranar 7 zuwa 12 ga watan Janairu, a shekarar 1980.
Daga farko sun daidaita kawunansu a Bakake da Wasulla da Auren Wasulla da kuma Tagwan Bakake, kana daga bisani suka daidaita ka’idojin rubuta kalmomi.

KAFCEE.

            Ga abubuwan da suka zayyana kamar haka:

BAKAKE.
Bakake na nufin harufa.

Bakaken da aka yarda da su a rubutun hausa, su ne Kamar haka.

KANANA: b, b’(mai lankwasa), c, d, d’ (mai lankwasa), f, g, h, j, k, k’(mai lankwasa), l, m, n, r, s, t, w, y, ’y, z

MANYA:   B, B’ (mai lankwasa), C, D, ‘D (mai lankwasa), F, G, H, J, K, K’ (mai lankwasa), L, M, N, R, S, T, W, Y, ’Y, Z

WASULLA

KANANA: a, e, i, o, u
MANYA:  A, E, I, O, U

AUREN WASULLA

KANANA: ai        au         maimakon      ay      aw
MANYA:   AI      AU       maimakon       AY    AW

TAGWAN BAKAKE.
tagwayen bakake na nufin,hade harufa biyu domin Samar da wani sautin furuci a harshen hausa.

KANANA:  fy, gw, gy, kw, ky, kw(mai lankwasa), ky (mai lankwasa), sh, ts

MANYA:    FY, GW, GY, KW, KY, KW (mai lankwasa), KY (mai lankwasa), SH, TS

KA’IDOJIN RUBUTA KALMOMI

Da suka dawo ka’idojin rubuta kalmomi kuma, sun fito da dokoki goma sha uku (13).

Ga ka’idojin rubuta kalmomin da aka fitar a taron da aka yi a kasar Nijar kamar haka:-

 (1). MANYA  BAKAKE

Wannan ya kasu kashi biyu ne:

(1a). Duk jimloli suna farawa da manya baki.
Misali: Gobe zan je kasuwa.
            Jiya na ci tuwo.
(1b). A rubuta manyan bakake a farkon zanannun kuma sunayen yankan na mutane da kuma na takamaimun wurare.
Misalin sunan yanka a mutane shi ne
Sunayen mutane:  Adamu, Shamsiyya, Haruna, Mahmud.
Sunayen wurare: Jami’ar Maiduguri, Asibitin Murtala, Bauchi, Kano.

(2). Ba a yarda a yi amfani da bakin P a rubutun Hausa ba , sai dai F. Amma  za a iya amfani da P a cikin zanannun sunaye kamar haka:
 Palasdinu       ba        Falasdinu      ba.
 Paris               ba       Faris              ba.
 Sipikin           ba        Sifikin           ba.
 Mustapha      ba        Mustafa      ba.
Amma za a iya rubuta harafin P idan ta zo cikin Kalmar amsa-kama, kana sun amince a rubata Fensiri  da Panko, maimakon Pensiri da Panko

(3). Ana amfani da wadannan ka’idojin wajen rubuta bakaken M ko na N.
(3i). A yi amfani da M a tsakiyar kalma, idan bakin B, B (mai lankwasa), F, ko da harafin M ne yake gaban M din, a rubuta M, misali:

(a). Tambaya        ba             Tanbaya             ba.
      Jimbiri           ba                 Jinbiri               ba.
      Gammo           ba              Ganmo               ba.
   
(b). Amma a rubuta N a sauran muhallai, misali:
     Gansheka         ba Gamsheka            ba.

     Gungume        ba           Gumgume            ba.

     Ganzaki           ba           Gamzaki              ba.

     Tuntube          ba          Tumtube               ba.

     Kanwa            ba          Kamwa                 ba.

(c). Ana rubuta N a karshen kalmomi, ko da kalmomin da ke gaba sun fara ne da bakaken                 B, B (mai lankwasa), F, ko M, misali:
   Gidan Bala                 ba                    Gidam Bala                   ba.

   Ramin  bera                ba                    Ramim bera                   ba.

   An fasa                       ba                    Am fasa             ba.

   Sabon maho               ba                    Sabom  maho                ba.

(d). Idan kalma tana karewa da M ne a karshen ta ,sai a rubuta M din:
       Malam Ali  ba        Malan Ali                      ba.

       Kullum                   ba        kullun               ba.

      Mutum daya            ba        Mutun daya       ba.

(e). Kalmomin amsa-kama masu karewa da M, sai a rubuta M din:
     Jimgim         ba        Jingin                ba.

     Sukutum      ba        Sukutun ba.

     Kundum      ba        Kundun             ba.
(4). Bakaken nasaba da  na mallaka.
     (1).Bakaken nasaba, watau da N da R, ba sa sajewa da bakaken da ke gabansu:
       (a)   Sarkin makafi  ba        Sarkim makafi               ba.

              Akwatin fata                ba       akwatim fata                 ba.

              Sarkin fada                  ba       Sarkim fada                   ba.

              Sarkin baka                 ba       Sarkin baka                   ba.

       (b)  Ranar dariya                 ba        Ranad dariya                 ba.

             Ranar kuka                   ba        Ranak kuka                   ba.

             Ranar tashi                    ba        Ranat tashi                     ba.

   (2). Bakaken mallaka, watau N da R ba sa sajewa da bakaken da ke gaba da su.
        (a). Gonakinmu                  ba        Gonakimmu                   ba.

              Rigunanmu                   ba        Rigunammu                    ba.

              Matanmu                     ba        Matammu                      ba.
   

       (b). Gonarmu                      ba        Gonammu                      ba.

             Rigarmu                        ba        Rigammu                       ba.

            Motarmu                       ba        Motammu                     ba.

(5). Bakin R mai zuwa karshen fi’ilan haddasau ba ya sajewa da bakin da ke biye da shi, misali:
  (a). Mayar da shi.                    ba        Mayad da shi                ba.

        Sayar masa da shi.             ba        Sayam masa da shi        ba

        Mayar wa Ali shi.  ba        Mayaw wa Ali shi          ba.

(b). Motar da ka shiga.            ba        Motad da ka shiga         ba

        Sakar da ta yanke             ba        Sakad da ta yanke         ba.

        Hular da ya karba              ba        Hulad da ya karba         ba.

(6). Ana rubuta karan-dori wajen rubuta tagwan kalma:
       Fadi-tashi               ba        Fadi tashi                       ba.

       Kwan-gaba            ba        Kwan gaba                    ba.

       Bar-ni-da-mugu,     ba        Bar ni da mugu  ba.
(7). Ana rubuta kalmomin jam’u a hade kamar haka:
       Komai                    ba                    Ko mai              ba.

      Kowa                      ba                    Ko wa               ba.

      Ko’ina                     ba                    Ko ina               ba.

      Koyaushe                ba                    Ko yaushe         ba.

      Kowanne                ba                    ko wane           ba.

      Kowane                  ba                    Ko  wane          ba.

      Kowadanne ba                    Ko wadanne      ba.

(8). Ana rubuta wadannan zagagen fi’ilan a hade:
    (a). Yakan     rubuta               ba       Ya kan              rubuta               ba.

          Takan          “                   ba        Ta kan                   “                   ba.

          Nakan         “                   ba        Na kan                   “                  ba.

          Mukan        “                   ba        Mu kan                  “                  ba.

          Kukan          “                  ba        Ku kan                   “                  ba.

          Sukan          “                  ba        Ku kan                   “                  ba.

          Kikan           “                  ba        Ki kan                    “                  ba.

          Kakan          “                  ba        Ka kan                  “                   ba.

          Akan            “                  ba        A kan                    “                   ba.
 

(b). Yana       rubutawa          ba        Ya na                rubutawa          ba.

          Tana              “                 ba        Ta na                       “                 ba.

          Ina                “                 ba        I na                        “                 ba.

         Muna             “                 ba        Mu na                     “                 ba.

         Kuna              “                 ba        Ku na                      “                 ba.

         Suna              “                 ba        Su na                      “                 ba.

         Kina               “                 ba        Ki na                       “                 ba.

         Kana              “                 ba        Ka na                      “                 ba.

         Ana                “                 ba        A na                        “                 ba

(c).  Yake        rubutawa          ba        Ya ke                rubutawa          ba.

         Take               “                 ba        Ta ke                        “                ba.

          Nake             “                 ba        Na ke                       “                ba.

          Muke            “                 ba        Mu ke                      “                ba.

          Kuke             “                 ba        Ku ke                       “                ba.

          Suke             “                 ba        Su ke                       “                ba.

          Kike              “                 ba        Ki ke                        “                ba.

         Kake             “                  ba        Ka ke                       “                ba.

         Ake               ”                  ba        A ke                        “                ba.

(d). Ana so kuma a rubuta kamar haka:-
      Ta       rubuta.
        Mun        “
        Kun         “   
        Kin          “   
        Ka          “   
        Sun         “   
        Ya           “ 
        An           “
                                 
(9).  Zagagen fi’ili masu nuna lokaci mai zuwa ana rubuta su ne: Kamar haka:
       Zai           tafi.

      Zan          tafi .

       Za mu      tafi        ba        Zamu    tafi        ba.

       Za ku        tafi        ba        Zaku     tafi        ba.

       Za su         tafi        ba        Zasu      tafi        ba.

       Za ki         tafi        ba        Zaki      tafi        ba.

       Za ka        tafi        ba        Zaka     tafi        ba.

       Za a          tafi        ba        Za’a      tafi        ba.

(10). Ana rubuta kalmomi masu ma’ana a wawware cikin jimla:
Misali Kamar ka ce:
        Ya sa ni in ba ka kudi.

         Abin da ya sa ya fi shi cancanta shi ne…..
        Na tsai da kai don mu yi kallon tare. Ka ga a Nan za ka ga cewa kowacce warrariyyar kalmar, a cikin su, za ta iya cin gashin kanta,woto za ta iya bada ma'ana.

(11)(a) Ana rubuta abin malllaka hade da gajeriyar kalmar mallaka:
           Dokina               ba        Doki     na         ba.

           Rigarsa               ba        Rigar     sa         ba.

          Zanenta               ba        Zanen    ta         ba.

     (b) A na rubuta abin mallaka daban, kuma doguwar kalmar mallaka daban:
Misali::
      Wani  doki  nawa                ba        Wani dokinawa ba.

      Wata riga tawa                    ba        Wata rigatawa               ba.

       Wani zane nata                   ba        Wani zanenata               ba.

(12) Ba a hade wakilin-suna mafa’uli da kowace kalma:
       Ya ba ni                ba        Ya bani                         ba.

       Mun sa shi, ba        Mun sashi                      ba.

       Ana kiran ka          ba        Ana       kiranka             ba.

(13) sannan ana rubuta
        Saboda                ba        Sabo     da                    ba.

        Watakila               ba        Wata kila                       ba.

Bayan sun fitar da wadannan ka’idojin rubutun kalmomi ne, suka sake fito da wasu ka’idoji da ya kamata abi wajen rubuta wa'yannan: kalmomom.Kamar haka:

Shi ne                ba        shine                ba.

Ita ce                ba        Itace                 ba.

Mu ne               ba        Mune                ba.

Kai ne               ba        Kaine                ba.

Ke ce                ba        Kece                 ba.

Su ne                ba        Sune                 ba.

Ku ne                ba        Kune                 ba.

Ni ne                 ba        Nine                  ba.

(2) haka a rubuta: Wa'yanan kalmomin kamar haka:

Ya yi            ba        Yayi                  ba.

Ya ci             ba       Yaci                  ba.

Ya tafi           ba           Ya tafi               ba.

 Ya je             ba       Yaje                  ba.

 Ya fi              ba       Yafi                   ba.

  Ya ki             ba       Yaki                  ba.

   Ta ki              ba       Taki                   ba.

   Ta yi             ba       Tayi                   ba.

Idan muka dawo a bangaren ka’idoji ko alamomin rubutu Kuma wato (orthography), nan ma na dan hakaito wa'yansu 'yan kura-kurai da mu ke antayawa. Wanda Lura da hakan ne ya sa na dan yi takaitaccen fashin baki a kan yadda ake amfani da alamomin rubutu, wajen rubutu  a cikin harshen Hausa.

(1). AYA (Full Stop) (.)
            Ana amfani da aya a rubutu wajen da ake bukatar cikakkiyar tsayawa, ko saukar da  numfashi gaba daya. Idan har an yi aya a rubutu, to wata jimla ko zance ko magana mai zaman kanta ce za a shiga, ko kuma rubutu ya kare. Bayan Aya in har za a ci gaba da rubutu, to da babban baki ake fara rubutun, misali:
     (1). Idris ya ci abinci ya koshi. Da yammaci kuma sai ya tafi rafi debo ruwa.
    (2). Shamsiyya ta tafi kasuwa.
A jimla ta biyu an nuna jimla ta riga ta kare, wanda hakan ne ma ya sa aka yi Aya a rubutun. Ana kuma amfani da Aya wajen takaita zance, misali, kamar :Mal. A. Shehu maimakon Malam Adamu Shehu.

(2). WAKAFI (COMMA) (,).
            Ana amfani da wakafi a rubutu wajen da ake bukatar ‘yar karamar dakatawa ko saukar da numfashi kadan. Bayan an yi wakafi a rubutu karamin baki ne yake biyo baya, kasancewar an dan hutar da mai karatu ne, don ya samu ya daidaita numfashinsa; domin karutan ya yi masa ma’ana da kuma dadi. Misali:
(a)    Musa ya tafi kasuwa dazu-dazu, don ya sayo yadin sallarsa. Ka ga an bayyana Musa ya tafi kasuwa, sannan sai aka yi wakafi, don a hutasar da mai karatu, daga bisani kuma aka karasa rubutun  da cewa ‘don ya sayo yadin sallarsa.’

(3). ALAMAR TAMBAYA (QUESTION MARK) (?).
            Wannan tana daga cikin ka’idojin rubutu, masu matukar amfani a rubutu, domin tana bambance ma’anar jimla, zance ko magana, inda take nuni da tambaya aka  yi, ba wai zance ko bada labari ba wato (statement). Ma’ana, ana kore wa mai saurare ko mai karatu tantama. A taikaice dai a duk inda aka yi alamar tambaya, to ana ja , wato madda yayin karantawa. Haka shi ma mai karantawa ana so ya ja yayin karantawar.

Misali:
            (1) Maryam ta je asibiti jiya.    Zance (Statement).

Amma idan ka ce:
            (2) Maryam ta je asibiti jiya ?  Tambaya (Interrogation).

A falsafance
Jimla ta farko ta nuna cewa da Maryam ta riga da ta je asibiti jiya. Amma sakamakon alamar tambaya da aka yi a jimla ta biyu, sai  ma’anar ta canza, inda ake tambayar ko Maryam ta je asibiti jiya?.
            Babban baki ne yake zuwa bayan an yi alamar tambaya a rubutu. Misali:
(a). Yaushe rabon duniyar siyasar kasar nan da ayyeyare ? Ina jin tun lokacin jamhuriya ta farko, hana rantsuwa zuwa farkon jamhuriya ta biyu.

(4). ALAMAR MOTSIN  RAI (EXCLAMATION MARK) (!).
            Ana amfani da alamar motsin rai, wajen sanar da mai karatu wani abu na takaici, tsoro, kaduwa, mamaki da sauransu. Misali:
            (a). Wayyo Allahna !
            (b). Ah ! Ya kashe ni.
            (c). Oh ! Abin da mamaki, dan akuya da wanke-wanke.
            (d). Ya cire min ido !
            Bayan an yi alamar motsin rai a rubutu, babban baki ne, yake biyo baya in har za a ci gaba da rubutu. Misali:
            Ah ! Na shiga uku, na lalace.
            Das ! Gabansa ya buga.
            Zambur ! Ta mike kamar wacce aka tsikara da tsinin mashi.
            Sun yi masa caa ! Kasuwar kuda.

(5). BAKA BIYU (BRACKET OR PARENTHESIS) ( ).

            Ana amfani da baka biyu a rubutu wajen karin bayani ga mai karatu, wato kara fito da ma’anar me ake nufi a zance, jimla ko maganar da aka yi.
            (a). Da sanyi safiya Abubakar ya bar jiharsa (Bauci).  Ka ga an ji Abubakar ya bar jiharsa, to amma wani zai so ya ji ina ne jihar Abubakar, amma da aka sa a cikin baka biyu, sai ya gamsar da mai karatu.
            (b). Sai a watan Satumbar  shekara ta 1927, aka samu wani basudane (dan kasar Sudan) da ya fitar da mutane daga duhun jahilci..
          HAka-zalika   Ana amfani da baka biyu, wajen sakaye wani batu da bai danganci rubutun da ake yi ba. Misali, ana rubutu cikin harshen Hausa, sai wata kalma ta shigo, ba ta Hausa ba, ko kuma an fadi ma’anarta da Hausa, amma kuma an fi saninta da Turanci, ko kuma dai ana so a santa cikin harshen Turanci, to sai a sanya ta cikin baka biyu. Misali,
            Amina ta dafa miyar tumatir (stew) da safe. Ka ga wani idan ya ji an ce, an yi miyar tumatir, abin zai dan ba shi mamaki, amma kuma kasancewar an sa Kalmar stew, cikin baka-biyu, kuma dama an fi sanin miyar tumatir din da sunan  stew, sai ya zamanto an fi fahimtar jimlar.
            Ana amfani da baka biyu wajen sakaye takaitattun harrufa. Misali,  Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Babban Bankin Najeriya (CBN).
            Yayin da ake amfani da baka biyu, wakafi, alamar tambaya ko aya duk za su iya biyowa baya.sai dai Kuma, ya danganci yaya jimlar, zancen ko maganar ta ginu. Misali:kamar;
            (1). Amina ta dafa miyar tumatir (stew), da sanyin safiya.      (wakafi)
            (2). Bafarawa ya bar biliyoyin Nairori a baitul-malin jiharsa (Sakkwato).     (aya)
            (3). Kana ganin zai iya rabuwa da ita (motarsa) ?         (alamar tambaya).
       Bakin da ke biyo baya, bayan an yi baka biyu a rubutu ya dangancin da wane daga cikin ka’idojin rubutu aka yi amfani. Idan wakafi ne aka sankama bayan Bayan baka-biyun. to karamin baki ne zai biyo baya. Idan kuma aya ko alamar tambaya ce, sai babban baki ya biyo bayan baka biyun.

(6) KARAN-DORI (DASH) (-).
            Ana amfani da karan-dori a rubutu, wajen rubuta tagwan kalmomi, misali,
            (1). Ahmad yana ta safa-da-marwa a dakinsa.
            (2). Shamsiyya ta tsaya kai-da-fata, domin ganin ta samu nasarar cin jarrabawarta.
            (3). Hassan yana ta fadi-tashi don ganin ya ci zabe.
            Akan Kuma yi amfani da karan-dori wajen hada kalma da kalma, misali, kamar ka ce kaka-tsara-kaka, tana-kasa-tana-dabo, sa-toka-sa-katsi. Idan bayan an yi amfani da karan-dori a karshen rubutu , aya ce take ke zuwa, idan kuma ba a karshen rubutu ya zo ba , wakafi ne ke zuwa. Misali:
           (1). Siyasar kasar nan, tana-kasa-tana-dabo.
           (2). Tana-kasa-tana-dabo, damben Shago da Namadi.
            Wani lokaci ko da an yi amfani da karan-dori, babban baki na iya biyowa baya, misali, wajen rubuta suna mai dauke da  Al:  Al-Mustapha, Al-Amin da sauransu. Haka zalika, ana amfani da karan-dori wajen nuna zancen wani musamman ma wajen aikin jarida, misali: Kungiyarmu ta dukufa wajen kare hakkin dan Adam - Alhaji Umaru Ahmed. Wannan karan-dorin da ya zo shi ya nuna cewa zancen wani ne. Har ila yau, ana amfani da karan-dori wajen danganta wasu batutuwa, misali: shekara 50-60, ko daga 1990-1999, awa 20-30, tarihin dandalin a daidaita sahu 2004-2009, da sauransu.

(7). RUWA BIYU (COLON) (:).
            Ana amfani da ruwa biyu idan za a lissafa ko zayyano wasu batutuwa yayin rubutu, kuma akasari idan an yi aya mai ruwa a rabutu, an fi yin sakin layi, misali:
            Bashir Yahuza Malumfashi ya yi rubuce-rubuce da yawa, wanda suka kunshi littattafan hikayoyi da wakoki. Daga cikin littattafansa akwai:
(1)   Kudin Jini.
(2)   Zinatu Matar Gwamna.
(3)   Sinadarin Rayuwa
(4)   Bikin Kishi.
Ba wai ya zama dole duk lokacin da aka samu ruwa biyu a rubutu, ya zama sai an yi sakin layi ba, misali, Kadan daga cikin wakokin Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) su ne: ‘Bara A Kufa’ da ‘Sakarkari’ da Bubukuwa. Abin da nake so Mai karatu ya antayawa kwakwalwarsa a Nan shi ne, a duk  lokacin da aka yi amfani da ruwa biyu a rubutu, to harafin da zai  biyo baya bai zama lalle sai babban baki ba, misali,
Ga yadda ake hada maganin: da farko a samu nono marar tsami, sai a zuba garin magani, sannan a kada, sai kuma a sha.
Amma  wasu masana ka’idojin rubutu sun ce, dole bayan an yi ruwa biyu a rubutu, sai babban baki ya biyo baya.

(8). WAKAFI MAI RUWA (SEMI-COLON) (;).
           Ana amfani da wakafi mai ruwa wajen daidaita jimloli, zantuka ko maganganun da suka zo bi-da-bi, misali:
            (1). Lokacin da aka shelanta ganin watan azumin Ramadana, wasu sun yarda; wasu shakulatin-bangaro suka yi da batun; wasu kuma sun tsaya a rigar-tsakani.
            (2). Hotuna ne guda uku, na farko Bello ne; na biyu Kabiru; na uku kuma  Fahad ne. Wani abu da ake so mutane su sani, shi ne, a wannan rukunin yayin da aka yi wakafi mai ruwa a rubutu, karamin baki ne yake biyo baya, ba kamar idan an yi aya ruwa biyu ba.

(9) ZARCEWA DODAR, (DOTS OR ELLIPSIS) (...).
            Ana amfani da zarce a rubutu wajen sanar da mai karatu cewa akwai sauran wani abu da ba a karasa ba, wani lokaci akan yi zarce a rubutu domin abin da ake so a sanar da mai karatu ya shige shi sosai, kasancewar shi zai karasa zancen da kansa. Zarce yana farawa ne daga ayoyi (digo) uku zuwa sama. Misali:
(1)   Rayuwar ‘yan Afirka a Turai, ba girin-girin ba………
(2)   Idan kunne ya ji, gangar jiki………..
Sai dai idan har rubutu bai kare ba, bayan an yi  amfani da zarce a rubutu, to babban baki ne zai biyo baya, misali:
(1). Rayuwar ‘yan Afirka a Turai ba girin-girin ba…… Amma idan ka je za ka gane irin kudar da ake dandanawa.

(10)ALAMOMIN ZANCEN WANI (QUOTATION MARK) (“  ” ko ‘ ’)
Ana amfani da alamomin zance don kebe ko nuna zance ko magana ta wani ne. Masana ka’idojin rubutu, sun amince a yi amfani da (“ ”) ko (‘ ’) yayin kebence ko nuna zancen wani. Ana kiran wannan alama ta farko  (“ ko ‘ ) da sunan BUDE ZANCE,  ta biyu kuma (” ko ’)  ana kiran ta da sunan RUFE ZANCE. Misali:
            Mamuda ya ce “Bello ya sayi na’urar kwamfyuta jiya.”  ko
            Mamuda ya ce ‘Bello ya sayi na’urar kwamfyuta jiya.’
Sai dai  takaddama ta kaure tsakanin masana ka’idojin rubutu, wasu daga cikin su, sun ce, lallai ne a saka Aya a karshen magana, zance ko jimla, misali:
            Hassan ya ce “Ibrahim ba shi da lafiya”.
   Dalilinsu na fadin hakan shi ne, idan dai an yi aya a rubutu  to komai ya kare, idan kuwa haka ne alamar zance za ta kasance kafin aya. Wasunsu kuma suka ce, a’a, idan har ba a sa Aya a rubutun ba, yaushe za a gane cewa zance ko, jimla ko maganar ta zo karshe, bare har a sa alamar zancen wani.
  Ittifakin da aka yi shi ne, duk ka’idar da ka dauka ka yi amfani da ita an amince. Ana nufin idan ka dauki amfani da Aya bayan alamar zancen wani shi ke nan, imma kuma ka zabi ka yi amfani da sai ka sa Aya kafin alamar zancen wani duk dai Annan wai (makaho ya Yi dare a kasuwa.

(12). KARAN TSAYE KO SANDA JIRGE (OBLIQUE OR SLASH) (/).
      Amfanin karan tsaye ko sanda jirge a rubutu shi ne, don a nuna kalmomi biyu ko fiye da haka, wa'yanda su ke da ma’ana iri daya, kuma duk wacce aka yi amfani da ita  ta wadatar. Misali:
           Ba da/bayar da
           Domin/don
           Sa da/sadar da.
            Kana za a iya amfani da karan tsaye ko sanda jirge a jimla, zance ko magana irin misalan da za su biyo baya:
(1)   Ka/ki amsa tambayoyi biyar kawai a wannan sashin.
(2)   Ware jinsin ka/ki daga nan: Namiji/Mace.
(3)   Wannan sashi an yi shi ne, don Yaro/Yarinya.

(13) DAFI (‘).
            Ana amfani da wannan alama a rubutu wajen banbamce wa mai karatu bakake da kuma wasulla da kuma yadda za a karanta a rubutu. Misali:
            Ko’ina     maimakon      koina
            Ka’idoji   maimakon      kaidoji
            Ummul’abai’sin maimakon Ummulabaisin.
            Ka ga yin amfani da wannan alama ce ya sa ake iya gane yadda za a furta wadannan kalmomi yayin karatu.

Da wanan ne mu ka zo karshen wanan makalar.
na Kuma sadaukar da wanan darasin ne wa ni kaina da Kuma sauran ilahirin al'umar hausawa baki daya.

Wanda a wata fuskar hakan daidai ya ke da in ce na sadaukar da wanan kasidar wa Kai/ke

A Nan na ke Mai cewa sai mun sake jamewa a jadawali na gaba.

(2).Kimiyya.

A hausance idan a ka ce kimiyya,a na nufin ;wani tsarin  binciken ilimi ne da ke amfani da hikima wajen  gano ko hakaito tsari da kintsin da Allah ya yi a hallitun, cikin sararin wanan duniyar, da ma ita kanta duniyar , har ma da kewayenta,Kama da ga kwayar zarra (atom) har IZuwa duniyar-duniyoyi,wato (univers.).

ASALI.

A falsafance ilimin kimiyya ilimi ne da aka San tarihin habakarsa Amma Kuma ba a san takamaiman tushenba,
 Sai dai    idan Kai musulmi ne,ko kirista zai fi maka sauki ka sanya a ranka cewa ko wanne ilimi da za ka ji ko za ka gani a duniyar Nan,to daga Allah ya ke.ganin damarsa ne, kuma ya saukar muna da ilimin ta hanyar wahayi,ko Kuma ta wadansu hanyoyin daban .wasu ilimimomin Kuma ya kan kyale mu ne ,mu je  mu Yi ta bincike har dai mu gano ya Abin ya ke.kasancewar  ya Riga da ya hore mana  fikira da  kaifin tinanin yin hakan .kasancewar kuma a haka ya tsara duniyar.

TARIHI

A kiyasance dai za a iya cewa ilimin kimiyya ya fara Gina kansa ne tun kimanin shekaru dubu hudu da su ka wuce.ya na Kuma girma da habaka ne a irin tsarin gini ko katanga.wato a duk lokacin da wani ya zo,zai Gina fahimtarsa ne,a kan ta wani , idan wani ya sake zuwa, dorawa kawai zai Yi a kan fahimtar wancan da ya gabace shi.duk da cewa a wasu lokutan wani yakan rushe fahimtar wani,Wanda ya gabace shin ,matukar cewa ,ya zo da fahimta da kuma hujjojin da su ka fi na wancan gamsarwa.

GIRMA.


 Duk  da cewa ilimin kimiyya shi ne ya Gina kansa hakan ba Yana nufin shi ya kirkiro kansa ba 'a'a,ana nufin dai ba mutum daya ne ko gari daya ne suka Gina shi ko kirkiro shi ba .wato hadaka ce ta fasihai da Kuma masana ta kowanne bangare na duniya.
 Yadda tsarin ke gudana  shi ne: ko Dan Ina ne Kai,idan ka zo da sakamakon wani bincike ko nazarinka akan wani Abu da ka yi a rubuce ko  kuma a zahirance,to za a karba a duba a gani a Kuma auna,idan ya yi daidai da tsarin da kimiyya ke tafiya a kai,to sai a karba a sa shi cikin kundin ilimin kimiyyar wanan fannin,a Kuma Yi kokarin yada wanan sakamakon I Zuwa uwa duniya.Kai Kuma a bisa kwazo da gudummuwarka a wannan fanin, za a martabaka iya martabawa,a Kuma Yi kokarin antaya sunanka a jikin tituna da makanratu,ta yadda sunan naka ba zai Yi sauri antayawa cikin kogin mantuwaba.

UWAYEN KIMIYYA.

 Kasashen da suka fi taimakawa kimiyya wajen ganin ta samu 'yancin kai su ne kamar haka: girka, (Greek) andalus,(Spain), jamus,(Germany) burtaniya,(England) farisa,(France) misira,da Kuma sauran daulolin larabawa da hindawa da ma wani yanki na sinawa.me yiwuwa wani zai iya tambayar kansa ya ce;" 'yancin Kai Kuma?,eh haka a ke nufin,domin ai a can farkon zamani kimiyya ba ta da 'yancin-kai.domin kuwa a wancan lokacin, duk wani Wanda ya zo da wani sabon ilimi ko fahimtar da ta sabawa addininsu na kiristanci, to hukuncinsa shi ne kisa.domin ya zo a tarihi cewa;wanan shaihin malamin ilimin TAURARI da lissafi da falsafa, Dan kasar andalus (spain).Mai suna; (Galileo galili)1564-1643,Wanda shi ne mutum na farko da ya fara kirkiro da na'urar nan ta hangen nesa wato (talaska)ko Kuma (telescope). wacce da ita  ya Yi amfani wajen gano cewa duniyarmu (earth) ba ita ce tsakiyyar duniyar-duniyoyi ba,wato (univers) ,Kuma ba Rana ce ke zagayar duniyarmu ba .wato ita duniyar tamu ce ke zagayar Rana.Wanda kuma hakan ya sabawa tsarinsu na kiristanci da yahudanci.hhmm, ai kuwa a nan take su ka kwamashe shi su ka garkame shi a magarkama,da ga karshe dai,a can ya iyar da sauran rayuwarsa.sai dai  duk da hakan , daga karshe  sai a ka zo, reshe ya juiye da mujiya,inda kimiyya da fasaha su ka kwace mulkin duniyar daga hanun malaman majami'ai, a ka Rika kashe malaman cocin.a takaice dai wanan manuniya ce da ke nuna cewa kimiyya ta hadu da kalubale kala-kala kafin ta samu ta tsira da mutuncinta.wanda yanzu ga shi an wayi gari,  ita ce abu mafi kima a siyasar duniya,ma'ana ;tattalin arzikin kowace kasa da karfin fada-ajinta,ya dogara ne kacokan a kan karfin kimiyya da fasaharta.
wani Abu Kuma da ya kamata Mai karatu ya shigar a kwakwalwarsa a yayin da ya ke auna ingancin falsafar kimiyya,shi ne;. A  tsarin irin na kimiyya; ba a yarda da tsafi ko sihiri ba ,Kuma ita kimiyya ba ruwanta da addini ko akida.wato atakaice dai  idan ka na karanta kimiyya a  matsayin godaben rayuwa,ne wato (carrier)ko Kuma ka na karanta ta ne domin nishadi.;abin da za ka yi kawai shi ne; ka dauki falsafar da ta zo daidai da karantarwar addininka.Sauran zancen kuma ka barmusu kayansu,ka ce da su; "su je dai su Kara bincike".me yiwuwa daga baya sa gano gaskiyar,kamar yadda  ya Sha faruwa.

 Masana kimiyya, sun karkasata,bangarori da dama,Amma dai bangarorin da za mu kwamaso a  darrussanmu na Wanan shafin su ne kamar haka:

1.kimiyyar rayuwa.(life science)

2.kimiyyar duniya.(earth science).

3.Kimiyyar na'urar comfiyuta.(computer science).

4.kimiyyar fasaha da kere-kere(engineering).



 A bisa lamuncewar UBANGIJi duk Wa'yanan fannonin ilimn ,Za mu  zuba su su a tire , daya-bayan-daya.

Ga Mai bukatar karanta  darusan a turance; sai ya ziyarci dayan shafinmu ta Wanan adireshin.
www.simplegeneralscince.blogspot.comwww.generalscience.blogspot.com
 Ga Mai neman Karin bayani ko gyara ko Kuma tsokaci,sai ya antayo sakon karta- kwana ta Wanan lambar,09035907765. Ko Kuma ya zuba sharhinsa ta Wanan akwatin sharhin..da ke kasan shafi.

Tuesday, December 25, 2018

(3).Kimiyyar rayuwa.

Idan a ka ce kimiyyar rayuwa a na nufin nazari da bincike a kan  abubuwan da su ka shafi hallitu masu rai,kamar kwari da dabbobi da tsirrai da ciyayi harma da ciyayyaki.sai dai kuma duba  da yadda wanan fanin ya ke da fadi sosai,ga Kuma karanci lokaci.wanda bisa la'akari da wa'yanan dalilan ne,  za mu karkata akalar nazarinmu kai-tsaye izuwa ga bangaren da ya shafi halittar dabbobi  ,a cikin hallitar  dabbobin Kuma za mu Mike ne dodar izuwa ga bangaren da ya shafi hallitar  dan adam.za mu yi hakan ne duba da ratar muhimmancin da ke tsakaninsu, .domin Kuwa  fahimtar tsari da yanayin  gudanarwar masarautar daukacin halittar jikinmu, na da matukar alfanu a garemu.domin ai kamar mota ce , da za ka tuka,wanda  sani da fahimtar  yadda ta ke gudanar da cakwalkwalin-zagayar-ma'aunin-juyawarta,(4.stroke).ya na da matukar muhimmanci ga kai matukinta.saboda a duk lokacinda ka ji  motar ta na kauri ko Kuma  ka ji ta Yi zafi,ko ta na kabiri ,Kai tsaye ka San inda za ka dosa.wanan a mota kenan,domin ai shi jikin Dan Adam,cakwalkwalin da ke cikinsa,ya fi na duk wata kerrariyar na'ura  da a ka  kera ko  ma wacce za a kera a Nan gaba. bugu-da -Kari Kuma sanin fasali da yanayin aikin massarrafan da ke jikinmu,zai yi matukar taimaka mana wajen magance afkuwar kananun matsalolin lafiya da ke addabar mu.wanda kuma hakan zai taimaka wajen rage yawan sinki-sinkin fayil-fayil da ke makare a cikin ma'adanan fayil na  asibitocinmu.

Kamar yadda na fada a baya cewa Nazarin hallitar Dan Adam,,babi ne Mai fadin gaske, hakan ne ma ya sa hallau za mu antayo bayanai ne a  daidai gwargwadon yadda lokaci  ya bamu dama.domin idan mu ka ce za mu yi bayanin komai da fadi sosai to babu mamaki babin ya iya daukar mu na tsawon shekaru biyar, ba mu kamalla shi ba.

Darasin namu,  zai fara ne tun daga kwayar zarra,(atom),izuwa kwayar hallita wato,(cell)har dai izuwa tantashi (tissue)  da masarrafai,wato(organs) daga nan kuma sai mu zo mu yi nazari da bayaninsu daki-daki,wato daya-bayan-daya.
 bayan mun caskale Wa'yanan ,sai kawai mu antaya  izuwa ga,babin
Tsarin gudanawar jikin Dan adam.wato(human body systems).

Monday, December 24, 2018

(4).Kwayar zarra.(atom).Kwayar hallitta.(cell). tantashi.(tissue).massarrafa.(organ).


MATASHIYAR FARKO.

  Kwayar zarra.(atom).

kwayar zarra,wata kankanuwar hallitta ce ,da idon Dan Adam ba ya da kaifin ganinta,sai tare da taimakon na'urar hangen kananun abubuwa,wato (microscope)
duk wani Abin da  da za ka gani a duniyar nan Mai cin mizanin muhalli,to za ka samu cewa, hadaka ce ta dubbanin kwayoyin zarra masu adadin madda da Allah ya hallita Kuma ya  tattara su  waje daya domin Gina Wanan bayyananiyar  hallitar
A kiyasance gundarin hallitar dan Adam hadaka ce ta kwayoyin zarra da adadinsu ya kai okutiliyan bakwai.(7,000,000,000,000,000,000,000,000,000,).

MATASHIYA TA BIYU.

Kwayar hallita.(cell).

 Rayyayen tubalin gina hallitta,ko Kuma ka ce kwayar hallita, a saukakkaken harshe. 
Duk wani ko wata hallitta mai Rai da za ka gani a duniyar nan, to tabbas za ka samu cewa, hadaka ce ta daya ko sama da dayan Wanan kwayar hallittar.duk da cewa da akwa kananun hallitun da ba su Kai girmanta ba kamar kwayar zarra,Amma kuma; ai sai a nata matakin ne Allah ya Fara sanyawa kananan halittu cikakken gundarin-ruhin-rayuwa, ya Kuma damka mata cikakken'yancin gudanarda rayuwa, ta yadda za ta iya rayuwa ita kadai wato a yanayin tilo da Kuma a yanayin hadakar kawance. To sai dai ita ma ,
kwayar hallittar, ta na gudanar da rayuwarta ne,tare da taimakon wa'yansu kananun hallitun da allah ya sanya a farfajiyar zagayyayen gangar jikin kwayar hallitar.inda kowanne daga cikinsu, da akwai gudummuwar da ya ke bayarwa wajen gudanar da 'yantaccen zagayyayen ruhi.muhimmai daga cikinsu, su ne kamar haka;
 1).ganuwar kwayark hallitta.
(CELL MEMBRANE)
Ganuwar kwayar hallitta wata katanga ce, da ke zagaye da farfajiyar muhhallin kwayar hallitta.amfaninta shi ne daidaita fasalin kirar kwayar hallittar,da Kuma kula da shige-da-fice na duk wani sinadarin ruwa ko na maiko,Hadi da dakartar da duk wani bakon-haure da ke kokarin shiga ciki,ba tare da izini ko tikiti ba.

2).Romon kwayar hallitta.(cytoplasma).

romon kwayar hallitta;wa'yansu ruwan yauki ne da ke cikin kawayar hallita,masu dauke da kananun sinadaran gishiri da sukari,da ma sauransu wa'yansu sinadaran. Romon  na zube ne kamar karamin kogi,a cikin kwayar hallittar.amfaninsu, dai-dai ya ke da amfanin ruwan kogi a wajen kifi.ma'ana; da su ake amfani wajen wankewa da Kuma tsaftace wa'yanan kananun hallitun da ke cikin kwayar hallitta.

3).kundin sirrin zuri'ar hallitta.(nucleus).

kundin sirrin zuriya; wata karamar hallita ce mai kamar tamola(kwallo),a tsakiyar kwayar hallitta.  Ita ce ta ke dauke da karan madarar  bayanan siffa da fasalin zuri'a ,wato (DNA).a cikin madarar ne kuma dunkullalun zaruruwan bayanan  gadon dabi'u da siffofi su ke.wa'yanda da za a warware su,to da a kiyasance tsawon zaruruwan zai iya Kai tazarar nisan mil miliyan goma.(10,000,000,).  amfanin Wa'yanan zaruruwan shi ne; gadar da samfurin hallitar baya izuwa ga na gaba,wato sawwara fasali, daga kakkanni izuwa ga jikokin da za a Haifa Nan gaba.
kamar  yadda bayani ya gabata cewa kwayar hallitta; wata rayyayar hallita ce da  ke iya gudanarda rayuwarta ita kadai,(uni-cellular) ko Kuma a yanayin hadaka , inda miliyoyin kwayoyin hallita ne, da Allah  ya  hade su waje daya, domin Samar da wata kamallalliyar hallitta, Mai cike da hikama,wato (multy-cellular organisims).kamar dai ta Dan Adam. Domin a kiyasance kwayoyin hallittu triliyan talatin da biyar ne Allah ya zuba a cikin  gangar jikin hallittar Dan Adam,.(35,000,000,000,000').inda ya rarraba musu ayuka daban-daban.
 A takai ce dai hallitar Dan Adam ta ginu  ne a wa'yansu matakai na hadakar hallittu guda biyar. matakin farko shi ne; matakin kwayar zarra,(atom,Wanda bayaninsa ya gaba, sai Kuma matakin kwayar hallitta,(cell)Wacce ita ma bayaninta ya riga da ya gabata.sai Kuma mataki na uku,wanda za mu Kira; da tantashi.(tissue).Daga Nan Kuma sai  mataki na hudu wato massarafa.(organ).mataki na biyar  kuma shi ne; tsarin gudanarwar jiki.
(human body system).
A bisa lamuncewar UBANGIJi,bayaninsu zai zo dai-bayan-daya.

MU KASANCE A ANKARE.


  Kasancewar da a kwai wa'yansu kananun matakan gina hallittar, Dan Adam da ke kafin kwayar hallitta (cell) izuwa ga kwayar zarra(atom).
mun gutsure su ne kasancewar su ba rayyayu bane,sai mu ka Fara daga masu Rai.ita ma kwayar zarrar mun kawo ta ne domin bada misalin tushe.
MATASHIYA TA UKU.

Tantashi.(tissue).

Domin Allah ya Gina wata hallitar Mai cike da 'yanci da nagarta, wacce za ta iya jure gwagwarmayar Wanan duniyar tamu,sai Allah ya tattaro kwayoyin hallatta masu Kama da juna ya kullamusu kawance da junansu,ya Kuma kaddarta musu wani takamaiman aiki, Wanda zai bada gudummawa da kuma taimakawa wajen  gudanarda nagarttaciyar hallitta.
 tantashi kamar wani Dan yanki ne daga cikin wata massarafa,kuma  iri hudu ne a  cikin jikin Dan adam.su ne ; kamar haka;  

Tantashin Kashi,
Tantashin tsoka,
Tantashin jini,
da Kuma na lakka..


MATASHIYA TA HUDU.

Masarrafa.(organ).

masarrafa wata halitta ce Mai fasali da aiki irin na na'ura,Kuma itama  hadaka ce ta kwayoyin hallittu, da Allah ya hada a cure waje daya, ya kuma umarcesu da   yin wani aikin a tare, da zai taimaka wajen tafiyarda rayuwar dan adam. Da akwai masarrafai da dama a jikin Dan Adam,wa'yanda adadinsu zai iya Kaiwa kimanin tamanin da bakwai,(87).
muhimmai  daga cikinsu ,su ne kamar   ; kwakwalwa ,zuciya ,huhu ,Koda, hanta da Kuma fata,. 
A bayyane ya ke cewa Wa'yanan da mu ka zayyano,su ne su ka fi muhimmanci a godaben tafiyar da rayuwa.Dom su ne  idan daya daga cikinsu ya kasa, gudanar da aikinsa,To faa sai... Ta Allah.
Idan Allah ya lamunce mana,za mu daukesu mu yi bayaninsu daya-bayan-daya. Daga nan ne kuma, sai mu antaya dodar izuwa ga  matakin karshe,wato tsarin gudanarwa.
(HUMAN body system).

SAI A DAKACE MU,,,,,mu na Nan dawowa..... 

Ga Mai bukatar karanta wa'yanan darussan a harshen turanci. sai ya ziyarci dayan shafinmu,Mai adreshi kamar haka;
www.simplegeneralscience.blogspot.com.ko Kuma ka antaya Nan ,domin a rage Maka hanya dodar,,,
Ga mai shawara ko  neman Karin bayani, sai a aika sako ta Wanan lambar; 09035907765 /ko
 a Wanan  akwatin sharhin da ke kasan shafin.

Sunday, December 23, 2018

(5)Sassan jikin Dan Adam da amfaninsu.(1)

Jikin dan Adam halitta ce  da ta kunshi sassa  da massarafai daban-daban, Kuma kowanne sashe daga cikin ssasan aiki ya ke tukuru domin baiwa Dan Adam damar  kasancewa cikakkiya Kuma rayyayar halitta, Mai cike da al'ajabi. duk wani stiro ko tantani da za ka gani a ciki da wajen  hallittar Dan Adam ,to za ka samu cewa da akwai amfaninsa,sai dai idan bincike da ilimin da mu ke da shi bai kai mu wajen gano amfaninsa ba. 
Da ya ke sassan jikin Dan Adam  su na da Dan yawa. Wanan ne ya sa   za mu dauki  muhimmai daga cikinsu mu yi nazari akansu dai-bayan-dai.
1)kwakwalwa:.

kwakwalwa ita ce massarafa mafi muhimanci da amfani a cikin jikin Dan adam. Domin kuwa cike ta ke da abubuwan al'ajabi, da ban mamaki. Wanda hakan  ne ma ya sa  har IZuwa yanzu masana falsafar kimiyyar kwakwalwa,ba su Kai ga  kamalla binciken gano yadda kwakwalwar  ke aikinta ba.domin a wani taron shaihhunan malamin  kimiyyar lakka da kwakwalwa wato (the conference of  neoro scientists ) da aka gudanar a kasar (Sweden).inda daya daga cikin su  mai suna Ptoenie Brogherter,Ya ke cewa " izuwa yanzu da na ke magana 
(4-10-20018).idan a ka yi maganar nazari da binciken kwakwalwa,wanda  ya samo asali shekaru  dubu uku,Wanda Kuma har yanzu a na kan aikin,Wanda kuma har izuwa yanzu matakin bincikenmu bai wuce mun gano kaso biyar ne kacal daga cikin dari ba 5% dangane da al'amarin da ya shafi kwakwalwa".ya ci gaba da cewa "Wanan dalilin ne ma ya sa mu ka kalubalanci duniyar tsoffafi da sabbabin malaman kere-kere,wato( electrical and mechanical engineers ), da cewa, a duniyarnan kaf ba su kirkiro ba ,Kuma ba za su iya kirkiro wata   na'urar da za ta yi sarkakiya da ban al'ajabi kamar kwakwalwa ba".,,Wanan falalar kwakwalwa kenan,,,,
 Amfanin kwakwalwa a jikin Dan Adam, shi ne kamar amfanin sarki ko sarauniya,  a cikin alkarya.( rayyayen gari).domin ita ce ta ke karba da sarrafawa tare da bada umarnin duk wani kafce da a ke aiwatarwa a ciki da wajen hallitar Dan adam.ita ce Kuma ta ke adana daukacin bayanan da a ka shigarmata da su, ta  ido  ko ta kunne, da ta hanci,da harshe da fata..kuma ita ce ta ke bada umarnin kaftawa da ginstewa na Kai tsaye ne ko na dindindin a kan duk wani aiki da za a zartar a ciki da wajen Dan Adam. 
Ta kan kuma karba da   aika sakon ne a yanayin lantarki, ko Kuma ta hanyar amfani da madarar sinadaran maganadisu,wato (hormones).

A kiyasance kwakwalwa ta na kunshe da kwayoyin hallitar lakka,(nereons).da adadinsu ya Kai biliyan tamanin da shida.(86,000,000,000,).Kuma ita ce ta ke lakume kaso talatin cikin dari na abincin da iskar oksijin .30.%.da mu ke ci ko Shaka.
 Kuma a kimiyance, an gano cewa bangren kwakwalwa na tsagin dama ne ya ke sarrafa bangaren gangar jiki na tsagin hagu,shi kuma na hugu,shi ne ya ke sarrafa bangaren tsagin jiki na dama.
Wani abin al'ajabi kari a bisa wancan da kwakwalwa ke da shi,shi ne ; a ita  zubin gundarin gangar jikin kwakwalwar , ba ta da shaukin Jin radadi. kenan hakan na nufin za a iya fafewa a cire wani sashe na kwakwalwar,ba tare da ta sani ba.to sai dai kuma ,da kwai 'yar cakwakiya kafin a Kai ga riskar ita kwakwalwar.kenan dai hakan zai yiwu, Kuma ba zai yiwu ba.
Wata sabuwar Kuma ,inji 'yan caca,ita ce ; Masana  kimiyyar kwakwalwa, sun Kai ruwa-rana wajen tantance adadin bayanan da kwakwalwa za ta iya killacewa a ma'adanarta.(memory).
wasu, daga cikin shaihhunan malaman,wato (professors).su ka ce ; "kwakwalwa za ta iya alkintawa Hadi da adana  gabadayan bayanan da ke cikin miliyoyin  gima-giman kwamfutocin da ke yanar ankabuti wato,yanar-gizo.wanda sun hada da bayanan rubutun bayanai na (tex) da na garmaho, (music) da hotunu (images) da Kuma na majigi wato (videos).wanda hakan na nufin dukan bidiyoyin  da ke makare a gidauniyar madaukar shafin Youtube,da ma duk sauran madaukan shafukan sada zumunta.kamar na manhajar facebook da na rariyar gilashin tambaya,wato google.wanda idan a ka tattara adadinsu ,zai iya lashe ma'adanin- farfajiyar- bayanai da mizaninsa zai iya Kaiwa zeta biliyan sitting da shida.(66,000,000,000,zeta byts)". 
A dayan bagaren masanan Kuma, su ka ce" shi rumbun ma'adanar bayanan - kwakwalwar Dan adam,ba ya da iyaka.,,,,,fakattt.
Hallau dai Masana falsafar kwakwalwar sun karkasa bangarorin kwakwalwa izuwa manyan bangarori  uku,.sun Kuma Yi kokarin bayanin rawar da kowanne bangaren ke takawa ,Amma fa a kintatance.
 Su ka ce "bangaren da ke gaban goshi shi ne ya ke da alhakin,  yin tunani,  da  magana, fahimtar yare, alkalanci,da Kuma fikira.
Bangaren tsakiya Kuma,su ka ce" ;  shi  ne ke da alhakin damalmalewa da al'amuran da su ka shafi,ji da gani, dandano, kamshi,da Kuma jin-dadi,wato a yayin da a ke cikin yanayin kodimo.su ka ce kuma Wanan bangaren ya na da wani yanki na alhakin sarrafa, bugun zuciya da jujjuya numfashi.
Shi Kuma bangaren bayan keya ,shi ne ya ke kula da ayukan da mu ke bayar da umarninsu,da Kuma ayyukan sarrafa mabubbugan madarar maganadisu,(hormones).Kuma shi ne ya ke da alhakin, daidaita,zafin jiki.

A falsafance za a iya cewa an gano
Duk wa'yanan al'amuran ne  ta hanyar gwaje-gwaje da nazarin mutanen da su ka samu tabin hankali da Kuma wa'yanda su ka samu rauni ko buguwa a kwakwalwar tasu.sanadiyar hadari ko wani iftila'i.
Misalin: a duk sanda wani ya samu rauni ko buguwa a wani bangare na kwakwalwarsa.sai Kuma a ka ga ya daina gani,bayan Kuma ga idanuwansa lafiya kalau,to kenan Wanan bangaren da ya cutu,shi  ne ke da alhakin samar da gani.
A Wasu lokutan Kuma a kan yi amfani da wa'yansu dabbobin,kamar birai da beraue wa'yanda a kimiyance,su na da kusanci da mu ta fuskar tushe.sai a dan yi nazarce-nazarce a  kan kwakwalwar dabbobin,domin ganowa ko hakaito 'yan banbance-banbancen da ke tsakanin mu da su.a kan Kuma Yi hakan a bisa wata mahangar kimiyya  wato ,(formula) da ke cewa ; (
 zubi-da- girman-kwakwalwar-dabba-a-bisa-la'akari-da girman-jikin-dabbar- a-rubanye.)

Duk wanan dai manuniya ce da ke nuna cewa kwakwalwa ita ce matakin farko Kuma a ajin farko a jikin Dan Adam,Wanda a turanci a ke cewa
 (first-lady).

Sai mu kula..
Domin idan wata rana aka yi rashin sa'a,  kwakwalwar ta hargitse, ta sanadiyar Shan miyagun kwayoyi, to fa.... ,sai ta Allah.
.kasancewar malaman Kimiyyar ma tsoron ta su ke yi...sai mu kiyaye.
2.) Zuciya.:
zuciya wata irin hallitace Mai fasali irin na mangwaro, da aka yi ta da wata irin stoka Mai gautsi da Kuma laushi.mazauninta na nan a tsakiyar kirji Maso hagu.aikinta shi ne  harba jini  domin zagayowa i Zuwa ga Sauran sassan jiki gabadaya.,tana yin hakan ne ta hanyar tamurewa da Kuma warwarewa.wato ta na kumbura ta na  sacewa,tana kuma  yin hakan ne a bisa wani tsarin da ke amfani da snadaran lantarki.
tsarin  harba jinin na gudana  ne kamar haka :zuciyar ta na da wasu kusurwai ko ramuka guda hudu,Kuma ko wannensu ya na  da mastuka,(valve) da ya ke stukewa da Kuma warwarewa,.jinin da  ke fitowa daga sassan jikin,ya kan shigo zuciyar ne ta ramen sama na dama, daga nan, sai shi kuma ramen kasa na dama ya bude, domin jinin ya shigo.daga nan sai  shi  Kuma ramen kasan, ya harba jinin I Zuwa ga huhu domin yin musayar sinadarai  ,idan jinin zai dawo sai ya shigo ta cikin ramen sama na hagu.daga nan Kuma sai ramen kasa na hagun ya bude domin jinin ya shigo ramen kasa na hagun ,ya na  shigowa,sai shi Kuma ramen kasa na hagun ya harba jinin i Zuwa sassan jikin gabadaya.hakan zai Yi ta maimaita kansa ne, ba-dare-ba-rana har na iya tsawon rayuwa.
KIDDIDIGA.

A kowacce rana zuciya na harba jini, da ke zagayar jiki,  Wanda idan da,a hanya dodar zai yi tafiya,to da tazarar tafiyarsa,za ta iya Kai,nisan kilomita,dubu goma-sha-tara.(19,000,km p. day).
Haka kuma  zuciya,ta na harba jini a yanayin kumbura da sacewa,da adadin yin hakan ya Kai biliyan uku(3,000,000,000).a gabadayan -daidaitacciyar -tsawon -rayuwar Dan Adam.
Ita ma dai, idan  a ka yi rashin sa'a har,ta je hutu ko yajin aiki , na stawon mintina biyar , to fa!!!!! Sai ta Allah.
3)huhu.

huhu wani nau'in masarrafa ce ko halitta da aka yi shi da wata tsoka Mai kamar tala-bushe,ta yadda zai iya kumbura ya sace akalla sau goma a cikin minti daya.amfanin huhu daidai yake da amfanin kasuwar musaya.ma'ana: huhu kan bada muhalli ne  domin gudanarda harkallar da bahaushe ke Kira da  bani-gishiri-in-baka-manda,wato musaya.

Yadda abin  ya ke  shi ne.: da a kwai wa'yansu sinadaran da jikinmu ya ke bukata domin gunarda aikin markade sinadaran abincin da mu ke ci a matsayin makamashi domin Samar da kuzari wajen gudanarda rayuwarmu ta yau-da-kulllum wato; (cellular-respration).,Kuma ,a cikin farfajiyar wanan duniyar tamu ne wanan sinadarin ya ke.,sai dai Kuma  a garwaye ya ke da iskar sarari da Kuma sauran iskokai,ta yadda ba za mu iya shansa ko cin sa  a loma-loma ba.sai dai  mu kan zuko sinadarin ne a yayin numfashi . Wato mukan zuko shi ta hanci , daga nan hanci zai tace shi ya mika shi izuwa ga makogwaro, har dai  IZuwa can kasan huhu, inda a Nan ne, a ke gudanarda  musayar.
  Shi ma dai haka abin zai Yi ta maimaita kansa, har na iya tsawon rai.bugu-da-kari kuma , huhu shi ne ya ke taimakamana wajen fitar da sautin magana
.
kamar dai Sauran massarrafan.
shima ya kan iya Zuwa yajin aiki idan a ka lazimci gurbatashi ,ta hanyar antaya Masa hayakin sigari ko kuma Wanan hayakin Mai guba,wanda ke fitowa daga masuburbudar hayakin injina, wato(carbon monoxide).!!
Dan haka sai mu kiyaye.
idan mun je a nazarin tsarin numfashi.za mu Yi bayani mai Fadi wato dalla-dalla.

Ga Mai bukatar karanta Wanan tartibin a harshen turanci  ,sai ya ziyarci dayan shafinmu,a adireshi kamar haka;
www.simplegeneralscience.blogspot.com.
Domin neman Karin bayani, Kuma 09035907765.